Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An fara tattara alƙaluman zaɓe a Edo

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi zaɓen gwaman jihar Edo da ke Najeriya da ƙarin labarai.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Mustapha Musa Kaita

  1. Yadda wasu 'yan Arewacin Najeriya suka yi zaɓe a Edo

    Wasu 'yan Arewacin Najeriya mazauna jihar Edo su ma sun kada kuri'arsu a zaben na jihar ta Edo. Ibrahim Isa ya tattauna da wasu da wasu daga cikinsu.

  2. Gwamna Obaseki na Jam'iyyar PDP ya jefa ƙuri'arsa

    Bayanan da muke samu daga wakilanmu a jihar Edo na cewa gwamna Godwin Obaseki kuma ɗan takarar Jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan da ke wakana ya jefa ƙuri'arsa.

    Sai dai gwamnan ya koka cewa "na tsaya kan layi har tsawon minti 90, ana samun tsaiko a wajen tantance katinan zaɓe a mazaɓata."

    Gwamnan dai ya isa wajen zaɓen ne tare da mai ɗakinsa Betsy Obaseki

    Za dai a rufe rumfunan zaɓe da ƙarfe 2:00 na rana amma idan aka samu mutanen da suke kan layi waɗanda basu kai ga yin zaɓ ba, INEC za ta ƙara tsawaita lokacin zaɓen.

  3. China na shirin ƙaƙaba wa kamfanonin waje takunkumi

    China ta sanar da cewa za ta ƙaƙaba takunkumi kan kamfanonin kasashen waje da kuma mutanen da ake ganin sun cutar da muradun ƙasar.

    Ana kallon wannna lamarin a matsayin wata ramuwar gayya ga Amurka.

    A ranar juma'a ce Amurka ta ce za ta fara dakatar da kamfanonin China - TikTok da WeChat.

    Wannan sabon tsarin na China ya ba ta damar cin tarar kamfanonin ƙasashen waje ko kuma ta hramta musu yin cinikayya ko zuba jari a China.

    Kawo yanzu ba a sanar da sunayen ɗaya daga cikin kamfanonin wajen ba da wannan takunkumin ya shafa.

  4. Ana zaben gwamna a jihar Edo

    A yau ne jama'ar jihar Edo suka fita domin zaben gwamna tsakananin 'yan takarar da suka hada da Ize Iyamu na APC da Godwin Obaseki na PDP dake neman a sake zabensa karo na biyu.

    Duk wanda ya yi nasara a cikin masu takarar gwamna, to shi ne zai jagoraci jihar tsawon shekara hudu masu zuwa.

  5. Hatsaniya ta ɓarke a mazaɓar Gwamna Obaseki

    Wata hatsaniya ta ɓarke a mazaɓar gwamnan Edo, Godwin Obaseki bayan wani mutum ya yi ƙoƙarin ta da ƙura.

    Wakilan BBC sun rawaito cewa lamarin ya faru ne bayan da Obaseki ya isa makarantar Emokpae da ke ƙaramar hukumar Oredo domin kaɗa ƙuri'arsa.

    Rahotanni na cewa tuni aka yi waje da mutumin domin gudun abin da ka je ya zo.

  6. Zaɓen Edo: Gwamna Godwin Obaseki ya isa rumfar zaɓe

    Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya bi sahun masu kaɗa ƙuri'a a makarantar firamare ta Emokpae a ƙaramar hukumar Oredo.

    Obaseki shi ne ɗan takarar Jam'iyyar PDP kuma yana neman kujerar ce a karo na biyu.

  7. Zaɓen Edo: Jami'an INEC na yi wa masu zaɓe gwajin zafin jiki saboda korona

    Bayanai daga jihar Edo da ke Kudancin Najeriya na cewa Jami'an hukumar zaɓe INEC na yi wa masu zaɓ gwajin zafin jiki kafin su kaɗa ƙuri'a domin cika ƙa'idojin tsare kai daga annobar korona.

    Baya ga zafin jiki, jami'an na ba wa masu kaɗa ƙuri'ar man wanke hanni kafin a tantance su.

    Kwamishinar hukumar zaɓe a Edo May Agbamuche- Mbu wey ta jaddada buƙatar ba da tazara tsakanin masu zaɓe da ke kan layi a wata mazaɓa da ke makarantar Western Bous a Ikpoba Ohka.

  8. Zaɓen Edo: Ɗan takarar APC ya jefa ƙuri'arsa

    Wakilan BBC da ke can jihar Edo sun bayyana cewa ɗan takarar gwamna a jihar ƙarƙashin Jam'iyyar APC Ize Iyamu ya kaɗa ƙuri'a.

    Ize-Iyamu ya shaida wa BBC cewa duk da akwai alamun mata basu fita sosai ba don yin zaɓe, a ƙarshe za a fi samun matan da suka fita kaɗa ƙuri'a a kan maza.

    Ya bayyana cewa wasu matan za su fara zuwa gona ne kafin daga bisani su je yin zaɓe kasancewar mafi yawa manoma ne.

  9. Yadda masu buƙata ta musamman ke zaɓe a Edo

  10. Babu alamun gushewar cutar korona – WHO

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargaɗin cewa har yanzu babu alamun gushewar cutar korona.

    Wani babban jami'in hukumar Mike Ryan ya bayyana ƙaruwar waɗanda ke mutuwa sakamakon cutar zuwa 50,000 a kowacce rana a matsayin abin tsoro.

    Ryan ya faɗawa wani taro da aka gudanar ta bidiyo a Geneva cewa akwai jan aiki a gaba, matsawar gwamnatoci na son rage yaɗuwar cutar da kuma kare marasa galihu.

    WHO ta ce yayin da yawan wanda suka kamu ya haura miliyan 30, sannan yawan waɗanda suka mutu ke riskar miliyan ɗaya, dole ne ƙasashen duniya su tashi tsaye kafin a kai ga kawo ƙarshen cutar.

  11. Hotuna: Yadda zaɓen gwamna a Edo ke kankama

  12. Yau ake zaben gwamna a Edo

    Yau al’umar Edo ke kaɗa ƙuri’a domin zaɓen sabon gwamna a jihar da ke Kudancin Najeriya.

    `Yan takara 14 ne suke neman kujerar ta gwamna sai dai 'yan takara biyu da su ne kan gaba sun haɗa da Godwin Obaseki na Jam'iyyar PDP, wanda kuma shi ne gwamnan jihar a halin yanzu, sai kuma Fasto Osagie Ize-Iyamu na Jam'iyyar APC.

    Jami'in watsa labarai na hukumar zaɓe a Najeriya, Nick Dazang ya shaida wa BBC cewa akwai rumfunan zaɓe 3,035 sannan akwai sama da mutum miliyan biyu da aka yi wa rajistar zaɓen.

    "Mutum miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai da ashirin da shida da ɗari bakwai da talatin da takwas sun karɓi katin zaɓen." in ji Dazang.

    Me ya sa zaɓen Edo ke da muhimmanci?

    Zaɓen jihar Edo na zagaye da ce-ce-ku-ce da kuma ruɗani irin na siyasa.

    Domin fahimtar me ya sa siyasa ta ɗauki zafi a jihar, ya kamata a gane cewa siyasa tamkar wani wasa ne na wa ya fi yawan jama'a. Duk Jam'iyyar da ta kasance ta fi yawan jihohi a Najeriya, to lallai ita ce kan gaba.

    Cikin jihohi shida na yankin kudu maso kudancin Najeriya, jihar Edo ce kaɗai ke da gwamna ɗan APC, a kwanakin baya kuma gwamnan ya tsallaka zuwa PDP, hakan na nufin PDP ce ke da kudu maso kudancin Najeriya baki ɗaya.

    Hakan kuma ya sa yawan jihohin da APC ke riƙe da su a Najeriya gaba ɗaya sun koma 20 daga 21.

    Latsa nan don karanta abubuwan da ya kamata ku sani kan zaɓen na 19 ga Satumbar 2020.

  13. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya. Da fatan mun wayi gari lafiya.

    Nabeela Mukhtar Uba ce ke tare da ku a shafin labarai kai-tsaye inda a ciki za mu riƙa wallafa labaran da suke wakana a sassan duniya musamman Najeriya da maƙwabtanta.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da mu.