Za
a sake bude gidajen sayar da barasa a Kenya a ranar Talata, watanni shida bayan
an rufe su don dakile yaɗuwar kwayar cutar Korona.
Sai dai an iyakance lokacin hada-hada zuwa karfe 10 na dare.
Shugaban
kasar Uhuru Kenyatta ne ya sanar da hakan yayin da yake yi wa al'ummar kasar
jawabi game da sabbin dubarun da gwamnati ta ɓullo da su don magance cutar.
Amma abin da ya bada mamaki shi ne yadda bai yi wani ƙarin bayani ba game da buɗe
makarantu ba, abin da ke nufin cewa za su ci gaba da kasancewa a rufe.
Sannan
shugaban ya tsawaita dokar hana fita ta dare zuwa ƙarin kwanaki 60, wadda za ta
riƙa aiki daga karfe 11 na dare zuwa 4 na asuba.
Wakilin
BBC ya ruwaito cewa an samu raguwar yaduwa cutar a makonnin da
suka gabata.
Ana
ganin sauƙaƙa matakan kullen da hukumomin Kenyan suka yi a yanzu na da alaka da
sauyin da aka samu.
Sai dai shugaba Kenyatta ya yi gargadi da kakkausar murya, yana cewa har yanzu
kasar ba ta tsira ba, don haka jama'a su kiyaye.
''Mun
samu nasarar rage yaduwar cutar korona, amma hakan ba wai yana nufin mun kawo
karshenta ba ne," in ji shi.