Ambaliyar ruwa na barazana ga gidan Firimiyan Sudan
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Rufewa
A nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai
tsaye kan abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya a wannan shafin.
Za ku iya zuwa har ƙasan shafin domin sanin abubuwan da
suka faru a ranar Litinin.
Sai ku kasance da mu zuwa gobe Talata inda za mu shafe
yini muna kawo labarai da rahotanni kai tsaye.
Bayanan hoto, Dorinar Ruwa da aka gani a wani ƙauyen Kebbi bayan ambaliyar ruwa
Ambaliyar ruwa na barazana ga gidan Firaministan Sudan
Asalin hoton, @dabangasudan.org
Bayanan hoto, Ambaliya a layin El Kadaro, Khartoum ta arewa a Sudan
Rahotanni daga Sudan sun ce ambaliyar ruwa ta mamaye wani ɓangare na gidan Firimiyan ƙasar Abdalla
Hamdok da ke arewacin Khartoum da ambaliyar ta mamaye.
Kafar yada labarai ta Radiyo Dabanga wani ɓangare na Radio Darfur ta ce ruwan kogin
Nilu da suka haifar da ambaliyar sun shiga gidan Firimiyan daga bayan gidansa.
Sai dai majiyar ta ce ambaliyar ba ta yi ɓarnar da har iyalansa za su
ƙauracewa gidan ba.
Ambaliyar ta yi sanadin rushewar gidaje sama da 120 a yankin Karari a
Omdurman.
Ma’aikatar kula da harakokin cikin gidan Sudan ta ce ambaliyar ta yi
sanadin mutuwar mutum sama da 100 yayin da kuma ta raba daruruwa da gidajensu.
Aƙalla gidaje 100,000 ambaliyar ta rusa, a cewar Radiyo Dabanga, kuma
Dubban ƴan Sudan ne ke matukar bukatar agajin abinci da wuta da magani yayin da
suke rayuwa a wasu rumfunan da suka samar.
Yawan masu korona sun haura miliyan ɗaya a Spain
Spain ta zama kasa ta farko a yammacin Turai da ke da yawan masu korona suka
zarta miliyan ɗaya
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da miliyoyin yara a fadin kasar suka koma
makaranta.
Sai dai duk da haka ministan lafiya na ƙasar ya ce adadin masu mutuwa
sakamakon cutar ya ragu, amma ta fi kama matasa a yanzu waɗanda ba su nuna
alamun kamuwa da cutar.
Wani jami'i a cibiyar lafiya ta Spain ya ce zai fi kyau a
sanya dokar kulle ta cikin gida maimakon ta kasa da kasa.
Kimanin mutum dubu 30 ne suka mutu a Spain sakamakon cutar.
Alexei Navalny jagoran adawar Rasha ya ɗan farfaɗo a asibiti
Asalin hoton, Reuters
Asibitin kasar Jamus da ke kula da jagoran adawar Rasha da aka sawa guba Alexei Navalny, ya ce
majinyacin ya dawo cikin hayyacinsa, kuma yana iya amsa magana.
Asibitin Charite da ke Berlin ya ce ana cire wa Mista
Navalny na’urar taimaka wa nunfashi a hankali, amma likitoci ba za su iya yanke
cewa har zuwa yaushe zai iya samun sauki ba.
An yi amannar cewan an sanya
wa Navalny wata guba ne mai kashe laka nau’in Novichok a cikin jirgi, yayin
wata tafiya da ya yi a watan da ya gabata.
Jamus na duba yiwuwar
kakaba wa Rasha takunkumi - sai dai fadar gwamnatin Rasha Kremlin ta musanta da
hannunta a cikin lamarin.
Ambaliya ta kashe mutum kusan 60 a Nijar
Asalin hoton, @niameyetles2jours
Akalla mutu m 57 suka
mutu yayin da dubbai suka gujewa gidajensu sakamakon ambaliya da ruwan sama da
aka shafe makwanni ana makawa ya haifar a Nijar kamar yadda Kamfanin dillanin
labaru na Nijar et les Deux Jours ya
ruwaito.
Alkalumman baya-bayan
nan da aka fitar sun nuna cewa ambaliyar ta shafi gidaje 34,000 yayin da
ambaliyar ta shafe gidaje da dama.
Kamfanin dillacin
labarun ya ce jimillar kauyuka 587 ambaliyar ta shafa a sassan Nijar da suka
hada da kauyukan Yamai babban birnin ƙasar.
Kotun Saudiyya ta soke hukuncin kisa kan kisan Khashoggi
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Saudiyya
ta sauya hukuncin kisa da aka yanke a bara kan wasu mutane biyar da ake zargi
da kisan Jamal Khashoggi.
Maimakon haka yanzu kotun ta yanke wa mutanen
biyar hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari, yayin da kuma uku aka yanke musu
hukuncin ɗaurin shekara bakwai zuwa 10.
An soke hukuncin
kisan ne bayan ƴan uwan Khashoggi sun yafe wa waɗanda suka kashe shi.
Majalisar Dinkin
Duniya ta bayyana hukuncin na rashin
adalci da baya kan doka.
Kashe Mista Khashoggi
kusan shekaru biyu da suka gaba da wasu jami’an Saudiyya suka yi a wani ƙaramin
ofishin jekadancinta a Istanbul ya nuna alamar tambaya kan Yariman ƙasar mai
jiran gado Mohammed bin Salman wanda ya musanta hannunsa a kisan.
Messi ya yi atisaye a filin wasan Barcelona
Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi ya koma atisaye a filin wasan Barcelona bayan da ya fasa shirinsa na barin kungiyar.
Messi, mai shekara 33, ya mika wa Barcelona takardar saki ranar 25 ga watan Agusta sai dai ranar Juma'ar da ta wuce ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a Barcelona, sakamakon ba zai yiwu wata ƙungiya ta iya biyan farashin da Barcelona take nema a kansa ba.
Wannan ne karon farko da dan kasar ta Argentina ya yi atisaye tare da abokansa da ke kungiyar tun bayan zuwan sabon koci Ronald Koeman.
Barcelona za ta yi wasanta na farko a La Liga ta bana ranar 27 ga watan Satumba inda za ta fafata da Villarreal.
'Mutum miliyan 50 za su yi fama da yunwa' a Kudancin Afirka
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin kasashen duniya sun yi gargadi game da karancin abinci da ake fama da shi a kudancin Afirka, suna masu cewa mutum kusan miliyan 50 na cikin kasadar fama da yunwa.
Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasashen Malawai, Mozambique, Zambia da Zimbabwe su ne lamarin ya fi shafa.
Kasashen sun yi fama da fari a 2019 sannan farin-dango sun mamaye su a wannan shekarar.
Kazalika yankin yana fama da tabarbarewar tattalin arziki sakamakon kullen da aka sanya saboda hana yaduwar cutar korona.
Hukumomin agaji sun kara yawan tallafin da suke bayarwa kasashen da zummar dakile matsalar ta yunwa.
Jam'iyyar adawa ta gindaya wa gwamnatin Kamaru sharuɗa kan zaɓe, Mohaman Babalala daga Garoua
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Mohaman Babalala daga garin Garoua
Jam’iyar adawa ta SDF a Kamaru ta gindaya wa gwamnati sharaɗi biyu da ya kamata ta cika kafin jam’iyyar ta shiga jerin zaɓukan larduna da za a yi nan gaba.
SDF ta ce har yanzu Kotun Ƙoli ba ta warware ƙararrakin da ta shigar a gabanta ba tun lokacin tagwayen zaɓukan ‘yan majalisar dokoki da na ƙananan hukumomi da suka gudana a watan Fabarairu.
Har wa yau, jam’iyyar na buƙatar gwamnati ta fara tabbatar da tsaro a yankin rainon Ingila sannan kansilolinta za su samu damar fita kaɗa ƙuri’a cikin kwanciyar hankali.
Minti Daya Da BBC Na Rana
Ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraren Minti Daya Da BBC Na Rana.
Bayanan sautiMinti Ɗaya da BBC na rana 07/09/2020
Ana zargin ƙungiyar IPOB da kashe Hausawa a Jihar Rivers
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga jihar Rivers da ke kudancin Najeriya sun rawaito cewa ana zaman dar-dar bayan an kashe wasu Hausawa guda biyu.
Ana zargin ‘yan kungiyar IPOB da ke neman ɓallewa daga Najeriya da kai wa Hausawan mazauna unguwar Oyigbo hari a Ƙaramar Hukumar Oyigbo.
Ya zuwa yanzu 'yan sandan Rivers ba su bayyana adadin waɗanda aka kashe ba a harin duk da cewa sun tabbatar wa da BBC faruwarsa.
Sai dai ƙungiyar ta IPOB ta nesanta kanta daga faruwar wannan rikici.
Shugaban 'yan arewa mazauna Kudu maso Gabashin Najeriya Alhaji Musa Sa'idu wanda kuma ya shaida lamarin, ya faɗa wa BBC cewa wannan hari shi ne na biyar da ƙungiyar ta kai wa Hausawa a yankin.
"Sun harbi mutum biyar sannan suka sassari mutum huɗu, inda biyu suka mutu ranar Lahadi kuma shi ne [karo] na biyar," in ji shi.
Alhaji Musa ya yi kira ga mutane da kada su yi ramuwar gayya a kan al'ummar Igbo mazauna arewa.
Lauyan ƙungiyar ta IPOB ya ce wasu ne suka kai harin domin su ɓata musu suna.
Hukumomin duniya na gargadin fuskantar matsalar abinci a kudancin Afrika
Asalin hoton, get
Hukumomin duniya na gargadin fuskantar matsalar abinci a kudancin Afrika, inda suka ce sama da mutum miliyan 50 na cikin hadari.
Wakiliyar BBC ta ce ana kallon karuwar matsalar abincin a matsayin wata masifa kamar yadda hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, wanda hakan zai fi shafar kasashen Malawi da Mozambique da Zambia da kuma Zimbabwe.
An samu mummunan fari na kusan shekara 29 wanda kuma farin dango suka kara ta'azzara shi a yankin kudancin nahiyar.
Yankin na fuskantar matsalar tattalin arziki wanda dokar kulle ta annobar korona ta janyo.
Sojoji 20 sun rasa rayukansu a Yemen
Rahotanni daga Yemen na cewa sojojin sama da 20 ne suka rasa rayukansu a wani rikici da ya barke tsakanin mayakan 'yan tawayen Houthi da kuma dakarun da suke yi wa gwamnatin da kasashen duniya suka yarda da ita yaki.
An yi wannan rikici ne a yankin al-Jawf da ke arewacin kasar, wanda dakarun gwamnati ke kokarin kwatowa daga hannun 'yan tawayen Houthi wadanda suka kwashe watanni shida suna iko da shi.
Wata majiya daga sojojin gwamnati ta ce an kashe mayakan 'yan tawayen Houthi 14, kuma takwas daga cikin sojojin gwamnati sun rasa rayukansu a gwabzawar da aka yi a yammacin Lahadi.
An sako Sarkin Sarakunan Fulani Usman Adamu
Asalin hoton, Getty Images
A
Najeriya, an sako Alhaji Usman Adamu, Sarkin Sarakunan Fulani wato Arɗon Arɗoɗi na Jihar Kwara, wanda wasu 'yan bindiga suka sace a safiyar Alhamis
da ta gabata.
An yi garkuwa da sarkin ne a kan hanyarsa ta shiga garin Ilori, babban birnin jihar.
A
daren jiya ne aka sako basaraken a dajin Makwa na Jihar Neja a kan hanyar zuwa
garin Kainji ba tare da an bayar da kuɗin fansa ba.
A
yanzu Alhaji Usman Adamu yana asibiti, inda ake yi masa magani sakamakon duka da aka yi masa. Sai dai babu rauni ko
karaya a jikin nasa.
Sace
sarkin sarakunan na Fulani makiyaya ya ƙara fito da irin yadda sace-sacen
jama'a ke ci gaba da yin ƙamari a arewacin Najeriya kuma babu wanda ya tsira
daga wannan matsalar.
China na son kafa sansanonin soja a ƙasashen Afrika huɗu
Asalin hoton, Getty Images
China tana tunanin kafa sansanin soja a kasashen Afrika
guda huɗu, a cewar rahoto daga Sashen Tsaro na Amurka.
Kenya, Seychelles, Tanzania da Angola suna daga cikin ƙasashe masu yawa da China
ke tunanin kafa sanasanin.
Ya zuwa yanzu gwamnatin kasashe huɗun ba su ce komai game da rahoton ba.
Rahoton da aka wallafa a makon da ya gabata, ya karaɗe duniya a karshen
mako, inda wasu daga cikin kasashen da za a kafa sansanonn suka musanta cewa suna tattaunawa da
China.
“Bayan sansaninta a ƙasar Djibouti, PRC [People's Republic of China] na tunanin ta kafa
wasu sansanonin soja don tallafa wa sojojin ruwa da na sama da na
kasa," in ji wani bangare na rahoton.
Cire tallafi wajibi ne kuma tarihi ba zai manta da Buhari ba - Garba Shehu
Asalin hoton, Garba Shehu
Biyo bayan sukar da wasu 'yan Najeriya suke yi wa Gwamnatin Tarayyar Najeriya game da tsadar kayayyaki, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar ya ce matakan da aka ɗauka ne suka jawo hakan waɗanda kuma "suka zama dole".
Malam Garba Shehu ya ce tarihi ba zai taɓa mantawa da sauye-sauyen da Shugaba Buhari ya kawo ba sakamakon daƙile cin hanci da rashawa a ɓangaren tallafi a kan man fetur da noma da wutar lantarki ta hanyar cire tallafin.
Sai dai cire tallafin ya jawo hauhawar farashin kaya musamman man fetur, wanda gwamnati ta ƙara zuwa naira 151 daga 148, yayin da 'yan kasuwar da ke sayar da man suka ce sai farashinsa ya kai kusan 160 kan kowacce lita ɗaya.
Kakakin shugaban ƙasar ya ce tun tuni ya kamata gwamnatocin baya su cire tallafin amma saboda "ba su da ƙarfin zuciyar yin hakan" sai suka gaza.
"Za a riƙa tuna Shugaba Buhari kan yadda ya kawo cigaban ƙasa da tattalin arziki ta hanyar daƙile cin hanci da rashawa a ɓangaren kuɗaɗen tallafi," in ji Garba Shehu a cikin wata maƙala da ya wallafa ranar Lahadi.
Mutum ya haddasa gobara a gidansa a ƙoƙarin kashe ƙuda
Asalin hoton, Getty Images
Wani mutum ya ƙona wani ɓangare na gidansa a Faransa a ƙoƙarin kashe ƙuda.
Mutumin mai shekara 80 da wani abu, yana ƙoƙarin fara cin abinsa na dare yayin da ya ji wani ƙuda na yi masa kuwwa a kunne.
Sai kawai ya ɗauki wata ragar kashe ƙwari ta lantarki ya fara kai masa duka, ashe tukunyar gas na ɗiga a gidan ba tare da ya sani ba.
Lantarkin da ke jikin ragar ya haɗu da gas ɗin, abin da ya haddasa fashewa wadda tarwatsa ɗakin girki da kuma wani ɓangare na rufin gidan da ke ƙauyen Parcoul-Chenaud.
A cewar rahoton wata kafar yaɗa labarai a garin, mutumin wanda ba a faɗi sunansa ba ya tsallake tare da ƙuna maras yawa a jikinsa.
Sai dai ba a san halin da ƙudan yake ciki ba zuwa yanzu, a cewar kafar Sud-Ouest.
Mutumin ya koma wani sansani da zama yayin da iyalansa ke gyara gidan.
Likitoci sun fara yajin aiki a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Likitoci masu neman ƙarin ƙwarewar aiki a Najeriya sun fara yajin aikin sai baba ta gani domin neman ƙarin albashi da kulawa da kuma ƙarin kayan aiki.
Yajin aikin wanda ƙungiyar likitocin ta National Association of Resident Doctors (Nard) ta shiga, shi ne na baya-bayan nan cikin jerin irinsa a ƙasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Nahiyar Afirka.
Fiye da kashi ɗaya cikin uku na likitocin ƙasar guda 42,000 ne za su shiga yajin aikin, yayin da take fafutikar kawo ƙarshen annobar cutar korona.
Shugaban ƙungiyar Aliyu Sokomba ya faɗa wa BBC cewa wasu daga cikin likitocin da ke kan gaba a yaƙi da annobar za su shiga yajin aikin.
Ya ƙara da cewa ba za a janye ba har sai an biya musu buƙatunsu.
Buhari ya isa Yamai na Jamhuriyar Nijar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Buhari yana halartar taron ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma na kwana ɗaya da ake yi a yau Litinin.
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Tun a watan Afrilun 2020 ne shugabannin ƙungiyar ta Ecowas suka zaɓi Buhari a matsayin jagoran yaƙi da annobar korona.
Fasinjoji sun ƙone ƙurmus a Anambra sakamakon hatsarin mota
Asalin hoton, FRSC
Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa fasinjoji sun ƙone ƙurmus sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su ta yadda ba za a iya gane su ba.
Mista Andrew Kumapayi ya faɗi hakan ranar Lahadi kuma ya ƙara da cewa har zuwa yanzu ba su san takamaiman adadin waɗanda suka rasu ba saboda ƙonewar da suka yi.
Hatsarin ya faru ne ranar Lahadi a kan titin Ihiala-Onitsha a Jihar Anambra, inda abin hawansu ya kama da wuta.
"A yammacin nan (Lahadi) wani hatsari da ya rutsa da mota ɗaya ya faru sakamakon fashewar taya saboda tsananin gudu. Abin hawansu ya yi alkafira sannan kuma ya kama da wuta," in ji shi.
"Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa dukkanin fasinjojin sun ƙone ta yadda ba za a iya gane su ba."