Shugabannin ƙasashen duniya sun fara miƙa saƙon jaje ga Shugaban Amurka Donald Trump da mai ɗakinsa bayan da aka tabbatar sun kamu da annobar korona.
Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa yana yi wa Trump da matarsa addu'ar samun sauƙi. A lokacin da Johnson yake asibiti bayan kamuwa da korona, Trump ta Tuwita ya bayyana cewa yana tare da Johsnon a halin da yake ciki.
Shi ma Firaministan India Narendra Modi wanda ya karɓi baƙuncin Trump yayin wata ziyarar aiki a farkon shekarar nan ya ce yana yi wa shugaban Amurkar da mai ɗakinsa "fatan samun sauƙi cikin gaggawa."
Charles Michel wani jami'i a Kungiyar tarayyar Turai shi ma addu'ar samun sauƙi ya yi wa ma'auratan inda ya ce "cutar korona yaƙi ne da za mu ci gaba da yi. Kullum. Ko ina muke a duniya."
Mai magana da yawun gwamnatin Faransa, ya ce kamuwar da Trump ya yi da annobar korona na nuna cewa "cutar bata raga wa kowa ba har da waɗanda suke nuna shakku game da cutar. Ina masa addu'ar samun sauƙi."
Babban abokin hamayyar Trump a zaɓen watan Nuwamba, Joe Biden kawo yanzu bai ce komai ba amma a ranar Talata ne suka fafata a muhawararsu ta farko da suka yi gabanin zaɓen.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce "kyawawan halaye da kuma kyakkyawan fata" na shugaba Trump zai taimaka masa wajen shawo kan cutar.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce "ina miƙa fatan alherina ga Donald da Melania,". "Ina fatan za su warke daga cutar."
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "Kamar miliyoyin Isra'ilawa da Sara [mai ɗakin Netanyahu] da kuma ni muna tunanin Shugaba Donald Trump da matarsa Melania Trump muna kuma yi musu addu'ar samun sauƙi".