An fara tattara alƙaluman zaɓe a Edo

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi zaɓen gwaman jihar Edo da ke Najeriya da ƙarin labarai.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labarai da rahotannin da muka wallafa a wannan shafin:

    • Yadda wasu 'yan Arewacin Najeriya suka yi zaɓe a Edo
    • Zaɓen Edo: Bidiyon yadda makafi suke kaɗa ƙuri'a
    • Adams Oshiomhole kan layin jefa ƙuri'a
    • 'Na yi zaton INEC ta shirya wa zaɓen Edo'
    • Obaseki na PDP ya lashe rumfar zaɓensa
    • APC ta doke PDP a rumfar zaɓen Ize-Iyamu
    • An fara tattara alƙaluman zaɓe a Edo

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai

  2. Rahoto na musamman daga Edo kan zaɓen jihar

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren rahoton Ibrahim Isa daga Edo
    Bayanan sautiRahoto na biyu
  3. Shugaban Rasha ya karrama wanda ya ƙirƙiro wa ƙasar babban makami mai linzami

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya gabatar da lambar yabo mafi girma ta ƙasar ga Herbert Efremov, wanda ya ƙirƙiri wani babban makami mai linzami wanda shugaban ya ce karon farko a tarihi ya ƙara ɗaga darajar Rasha a matsayin wadda ta fi ƙarfin makami a duniya.

    A wani taro na bidiyo, Mista Putin ya kwatanta Mista Efremov da masanan da suka ƙera wa Daular Soviet makaman ƙare dangi.

    Shugaba Putin ya ce babban makamin ya sha gaban na kowace ƙasa, wanda ba za a iya kakkaɓowa ba.

    Shugaban ya ce matakin da Tsohon Shugaban Amurka, George W. Bush, ya ɗauka na ficewa daga yarjejeniyar haramta makamai masu linzami a 2002, shi ya tursasa wa Rasha ƙera nata babban makamin domin taka wa Amurka burki.

  4. Annobar korona ta fi yaƙi illa ga harkar fetur cikin shekaru 60 – Barkindo

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren shirin
  5. An fara tattara alƙaluman zaɓe a Edo

    ..

    Tun ƙarfe 2:30 na rana kusan duka rufunan zaɓen da ke ƙananan hukumomi 18 na Edo suka rufe tantance masu zaɓe inda kuma wasu a lokacin suka fara ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa.

    Sai dai akwai wasu rumfunan zaɓen kayayyakin zaɓe ba su isa da wuri ba, wanda hakan ya sa ba su fara zaɓe da wuri ba.

    Tuni wasu rumfunan zaɓen suka ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa, inda Jam'iyyu biyu da suka fi shahara na APC da PDP ke nasara.

    A yanzu dai an fara kai akwatuna gundumomi inda ake tattara alƙaluman zaɓe.

    Gwamnan jihar Godwin Obaseki ne ke takara ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, sai kuma Fasto Osagie Ize-Iyamu ƙarƙashin Jam'iyyar APC.

    Sakamakon farko-farko da ya fara fitowa ya nuna duka 'yan takarar sun lashe rumfunan zaɓensu.

    ..
  6. 'An kashe mambobin Taliban 30 a Afghanistan'

    Jami'ai a arewacin lardin Kunduz da ke Afghanistan, sun bayyana cewa akalla mutum 20 suka mutu bayan wani hari da aka kai ta sama kan 'yan Taliban.

    Sai dai sanarwa daga ma'aikatar tsaro ta ƙasar ta bayyana cewa, an kashe mambobin Taliban 30, haka kuma ana ci gaba da bincike kan zargin da ake yi na kashe farar hula.

    Gwamnan lardin Kunduz ya shaida wa BBC cewa, cikin waɗanda suka mutu da alama akwai farar hula.

    Harin na farko da aka kai, an kai shi ne kan wani babban wuri na 'yan ƙungiyar Taliban.

    Harin na biyu kuma ya samu mutanen da ke ƙasa waɗanda suka ruga domin su gano waɗanda suka samu rauni da kuma waɗanda suka mutu.

    Wannan rikicin na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Taliban da kuma Jami'an Gwamnatin Afghanistan ke tattaunawar sulhu a Qatar.

  7. Wata mata ta faɗo daga mota saboda Snapchat

    ...

    Asalin hoton, Google

    Wata mata ta faɗo daga cikin mota kan babbar hanya yayin da take naɗar bidiyon da za ta ɗora a manhajar Snapchat a gundumar Surrey da ke Ingila.

    Matar ta faɗo ne a daidai lokacin da ta fito da jikinta ta tagar mota tana naɗar bidiyo, sai dai 'yan sanda sun bayyana cewa matar ba ta ji rauni sosai ba.

    Jami'an bayar da agajin gaggawa sun bata magunguna a wurin da lamarin ya faru, kuma sun ce ba ta samu wani rauni da zai yi barazana ga rayuwarta ba.

  8. An kama tsohon jami'in gwamnatin CAR kan laifukan yaƙi

    CAR

    Asalin hoton, AFP

    'Yan sanda a Faransa, sun kama wani tsohon mai tsaron shugaban ƙasa daga Afrika ta Tsakiya CAR bisa zargin aikata laifukan yaƙi da kuma cin zarafin bil adama.

    Ana kuma zargin Eric Danboy Bagale da azabtar da mutane a lokacin da yake tare da Shugaban ƙasar na lokacin wato Francois Bozize.

    Ana zarginsa da jagorantar gungun mayaƙa mabiya addinin kirista waɗanda kuma suka aiwatar da kashe-kashen ramuwar gayya bayan da aka hamɓarar da shugaban CAR a 2013.

    Dubban jama'a ne suka mutu a rikicin da ya biyo baya.

  9. Zaɓen Edo:Yadda ake soke takardun jefa ƙuri'un da ba a yi amfani da su ba

    ..
  10. Hotuna:Yadda masu dafa abinci ke cin kasuwa a rumfar zaɓe

    Edo
    Edo
    Edo
    Edo
  11. Labarai da dumi-dumi, APC ta doke PDP a rumfar zaɓen Ize-Iyamu

    ..

    Ɗan takarar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, shi na ya lashe rumfar zaɓensa, kamar yadda takwaransa na PDP Godwin Obaseki ya lashe tasa.

    Ize-Iyamu na Jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 292, sai kuma Obaseki na PDP ya samu ƙuri'u 21.

  12. Labarai da dumi-dumi, Obaseki na PDP ya lashe rumfar zaɓensa

    ..

    Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya samu nasara a rumfar zaɓensa da ya jefa ƙuri'a inda Jam'iyyarsa ta PDP ta samu ƙuri'u 184, sai kuma APC ta samu 62, sai kuma ADP 2.

    Jam'iyyar Labour kuma ta samu 1, sai kuma ƙuri'u 5 da suka lalace.

  13. Hotuna: An fara tantance ƙuri'un da a aka kaɗa a mazabar Obaseki

    Edo
    Edo
    Bayanan hoto, Masu zaɓe tsai-tsaye a gefe suna sa ido kan yadda ake tantance ƙuri'un da ka kaɗa
    Edo
    Edo
    Bayanan hoto, An fara tantance ƙuri'u a mazaɓa ta 4 rumfa mai lamba 22 yayin da aka kammala jefa ƙuri'a
  14. Davido ya yi addu'a ga masu zaɓe a Edo

    /...

    Asalin hoton, INSTAGRAM: @DAVIDOOFFICIAL

    Shahararren mawaƙin nan ɗan Najeriya, Davido ya yi addu'a ga mutanen da suka fita kaɗa ƙuri'a a zaɓen da ke gudana a jihar Edo.

    Mawaƙin ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. An tuhumi fitattun 'yan siyasa a Habasha da hannu a aikata ta'addanci

    Etrhiopia

    Babban Lauyan Habasha ya tuhumi wasu mutum 24 kan ta'addanci da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a ƙarshen watan Yuni.

    Mutanen sun haɗa da wasu fitattun 'yan siyasar yankin Oromo guda biyu Bekele Gerba da Jawar Mohamed - waɗanda suka mallaki kafafen yaɗa labarai masu tasiri.

    Wata sanarwa daga babban lauyan ta ce baya ga tuhumar aikata ta'addanci, ana zargin mutanen da wasu laifukan na daban.

    Lauyan Mr Jawar ya bayyana zarge-zargen a matsayin waɗanda basu da tushe.

    Dubban mutane aka cafke sakamakon rikicin ƙabilanci da ya faru sanadin kisan fitaccen mawaƙin nan Hachalu Hundessa a watan Yuni.

  16. 'Na yi zaton INEC ta shirya wa zaɓen Edo'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya bayyana cewa ya yi zaton INEC za ta yi kyakkyawan shiri game da zaɓen Edo na 2020, ya ce bai ji daɗi ba sakamakon yadda na'urar tantance masu zaɓe ke tafiyar hawainiya, banda haka ya ce ya shafe sama da sa'a ɗaya kafin ya yi zaɓe.

    "Na yi zaton INEC ta shirya wa zaɓen nan, na yi jiran awa ɗaya da rabi kan layi kafin na jefa ƙuri'a, abin ba daɗi," in ji Gwamna Obaseki.

    "Ganin cewa wannan zaɓen na rana ɗaya ne, na yi zaton za a fi shirya wa zaɓen. Na'urar tantance masu zaɓe ba ta sauri, kuma haka abin yake a kowace mazaɓa."

  17. Masu sa ido kan zaɓe sun yaba wa Gwamna Obaseki

    ..

    Masu sa ido kan zaɓe sun jinjina wa Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, sakamakon tsawaya kan layi na lokaci mai tsawo kuma cikin rana domin jefa ƙuri'arsa.

    Wasu daga cikin su sun shaida wa BBC cewa hukumar INEC ta yi ƙoƙari wurin bin ƙa'idojin da hukumar NCDC ta gindaya kan annobar korona, amma dai duk da haka mutane sun ƙi bayar da tazara a tsakani.

    Masu kaɗa kuri'a da dama sun saka takunkumi, suna tsaftace hannunsu da mai na sanitizer tare da bari ana duba zafin jikinsu kafin su jefa ƙu'ria.

  18. Adams Oshiomhole kan layin jefa ƙuri'a

    ..

    Tsohon Gwamnan Edo kuma Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na Najeriya Adams Oshiomhole kenan kan layin jefa ƙur'ia a mazaɓarsa.

    Mista Oshiomhole dai ya raba gari da gwamnan jihar Godwin Obaseki inda yake goyon bayan ɗan takarar APC Fasto Osagie Ize-Iyamu.

  19. Yadda aka samu hatsaniya a mazaɓar gwamnan Edo

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  20. Zaɓen Edo: Bidiyon yadda makafi suke kaɗa ƙuri'a

    Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda makafi suke zabe