Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Najeriya ta mayarwa Ghana martani kan 'cin zarafin 'yan kasarta'

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Jirgi mara matuƙi na Daular Larabawa ya kashe sojoji 26 a Libiya

    BBC ta samu wasu sabbin bayanai da ke nuna cewa wani jirgi mara matuƙi mallakar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya kashe wasu masu koyon aikin soja 26 a Libiya.

    Sojojin da aka kashe ba su riƙe da makamai a lokacin da aka kai musu hari a Tripoli babban birnin ƙasar a Janairun wannan shekara.

    .A lokacin da aka kai harin, rundunar Janar Khalifa Haftar ta zagaye birnin na Tripoli. Janar Haftar dai na da kyakkyawar alaƙa da Daular Laraba.

    Har yanzu ƙasar da ke yankin Gulf ba ta mayar da martani ba kan binciken da BBC ta gudanar.

    Tun a baya dai, Janar Haftar da Daular Larabawa sun musanta kai wannan hari. Haka zalika Daular Larabawan ta musanta duk wani zargi da ake yi mata na cewa tana da hannu kan abin da sojojin Libiya ke yi.

    Ƙasar ta ce tana goyon bayan shirin da Majalisar Ɗinkin Duniya take yi na samar da zaman lafiya.

  2. Tsawa ta kashe yara 10 a Uganda

    Tsawa ta kashe yara 10 a garin Arua da ke arewa maso yammacin Uganda. An kwana biyu ana zabga ruwan sama a yankin tare da walƙiya da tsawa.

    Ruwan da aka yi mai ƙarfi a ranar Alhamis ya ja yaran suka bar ƙwallon ƙafar da suke bugawa domin rakuɓewa ƙarƙashin wata bukka.

    Ana cikin ruwan ne sai tsawa ta faɗa kan bukkar. Yara tara da ke tsakanin shekara 13 zuwa 15 suka mutu nan take, sai kuma ɗayan yaron ya mutu a hanyar kai shi asibiti.

    Yara uku da suka tsira na jinya a wani asibiti da ke yankin.

    Makamancin wannan lamarin shi ne ma fi muni da ya faru a Uganda tun bayan makamancin hakan da ya faru a 2011.

  3. An kai wa R. Kelly hari a gidan yari

    Lauyan shahararren mawaƙin nan R. Kelly ya buƙaci a saki wanda yake karewa daga gidan yari sakamakon harin da wani ɗan fursuna ya kai mashi.

    Steve Greenberg, wanda shi ne lauyan R. Kelly, ya bayyana cewa an kai wa wanda yake karewa hari ne a gidan gyara ɗabiu na Chicago, wanda a wurin ne R. Kelly ke zaman jiran shari'a.

    Babu wani tabbaci kan irin raunin da aka ji wa R. Kelly yayin harin da aka kai masa, in ji Mista Greenberg a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter,

    R. Kelly dai ya musanta duka zarge-zargen da ake yi masa, ciki har da batun cin zarafin yara ƙanana ta hanyar lalata da kuma safarar mutane domin aikata karuwanci.

  4. Labarai da dumi-dumi, Firaministan Japan Shinzo Abe ya yi murabus

    Firaministan Japan Shinzo Abe ya yi murabus sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

    Ya bayyana cewa ba ya so rashin lafiyarsa ta shafi aikinsa na shugfabanci, ya kuma bayar da hakuri ga mutanen Japan kan gaza gama wa'adinsa na mulki.

    Shinzo mai shekaru 65 ya shafe shekaru yana fama da ciwon hanji, amma ya ce a 'yan kwanakin nan ciwon ya ƙara tsanani.

    A shekarar da ta gabata, ya zama firaminista na Japan da ya fi daɗewa kan mulki.

    Ya fara mulki ne tun daga shekarar 2012.

    Shugaban dai zai ci gaba da mulki har sai an zaɓi sabon Firaministan da zai maye gurbinsa.

  5. Mutum 225,000 sun rasa muhallansu a Nijar saboda ambaliya

    Hukumomi a Jamhuriyyar Nijar sun bayyana cewa ambaliyar ruwa a Niamey babban birnin ƙasar ta raba mutum 225,000 daga muhallansu.

    Adadin waɗanda ambaliyar ta kashe ya kai 45.

    Ruwa ya mamaye wasu sassa na birnin tun a ranar Talata sakamakon Kogin Niger da ya cika.

    Tun bayan lokacin ruwan sama mai ƙarfi ya ci gaba da lalata dukiyoyi.

    Masu bayar da agaji na amfani da jirgin ruwa domin ceto mutane, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    Hukumomi a ƙasar sun ƙara jaddada cewa a watan da ya gabata an yi gargaɗin cewa kusan mutum 300,000 na cikin barazanar samun ambaliya sakamakon an fara ruwan sama mai ƙarfi.

  6. Shugaban Uganda ya ware gobe Asabar a matsayin ranar addu'a kan korona

    Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ayyana gobe Asabar a matsayin ranar addu'a kan annobar korona.

    Shugaban ya ce ya samu wannan shawara ne daga wani ɗan Uganda wanda ya samu ilhama daga ubangiji.

    "Ubangiji ya faɗa mashi cewa da na haɗa addu'a ta musamman ta ƙasa baki ɗaya, domin ubangiji ya kawo mana ƙarshen cutar korona. Na ayyana ranar 29 ga watan Agusta ta 2020 a matsayin ranar hutu kuma ranar addu'a. Ku tsaya a gidajenku ku yi addu'a," a wani saƙo da Museveni ya wallafa a shafin intanet.

    A halin yanzu, mutum 2,679 suka kamu da cutar korona inda mutum 28 aka bayar da rahotn cutar ta kashe.

  7. Messi ya tuntubi Guardiola kafin ya saki Barca

    Shahararren dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, ya tuntubi kocin Manchester City Pep Guardiola a makon jiya inda ya gaya masa cewa yana son barin Barcelona, a cewar jaridar Times - subscription required.

    A shirye Manchester City take ta bayar da 'yan wasan Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, da Angelino, mai shekara 23, a cikin yarjejeniyar dauko Messi. (Manchester Evening News)

    Kazalika Manchester City ta shirya bai wa Barcelona £89.5m tare da 'yan wasan da suka hada da Garcia, Bernardo Silva, da Gabriel Jesus domin karbo Messi. (Sport - in Spanish)

    Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, ya kawar da jita-jitar da ake yi a kansa ta barin Juventus inda ya ce yana shirin buga wasanni na kakarsa ta uku a kungiyar. (Mundo Deportivo - in Spanish).

    Latsa nan don karanta cikakken labarin wasannin:

  8. 'Zai yi wahala yaran da suka kamu da cutar korona su mutu'

    Mawallafan bincike na farko da aka gudanar kan yaran da suka kamu da cutar korona a duniya, sun gano cewa yiwuwar mutuwar kananan yara sakamakon cutar bata taka kara ta karya ba.

    Binciken da aka wallafa a mujallar harkokin lafiya ta Birtaniya ya yi duba kan kusan yara 650 da cutar ta harba a kasar.

    Ya kuma gano cewa yaran da ke da kumari sosai, 'yan kasa da wata ɗaya da kuma yara baƙaƙe sun fi fuskantar barazanar shigar da su sashen bada kulawa ta musamman.

    Masana kimiyyar sun buƙaci iyaye a faɗin duniya su kwantar da hankulansu, saboda bincikensu ya gano cewa da matuƙar wuya takai ga kai 'ya'yansu asibiti saboda cutar korona.

  9. Barkanmu da Juma'a

    Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da Juma'a. Da fatan za ku bibiye mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman game da labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar, da wasu sassa.

    Za ku iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta na Facebook da Twiiter da Instagram