Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An gudanar da jana'izar Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi sakamakon zaɓen gwaman jihar Edo da ke Najeriya da ƙarin labarai.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Mustapha Musa Kaita

  1. Gwamna Wike ya bayyana abin da faru ga jami'in tattara zaɓen Ƙaramar Hukumar Orhionmwon

    Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya gudanar da wani taron 'yan jarida domin yin bayani kan abin da ya haifar da tsaiko wajen fitar da sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Orhionmwon.

    Gwamna Wike wanda a baya ya bayyana gamsuwa da tsarin zaɓen gwamnan na Edo, ya ce ya yi mamaki kan yadda aka bayyana jami'in tattara sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar ya yi ɓatan dabo.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a shafin gwamnan Edo Godwin Obaseki na Facebook.

  2. Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris ya rasu

    Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa.

    Ya rasu yau Lahadi.

    Uban Garin Zazzau kuma Hakimin Soba, Alhaji Bashir Shehu Idris wanda ɗa ne ga marigayin shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin.

    Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna.

    Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani.

  3. Obaseki ya lashe zaɓe a Ƙaramar Hukumar su Iyamu

    Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya lashe zaɓe a Ƙaramar Hukumar Orhionmwon wadda ita ce Ƙaramar hukumar da ɗan takarar APC Ize-Iyamu ya fito.

    Ga yadda sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar ya kasance:

    APC: 10458

    PDP: 13445

  4. Amurka ba ta da ikon ƙaƙaba mana takunkumi – Iran

    Iran ta yi Allah wadai da sanarwar Amurka cewa an sake ƙaƙaba mata takunkumi saboda karya dokokin da suka shafi yarjejeniyar nukiliya ta duniya.

    Iran ta ce Amurkawa ba su da ikon sake ƙaƙaba takunkumin sannan kuma sanarwar ba ta da wata ma'ana.

    Shugaba Trump ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar shekara biyu da suka gabata.

    Amma Amurka ta ce har yanzu tana da ikon sanya wa a ƙaƙaba wa wata ƙasa takunkumi.

    Sauran ƙasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sun nuna ƙin amincewarsu - har da Burtaniya da Faransa da Jamus.

    Rasha ta ce Amurka na iƙirarin cewa takunkumin da aka sake ƙaƙabawa ya saɓa doka.

  5. Zaɓen Edo: INEC ta kira taron wakilan jam'iyyu

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta kira wani taro da wakilan jam'iyyun da suka fafata a zaɓen gwamna na jihar Edo.

    Sai dai kuma a yanzu haka, INEC ta tafi hutu kuma da zarar ta dawo daga hutun ne za ta ci bayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi biyu da suka rage.

    Ƙananan hukumomin biyu sun haɗa da Orhionmwon da Ovia South-West.

  6. 'Jami'in tattara sakamakon zaɓe na Ƙaramar Hukumar Orhionmwon ya yi ɓatan dabo'

    Wakilan BBC da ke cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan Edo sun ce hukumar INEC ta bayyana fargaba kan rashin sanin inda Jami'in tattara zaɓe na Ƙaramar Hukumar Orhionmwon yake.

    Bayanai sun ce an hange shi a cibiyar tun da farko amma kuma ba a san inda yake ba.

    Wannan ce ƙaramar hukumar ɗan takarar APC kuma babban abokin karawa a zaɓen,

    Lamarin dai ya sa wakilan jam'iyyu na zargin akwai lauje cikin naɗi.

  7. Kai-tsaye: Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo

    Ku duba yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Edo yake kai-tsaye kamar yadda ake ci gaba da sanarwa a cibiyar tattara sakamakon ƙuri'u da ke Benin, babban birnin jihar Edo.

    Za ku iya samun ƙarin bayani a nan.

  8. 'An harbi jami'in INEC a Ƙaramar Hukumar Etsako Central'

    Jami'in tattara sakamakon zaɓe na Ƙaramar Hukumar Etsako Central Farfesa Godswill Alaminiokuma na jami'ar gwamnatin tarayya ta Effurun a jihar Delta ya bayyana cewa wani rikici da ya tashi a yankin ya janyo an harbi jami'in INEC.

    Ya shaida haka ne bayan kammala sanar da sakamakon zaɓen Ƙaramar hukumar a cibiyar da ake tattara zaɓen gwamnan Edo da aka gudanar jiya.

    Ya kuma ce akwai wani jami'in hukumar ta INEC da a yanzu haka yake kwance a asibiti.

  9. Sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Etsako Central

    APC: 8359

    PDP: 7478

  10. Sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Etsako East

    APC: 17011

    PDP: 10668

  11. Coronavirus: 'Za a fara gwada magungunan gargajiya na Afirka'

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince a fara gwada magungunan yaki da cutar korona na gargajiya da aka samar a Afirka.

    Cikin wata sanarwa, ofishin hukumar na Afrika da ke Brazzaville ya ce ya amince da yarjejeniyar gwada magungunan dai-dai da sauran gwaje-gwajen da ake yi wa rigakafin cutar da ake samarwa a kasashen duniya.

    Hukumar ta ce duk wani maganin gargajiya da aka yanke hukuncin yana da inganci to kuwa za a iya fara amfani da shi a fadin duniya take yanke.

    Matakin ya zo ne watanni bayan da shugaban Madagascar ya shelanta wa duniya wani maganin gargajiya da ba a gwada ba, da yace zai taimaka wajen dakile cutar ta korona.

  12. Sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Akoko Edo

    APC: 22963

    PDP: 20101

  13. Zaɓen Edo: INEC ta dawo daga hutu domin ci gaba da bayyana sakamako

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC wadda ke tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo da aka kammala jiya ta dawo daga hutun sa'a ɗaya da ta tafi domin ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen.

    Baturen zaɓen gwamnan Edo shi ne Farfesa Akpofure Rim-Rukeh kuma shi ne shugaban jami'ar gwamnatin tarayya ta Effurun a jihar Delta.

    Tuni aka bayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 13 cikin 18 da ake da su a jihar ta Edo.

    A halin yanzu, ana dakon sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi guda biyar sannan daga bisani INEC ta sanar da wanda ya lashe zaɓen gwamnan na Edo.

  14. Mun gamsu da tsarin zaɓen gwamna na Edo – Nyesom Wike

    Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce ya gamsu da tsarin da aka bi na yin zaɓen gwamna a jihar Edo.

    Ya ce ya ji daɗi da yadda mutane suka yi tururuwar fita domin zaɓar 'yan takarar da suke so.

    Gwamnan ya ƙara da cewa ba a samu matsalar tashin hankali ba saboda irin matakan da hukumomin tsaro suka ɗauka a jihar.

  15. Wakilin PDP ya yi tsokaci kan sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Etsako West

    Wakilin Jam'iyyar PDP a Ƙaramar Hukumar Etsako West ya koka da kura-kuran da aka samu a sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar da aka sanar.

    Ya bayyana haka ne bayan da jami'in da ya tattara sakamakon zaɓen ya kammala sanar da sakamakon zaɓen karamar hukumar.

    Ya ce an ɗan samu matsalar ƙuri'un da aka kaɗa sun zarce mutanen da suka yi zaɓen a mazaɓa ta 10, rumfa ta 1 da 2 da kuma 3.

    Baturen zaɓen, Farfesa Chinedu ta ce akwai batutuwa da dama da INEC ya kamata ta warware su.

  16. Obaseki ya bai wa Ize Iyamu tazara a yawan kuri’u

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo a ƙananan hukumomi 13 daga cikin 18.

    Alkaluman da INEC ta fitar a hukumance sun nuna cewa Gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP ya bai wa babban abokin hamayyarsa Ize Iyamu na jam'iyyar APC tazara da dubban ƙuri’u.

    I zuwa ƙarfe tara na safiyar ranar Lahadi, hukumar INEC a cibiyar tattara sakamakon zaɓe a Benin, babban birnin jihar Edo ta ce Obaseki na PDP ya samu ƙuri’u mafi rinjaye a ƙananan hukuma 11 a yayin da Ize Iyamu ya lashe zaɓe a ƙananan hukumomi biyu.

    Ga sakamakon zaɓen na ƙananan hukumomin:

    Karamar Hukumar EGOR

    APC: 10202

    PDP: 27621

    Karamar Hukumar OWAN EAST

    APC: 19295

    PDP:14762

    Karamar Hukumar OVIA NORTH EAST

    APC: 9,907

    PDP: 16,987

    Karamar Hukumar ETSAKO WEST

    APC: 26,140

    PDP: 17,959

    Karamar Hukumar ESAN WEST

    APC: 7,189

    PDP: 17,434

    Ƙaramar Hukumar ESAN SOUTH EAST

    APC: 9237

    PDP: 10563

    Ƙaramar Hukumar OREDO

    APC: 18365

    PDP: 43498

    Ƙaramar Hukumar IKPOBA OKHA

    APC: 18218

    PDP: 41030

    Ƙaramar Hukumar IGUEBEN

    APC: 5199

    PDP: 7870

    Ƙaramar Hukumar OWAN WEST

    APC: 11193

    PDP: 11485

    Ƙaramar Hukumar ESAN CENTRAL

    APC: 6719

    PDP: 10794

    Ƙaramar Hukumar ESAN NORTH EAST

    APC: 6556

    PDP: 13579

    Ƙaramar Hukumar UHUNMWODE

    APC: 5972

    PDP: 10022

  17. Sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Igueben

    Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista: 46828

    Masu zaɓe da aka tantance: 13404

    Halastattun Ƙuri'u: 13170

    Ƙuri'un da suka lalace: 212

    Ƙuri'un da aka kaɗa: 13382

    Yawan ƙuri'un jam'iyyar APC da PDP:

    APC: 5199

    PDP: 7870

    Za ku iya shiga nan domin ku duba yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Edo yake kai-tsaye

  18. Sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Uhunmwode

    Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista: 73416

    Masu zaɓe da aka tantance: 16741

    Halastattun Ƙuri'u: 16283

    Ƙuri'un da suka lalace: 352

    Ƙuri'un da aka kaɗa: 16635

    Yawan ƙuri'un jam'iyyar APC da PDP:

    APC: 5972

    PDP: 10022

  19. Sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Ikpoba Okha

    Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista: 310073

    Masu zaɓe da aka tantance: 61731

    Halastattun Ƙuri'u: 60052

    Ƙuri'un da suka lalace: 1378

    Ƙuri'un da aka kaɗa: 61,430

    Yawan ƙuri'un jam'iyyar APC da PDP:

    APC: 18218

    PDP: 41030