Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Najeriya ta mayarwa Ghana martani kan 'cin zarafin 'yan kasarta'

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Rufewa

    Masu bibiyar mu da haka muke sallama da ku a wannan shafin sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa ku kwana lafiya

  2. Minti daya da BBC na Dare

  3. Amurkawa sun yi gangamin neman ƴancin baƙar fata a birnin Washington

    An gudanar da wani gangamin fafutukar neman ƴancin baƙar fata a birnin Washington na Amurka.

    Fitaccen dan gwagwarmayar nan, Al Sharpton na daga cikin wadanda suka halarci gangamin kuma ya yi kira da a kawo ƙarshen kisan bakaken fata a ƙasar.

    Al Sharpton ya ce ba wai ana taron ba ne kawai don gani da ido, ƙoƙari ake don nuna jajircewa komai tsanani da zafi.

    Cikin jawabin da ta gabatar ta kafar intanet ga dubban mutane da suka taru a birnin Washington, ƴar takarar mataimakiyar shugaban kasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar demokrat, Kamala Harris ta bukaci a ƙara himma a yunkurin ganin an kawo gyaran neman wanzar da adalcin bai daya.

  4. Labaran Korona a Cikin Minti Ɗaya Daga Nahiyar Afrika

    1. Sama da matasa 40 masu rubuta jarrabawar fita sakandare sun kamu da korona a Najeriya.

    Mahukunta a fannin ilimi sun ce ɗaliban za su ci gaba da rubuta jarrabawar a wuraren da aka ware domin killace su.

    2. A Namibia kuma, Shugaban Ƙasa Hage Geingob ya ce za su ƙara yawan gwajin korona, inda suke fatan zama ƙasa wadda ta fi kowacce yawan yin gwajin korona a Afirka.

    Shugaban ya ce za a ci gaba da taƙaita zurga-zurga a lardin Khomas, amma za a sassauta a Erongo, musamman ma a Walvis.

    3. Ƙasar Gambia ta ƙara tsawaita dokar ta ɓaci da kwana 21. Wannan ya zo ne bayan ƙarin samuwar korona wanda hakan ya sa mahukunta suka hana taro a wuraren ibada da kuma kullen makarantu.

    A tabbatar cewa ana sa takunkumi idan za a shiga taron jama’a.

  5. Najeriya ta mayarwa Ghana martani kan 'cin zarafin 'yan kasarta'

    Najeriya ta zargi Ghana kan abinda ta kira "cin zarafin 'yan kasarta a Ghana da kuma yadda hukumomin Ghana din ke ƙara matsawa 'yan Najeriya lamba".

    Wata sanarwa daga ministan yada labaran kasar Lai Mohammed ta ce an mayar da 'yan Najeriya a Ghana "wasu abin yi wa ba'a".

    Ya lissafa abubuwan da ake yi wa 'yan Najeriya da suka hada da

    • Rushe wani gini na ofishin jakadanacin Najeriya a babban birnin kasar Accra. Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya nemi afuwa bisa lamarin
    • Yawan iza keyar 'yan Najeriya gida ba ƙaƙƙautawa
    • Rufe shagunan 'yan Najeriya.

    Lai Mohammed ya ce gwamnatin Najeriya na duba hanyoyin da za ta dauka na yi wa tufkar hanci, sai dai bai bayyana matakan ba.

    Tun da farko a wannan makon, ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey ta kira jakadan Najeriya a Ghana domin yi masa ƙorafi kan wasu kalamai da aka ce Najeriya ce ta yi.

    An rawaito cewa ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama na cewa farmakin da ake kai wa masu kasuwanci ba bisa ƙa'ida ba a Ghana ana yi ne saboda ƙoƙarin cimma manufar siyasa.

    A cikin jerin sakonnin da ta wallafa a shafin tuwita, ta bayyana kalaman a matsayin "abin takaici" sannan ta bayyana cewa gwamnatin Ghana ba ta da nufin cuzgunaw 'yan wata ƙasa.

    Dokokin Ghana dai sun haramtawa 'yan ƙasashen waje bude shagunan sayar da kaya daidaiku, musamman ma a yankunan da ake kasuwanci, kuma 'yan kasuwa na cikin gida na matsawa gwamnati lamba kan ta tabbatar an yi aiki da dokokin, kamar yadda wakilin BBC a Accra Thomas Naadi ya bayyana.

    Huldar diplomasiyyya tsakanin ƙasashen biyu ta taɓarɓare a 'yan watannin nan, bayan sabani kan rufe shaguna da kuma rushe gini mallakin ofishin jakadancin Najeriya.

  6. Dabbar polar bear ta kashe wani mutum a Norway

    Dabbar polar bear ta kashe wani mutum a tsibirin Spitsbergen da ke ƙasar Norway, a cewar jami'ai.

    Lamarin ya faru ne a wani waje da ke kusa da garin Longyearbyen.

    An tsinci gawar dabbar pola bear ɗin wadda aka harbe a kusa da fiin jirgin saman garin.

    Ƙwararru sun ce a yanzu polar bear na ƙara shiga cikin al'umma a ƙoƙarinsu na neman abinci, saboda yadda ƙanƙarar da ke tekun Arctic ke ƙara narkewa inda suke rayuwa.

    Dabbar ta kai wa mutumin mai shekara 38 ɗan ƙasar Holland mai suna Johan Jacobus Kootte, hari ne a cikin tantinsa kafin asubahin ranar Juma'a, kuma bai daɗe ba ya ce ga garinku sakamakon raunukan da ya ji.

    Jami'an yankin sun ce akwai mutum bakwai a wajen lokacin da lamarin ya faru su ma kuma jami'an lafiya na duba su.

  7. Wani mutum ya amsa laifin kisan mutum 39 'yan ciranin Vietnam a Birtaniya

    Wani mutum ya amsa laifin kisan mutum 39 'yan Vietnam 'yan ci rani da aka gano su a wata babbar mota a yankin Essex a Birtaniya.

    Mutanen da aka kashe da suka hada da maza da mata da yara an gano su ne a wata mota mai na'urar sanyaya kaya a yankin Grays ranar 23 ga watan Oktoba.

    Haulier Ronan Hughes, mai shekaru 40 mazaunin yankin Tyholland, a yankin Monaghan da ke Ireland, ya amsa laifin kisan mutanen da kuma haɗa baki wajen taimaka wa 'yan ci rani ba bisa ƙa'ida ba a babbar kotun miyagun laifuka ta Old Bailey.

    Mutum na biyu Eamonn Harrison mai shekara 23 da ke zaune a unguwar Mayobridge a yankin Down ya musanta laifukan kisan kai.

    Mista Harrison ya kuma ƙi amsa lafiin cewa ya haɗa baki wajen shigar da baƙin haure ba bisa ƙa'ida ba, amma yana fuskantar shari'a a watan Oktoba.

    An gano gawawwakin 'yan Vietname ɗin ne a wani yankin masana'antu jim kaɗan bayan babbar motar ta shiga Birtaniya daga Belgium.

  8. China na fuskantar sauyin yanayi mai tsanani

    Sabbin bayanai daga China na cewa ƙasar na fuskantar sauyin yanayi mai tsanani.

    Taron shekara-shekara na gwamnatin Beijing kan sauyin yanayi ya nuna cewa yanayin zafi da yawan ruwan teku na ƙaruwa da sauri-sauri fiye da yadda ya saba yayin da ake samun yanayi mai tsanani kamar ruwan sama mai ƙarfi da fari akai-akai.

    Ya kuma bayyana cewa yawan ruwan teku na ƙaruwa cikin sauri fiye da yadda ya saba sannan manyan curin ƙanƙara na narkewa fiye da a baya-baya.

  9. Bama-bamai sun kashe mutum 14 a Afghanistan

    Hukumomi a kudancin Afghanistan sun ce mutum 14 sun hallaka yayin da uku suka jikkata a tashin wasu bama-bamai biyu da aka sanya a kan hanya.

    Sun ce al'amarin farko ya faru ne a garin Spin Boldaka da ke lardin Kandahar lokacin da wata mota da ke ɗauke fasinjoji ta taka nakiyar da aka sanya a kan hanyar inda mutum 13 suka hallaka ciki har da yara uku.

    Mutanen da ke cikin motar na tafiya ne domin halartar wani bikin ɗaurin aure.

    Wakilin BBC ya ce bayan wasu sa'o'i da faruwar al'amarin farko, an sake samun wata fashewar da ta shafi wata mota inda mutum ɗaya ya hallaka.

    Kawo yanzu babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin.

  10. Maƙwabtan Mali na ci gaba da matsa mata kan bai wa farar hula mulki

    Maƙwabtan Mali a Afrika Ta Yamma sun sake amincewa da cewa ƙasar ta yi gaggawar miƙa mulki ga farar hula.

    Hakan na zuwa ne bayan tataɓurzar da ake ta ti kan batun mulkin bayan kifar da gwamnati da sojoji suka yi.

    A wani taro da suka yi ta bidiyo yau Juma'a, ƙungiyar yankin mai ƙasashe 15 ta yi kira ga dakarun da su koma sansanoninsu sannan a yi zaɓe cikin wata 12.

    Amma sojojin juyin mulkin suna so su tsaya a madadin gwamnatin riƙon ƙwarya tsawon shekara biyu.

    Har yanzu ƙasar na cikin rikici. Sojojin juyin mulkin sun saki tsohon shugaban ƙasar a jiya gabanin taron ECOWAS.

    Amma ECOWAS ta ce sakin nasa kawai bai isa ba. Kuma ƙungiyar ta sanay wa Mali takunkumai kan juyin mulkin da suka haɗa da rufe iyakokinta da dakatar da ita daga ƙungiyar da kuma dakatar da kasuwanci da ita.

    Amma a taron na yau sun ce a hankali za su ɗage takunkuman yayin da ƙasar ke komawa turbar dimokraɗiyya.

  11. An kashe mutum biyar a gabashin Sudan kan naɗin sabon gwamna

    Mutum biyar sun hallaka a gabashin Sudan a zanga-zangar nuna rashin amincewa da mutumin da aka nada a matsayin sabon gwamnan jihar Kassala.

    Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ce an cinnawa wasu gine-gine wuta tare da lalata dukiyoyin jama'a bayan da aka harbi motar shugaban wata ƙabila da ke adawa da naɗin gwamnan jihar.

    An tura da jami'an tsaro zuwa birnin bayan da ƴan ƙabilar Hadendowa suka shigo cikin babban birnin yankin riƙe da sanduna da takubba.

    Sun fusata ne a kan cewa gwamnan da aka naɗa ya fito ne daga ƙabilar Beni Amer wadda ba sa ga maciji da su.

  12. Waɗanda cutar korona za ta kashe a Amurka za su haura 200,000 a tsakiyar Satumba

    Mace-macen da ke da alaƙa da cutar korona a Amurka ka iya haura 200,000 nan da tsakiyar watan Satumba, a cewar Cibiyar Hana Yaɗuwar Cututtuka Ta Amurka CDC ta yi hasashe.

    Ana sa ran cewa za a samu mace-mace 4,000 zuwa 8,300 a cikin makon ƙarshe na Satumba, in ji CDC.

    CDC ta ce za a iya samun mace-mace har 207,000 a jumulla zuwa wannan ranar.

    A ƙalla mutum 180,000 ne suka mutu sakamakon cutar korona zuwa yanzu a Amurka, yawan da ya fi na ko ina a duniya, kamar yadda alƙaluman Jami'ar Johns Hopkins suka nuna.

  13. Dubban mutane za su yi maci kan haƙƙoƙin fararen hula a Washington

    Ana sa ran dubban za su taro a birnin Washinton DC na Amurka don tuna wa da Macin da aka yi a shekarar 1963 kan haƙƙoƙin fararen hula da kuma nuna adawa da ''cin zarafin'' da ƴan sanda ke yi.

    Iyalan Amurkawa baƙaƙen fata da ƴan sanda suka kashe za su yi magana a wajen da Martin Luther King Jr ya gabatar da jawabinsa mai taken ''I Have a Dream,'' ''Ina da buri.''

    Taken macin na ranar Juma'a: Sa gwiwarku a kan wuyanmu, wani abu da ake misaltawa da kisan George Floyd.

    Hakan ya biyo bayan sabbin zanga-zanga ne kan kisan da ƴan sanda suka yi wa wani baƙar fata Jacob Blake.

    Ana sa ran dangin Mr Blake da na Mr Floyd da Breonna Taylor da Eric Garner za su gabatar da jawabai a wajen macin.

  14. Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin Darussalam a jihar Nasarawa

    Masana harkokin tsaro sun ce bayyanar wata ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya mai aƙidu irin na Boko Haram babbar barazana ce ga Najeriya da ke fama da hare-haren ta'addanci a sassan ƙasar.

    A ranar Laraba ne rundunar sojin kasar ta ce dakarunta sun tarwatsa wani sansanin wata ƙungiya da ake kira Darussalam (Darul Islam) a yankin Uttu da ke ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.

    Sojojin na Najeriya sun ce suna tsare da mambobin ƙungiyar fiye da 400 da suka suka ce sun miƙa wuya gare su - yawancin su mata da yara ƙanana.

    Ku latsa nan don karanta abubuwa biyar game da ƙungiyar Darus Salam.

    Sannan ku latsa hoton da ke ƙasa don sauraron rahoto kan lamarin:

  15. Shugaba Buhari ya jajanta wa masu hatsarin helikwafta na Legas

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa saƙon ta'aziyarsa ga iyakan waɗanda suka mutu a hatsarin helikwafta da ya faru yau a Legas.

    A wata sanarwa da Femi Adesina mai bai wa Buhari shawara kan harkar yaɗa labarai ya fitar ya ce shugaban ya kuma ce a yayin da ake jiran sakamakon binciken abin da ya jawo hatsarin, shugaban na addu'ar Allah Ya bai wa iyalan mamatan haƙurin rashinsu, tare da bai wa marasa lafiya sauƙi.

    A yau Juma'a ne helikwaftan ya yi hatsari a garin Legas da ke kudancin Najeriya.

    Rahotanni sun ce aƙalla mutum biyu suka mutu a hatsarin inda jirgin ya faɗi a ginin wata coci ta sojoji a unguwar Opebi cikin Ikeja.

  16. Firaministan Nijar ya kai ziyara Zamfara

    Firaministan Jamhuriyar Nijar Brigi Rafini tare da Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle lokacin da firai ministan ya kai ziyara jihar Zamfara ranar Alhamis.

  17. An kashe masu zanga-zanga biyar a Sudan

    Rahotanni daga gabashin Sudan na cewa akalla mutum biyar aka kashe yayin wata zanga-zangar nuna rashin goyon baya kan naɗin da aka yi na sabon gwamnan jihar Kassala.

    Kafafen watsa labarai a yankin sun ruwaito cewa an cinna wa gine-gine wuta tare da lalata dukiyoyi bayan an harbi motar wani jagoran masu adawa da sabon gwamnan.

    An tura jami'an tsaro bayan mambobin ƙabilar Hadendowa sun taru a babban birnin yankin ɗauke da sanduna da wuƙaƙe.

    Ana zanga-zangar ne sakamakon sabon gwamnan ya fito ne daga ƙabilar Beni Amer.

  18. An gudanar da Sallar Juma'a a Masar a karon farka bayan kusan watanni shida

    Manyan Masallatan Juma'a a Masar sun gudanar da Sallar Juma'a a ƙasar, sama da watanni biyar bayan an dakatar da Sallar Juma'a a ƙasar.

    Masallatan sun bi ƙa'idojin da aka gindaya na kare kai daga kamuwa da korona. Ƙa'idojin sun haɗa da saka takunkumi da bayar da tazara a tsakanin masallata.

    Masallata sun zo da dardumar sallan su, hakazalika an taƙaita huɗubar da ake yi ta Sallar Juma'a inda huɗubar ba ta wuce mintuna goma a kusan duka masallatan.

    A halin yanzu mutum 98,000 suka kamu da cutar korona a Masar inda sama da mutum 5,300 suka mutu.

  19. Helikwafta ya yi hatsari a tsakiyar Legas

    Wani jirgin helikwafta ya yi hatsari a garin Legas da ke kudancin Najeriya.

    Rahotanni sun ce aƙalla mutum biyu suka mutu a hatsarin da ya faru a Ikeja a ranar Juma'a.

    Bayanai sun ce jirgin ya faɗi a ginin wata coci ta sojoji a unguwar Opebi cikin Ikeja.

    Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sadarwa na Intanet ya nuna yadda jirgin ya faɗi a rukunin gidaje.

    Bayan mutane biyu da suka mutu a hatsarin jirgin, mutum na uku da ke cikin jirgin na asibiti inda aka kai shi sashen kulawa da marasa lafiya na musamman.

  20. Sama da mutum dubu 60 ke kamuwa da korona a duk rana a Indiya

    Yawan masu kamuwa da cutar korona a Indiya na ƙaruwa a kullum inda sama da mutum 60,000 ke kamuwa da cutar a duk rana.

    A sa'o'i 24 da suka gabata, an samu mutum 76,827 da aka tabbatar sun kamu da wannan cuta, wanda wannan shi ne adadi ma fi yawa da aka samu a wannan watan.

    Jumullar mutum miliyan 3.4 da ke ɗauke da cutar a ƙasar ya sa ƙasar ta Indiya ta zama ta uku a yawan waɗanda suka kamu da cutar ta korona.

    Masana sun bayyana cewa ba abin mamaki bane idan an samu irin wannan adadi mai yawa a Indiya ganin cewa ƙasar na da ɗumbin jama'a da suka kai biliyan 1.3.

    A halin yanzu dai mutum 61,700 suka kamu da cutar a ƙasar ta Indiya.