Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An ceci mutumin da aka ɗaure shekaru 30 a Kano

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • Sojojin Mali sun tattauna da ƴan adawa
    • Boko Haram ta 'sace mutane da dama' a Borno
    • Ranar Juma'ar ce sabuwar shekarar musulunci a Najeriya
    • An buɗe ɗakin gwajin korona a Gombe
    • An ceci mutumin da aka ɗaure shekaru 30 a Kano
    • An harbe dogarai shida na mataimakin shugaban Sudan Ta Kudu
    • Shugabannin ECOWAS na son a mayar da Shugaba Keita kan mulki

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. An saki mutanen da aka yi garkuwa da su a Somaliya kusan shekaru 5

    Masu fashin teku a Somaliya sun saki wasu mutum uku 'yan ƙasar Iran da suka yi garkuwa da su shekaru biyar da suka gabata.

    Wani mai shiga tsakani wanda ya sasanta lamarin John Steed ya shaida wa BBC cewa mutanen da aka saki su ne na ƙarshe a wani jirgin ruwa da aka kama a 2015 mai suna FV Siraj.

    Ya bayyana cewa sakin mutanen ya kawo ƙarshen kukan da ake yi na mutanen da aka kama a Somaliya da aka manta da su na tsawon shekaru.

  3. Rikicin ƙabilanci: An kashe mutum biyar a Habasha

    Jami'ai a ƙasar Habasha sun bayyana cewa akalla mutum biyar aka kashe yayin wata arangama tsakanin jami'an tsaron ƙasar da masu zanga-zangar neman sakin shugabannin ƙabilar Oromo da aka kama.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙi sun bayyana cewa adadin waɗanda ke mutuwa na ƙaruwa sosai.

    Rahotanni a ƙasar sun ce an kashe mutane a wurare da dama.

    Zanga-zangar ta ɓarke ne a ranar Talata bayan wani gangami da aka yi a shafukan sada zumunta inda ake kira da a saki shugabannin 'yan adawa a ƙasar, Jawar Mohammed da kuma Bekele Gerba.

    An kama su ne tun a watan Yuni bayan da aka harbe shahararren mawaƙin nan ɗan ƙabilar Oromo Hachalu Hundessa.

  4. Shugabannin ECOWAS na son a mayar da Shugaba Keita kan mulki

    Shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika ƙarƙashin jagorancin kungiyar ECOWAS, sun buƙaci a mayar da Tsohon Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keita kan mulki.

    A wata tattaunawa da suka yi ta bidiyo ƙarƙashin jagorancin Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou, sun bayyana cewa za su tura wakilai na musamman ƙasar domin tabbatar da an dawo da mulkin dimokraɗiyya ƙasar.

    Akwai sojoji da dama da aka jibge a wajen ma'aikatun gwamnati a Bamako babban birnin ƙasar, sai dai tunbi aka buɗe shaguna da kuma ci gaba da kasuwanci.

    Sojojin da suka jagoranci juyin mulkin da aka yi a ranar Talata sun sha alwashin gudanar da zaɓe a abin da suka kira "lokacin da ya dace".

  5. Lauyoyin Najeriya sun yi wa El-Rufai tutsu

    Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, biyo bayan zanga-zangar da wasu lauyoyi suka yi kan gayyatar.

    A wani saƙo da Ƙungiyar Lauyoyin ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta yanke shawarar janye goron gayyatar da tura wa gwamnan kuma tuni ta shaida wa gwamnan matakin da ta ɗauka.

    Tun da farko dai wani lauya ne mai suna Usani Odum ya ƙaddamar da takardar koke ta intanet inda ya nemi ƙungiyar ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan.

    A ranar Alhamis dai sama da mutum dubu uku ne suka aika da koken su a shafin Change.org.

    Masu koken akasari na zargin gwamnan da gazawa wurin shawo kan rikicin Kudancin Kaduna da kuma take haƙƙn bil adama.

  6. An harbe dogarai shida na mataimakin shugaban Sudan Ta Kudu

    An harbe dogarai shida na Mataimakin Shugaban Sudan Ta Kudu, James Wani Igga, bayan an kai hari ga ayarin motocinsa.

    Mai magana da yawunsa, Kalisto Lado, ya shaida wa BBC cewa wasu 'yan tawaye ne suka kai harin inda kuma suka raunata mutum biyu bayan shidan da suka kashe.

    Mista Wani ba ya cikin jerin ayarin motocin da aka kai wa harin a mahaifarsa da ke ƙauyen Lobnok, kudu da babban birnin ƙasar Juba.

    Harin wanda da aka kai a ranar Laraba ya faru ne yayin da 'yan tawaye daga ƙungiyar National Salvation Front suka tare motar da dogaran suke ciki suka lalata ta kuma suka ƙona motar.

    Har yanzu dai ƙungiyar ba ta ce komai ba kan wannan harin.

    Mista Igga na cikin mataimakan shugaban ƙasa biyar da ake da su a Sudan Ta Kudu, kuma shi ke kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasar.

  7. Iran ta ƙwace jirgin ruwan Daular Larabawa

    Iran ta bayyana cewa ta ƙwace wani jirgin ruwa na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan an harbe wasu masu kamun kifi a yankin na Gulf.

    Ma'aikatar harkokin wajen Iran da ke Tehran ta ce an ƙwace jirgin ne a ranar Litinin, yayin da ya ke tafiya ba kisa ƙa'ida ba cikin tekun na Iran.

    Har yanzu Daular Larabawan ba ta ce komai ba kan wannan lamari, amma hakan ya faru ne a daidai lokacin da ake zaman doya da manja tsakanin ƙasashen masu makwaftaka tun bayan da Daular Laraban a makon da ya gabata ta bayyana cewa za ta ci gaba da ƙawance da Isra'ila.

    Iran ta ce matakin da Daular Larabawan ta ɗauka na ci gaba da ƙawancen babban kuskure ne.

  8. An ceci mutumin da aka ɗaure shekaru 30 a Kano

      • Marubuci, Mansur Abubakar
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Pidgin, Kano

    'Yan sanda a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ceto wani mutum mai shekaru 55 da 'yan uwansa suka ɗaure na tsawon shekaru 30 sakamakon yana da taɓin hankali.

    Wani ɗan kare haƙƙin bil adama Sani Shuaibu ya shaida wa BBC cewa mutumin ya shafe shekaru yana cikin wahala, inda aka ɗaure shi jikin wani ƙaton ƙarfe a cikin wani ɗaki da bai da ƙofa ko kuma taga.

    Hakan ya sa ya faɗa wa 'yan sanda halin da mutumin yake ciki bayan ya samu labari kan mutumin, kuma suka ceto shi tare da 'yan sanda a garin Rogo da ke Kano.

    "Mutumin yana da taɓin hankali kuma ya fara faɗa, a maimakon a nemo masa magani tun a 1990, sai mahaifinsa ya yanke shawarar ɗaure shi," in ji Shu'aibu.

    Bayan mahaifin mutumin ya rasu a shekarun baya, sai 'yan uwansa suka ci gaba da kulle mutumin, amma a halin yanzu, an sake shi. Wasu daga cikin makwaftansa da suka san halin da yake ciki sun taimaka wurin ceton, in ji shi.

    Mutumin mai shekaru 55 a halin yanzu yana babban asibitin garin Rogo inda a nan ne yake karɓar magani, inda kuma tuni aka tafi da 'yan uwansa wurin 'yan sanda.

    Mai magana da yawun 'yan sandan Kano Abdullahi Haruna ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamarin kuma ya ce ana gudanar da bincike.

    Wannan ne aikin ceto na uku cikin ƙasa da makonni biyu da aka yi na mutane masu buƙata ta musamman da 'yan uwansu suka yi musu ɗaurin talala.

  9. An buɗe ɗakin gwajin korona a Gombe

    An fara amfani da ɗakin gwajin cutar korona a asibitin ƙwararru da ke Gombe, inda ake gwajin kusan mutum 50 a rana.

    Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Ahmed Mohammed Gana ya bayyana cewa nan da lokaci kaɗan za a ƙara adadin mutanen da ake wa gwaji zuwa 120 a duk rana.

    Ya bayyana cewa a halin yanzu, an samu kusan mutum 16 da aka tabbatar sun kamu da wannan cuta.

    A ƙididdigar da hukumar NCDC ta fitar a ranar Laraba a Najeriya, mutum 684 suka kamu da cutar a jihar tun bayan ɓullar cutar a Najeriya.

  10. An ɗaure ɗan uwan maharin Manchester

    Kotu a Birtaniya ta yanke hukuncin daurin shekara 55 ga ɗan uwan mutumin da ya kai harin ƙunar bakin wake a dandalin Manchester a shekarar 2017.

    Kotun ta sami HashIm Abe-di da laifin kisa da yunkurin aikata kisa tare kuma da bada hadin kai wajan haddasa fashewar abubuwa.

    Mutum 22 ne suka rasa rayukansu a harin bam da aka kai lokacin da fitacciyar mawakiyar pop ta Amurka Ariana Grande ta Ke waka.

    Sai dai Hashim Abedi yana ƙasar Libya lokacin da dan uwan nasa Salman ya kai harin.

  11. Ganduje ya ja kunnen malamin da ya buɗe makarantar Islamiyya

    Gwamnatin jahar Kano ta gayyaci wani shugaban wata makarantar makarantar Islamiyya ta Salman Faris islamiyya da ke rijiyar zaki sakamakon bude makarantar ba tare da izini ba.

    Da yake yi wa BBC karin bayani, shugaban hukumar da ke kula da makarantun tsangayyu da islamiya a Kano, Gwani Yahuza Gwani Danzarga ya ce sun gayyaci malamain ne biyo bayan wata takardar koke da suka samu daga iyayen yara da ke makaranatar kan bude makarantar da aka yi, tare da neman ɗaliban su biya wasu kuɗaɗe.

    Gwamnati ta rufe makarantu Islamiyya saboda tsoron yaduwar cutar korona a jihar. Kuma gwamnatin ta ce har yanzu ba ta bayar da izinin buɗe makarantun Islamiyya ba.

    Ga rahoton da Wakilin BBC a Kano Khalifa Shehu Dokaji ya aiko.

  12. Ku saurari Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 20/08/2020

  13. Buhari ya buƙaci sojojin Mali su gaggauta miƙa mulki ga farar hula

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yanayin da ake ciki a Mali babban koma bayan diflomasiya ne ga yankin yammacin Afirka kuma babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.

    Shugaban ya yi kira ga hukumomin sojin Mali da ya kira 'haramtattu' su gaggauta dawo da mulkin farar hula a ƙasar.

  14. ISWAP ta ce ita ta kashe sojojin Najeriya a Kukawa

    Ƙungiyar IS ta ce ta kashe sojojin Najeriya guda bakwai a garin Kukawa da ke cikin jihar Borno, yayin da rahotanni suka ce kuma mayakan sun kuma yi garkuwa da mutane da dama a garin.

    A sanarwar da ta fitar IS ta ce mayakanta sun kai hari sansanin Soji inda suka yi artabu da su, tare da ikirarin kashe mutum bakwai da raunata wasu.

    Sannan ƙungiyar ta ce ta kwace motocin yaki da makamai na sojojin Najeriya

    Sai dai ba ta bayyana cewa ta yi awon gaba da mutanen garin na Kukawa ba a harin da ta kai ranar Talata.

  15. Ranar Juma'ar ce sabuwar shekarar musulunci a Najeriya

    Kwamitin ganin wata ƙarkashin majalisar ƙoli ta harakokin musulunci a Najeriya ya ce ba a samu rahoton ganin sabon watan Muharram ba na shekarar musulunci ta 1442 bayan hijira.

    Hakan na nufin ranar Alhamis na cikin watan Dhul Hijja na shekerar 1441 yayin da kuma Juma’a za ta kasance 1 ga watan Muharram.

    Wannan ne ya sa Sarkin musulmi ya sanar da ranar Juma’a a matsayin 1 ga watan Muharram kamar yadda Farfesa Sambo Wali Junaidu Wazirin sokotoya bayyana a cikin wata sanarwa.

  16. Shugabannin Ecowas na tattauna batun Mali

    Shugabannin kasashen Afrika ta yamma Ecowas, na tattaunawa a kan juyin Mulki da aka yi a kasar Mali ta Intranet.

    Tuni Ecowas ta riga da ta sanar da ɗaukar mataki kan Mali inda ta rufe kan iyakokinta da ƙasar.

    ECOWAS na duba yiwuwar sanya takunkumi ga wadanda ke da hannu a juyin mulkin na ranar lititin.

    Assimi Goita, jagoranr mulkin na soja. Faransa ta ce za ta ci gaba ayyukan sojoji a kan ma su jihadi a Mali bayan hamɓarar da shugaba Ibrahim Boubakar Keita.

  17. Boko Haram ta 'sace mutane da dama' a Borno

    Mayaƙan Boko Haram sun shiga garin Kukawa a jihar Borno inda rahotanni suka ce sun kashe mutane ciki har da sojoji tare da kuma yin garkuwa da wasu.

    A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da harin amma ta yi ikirarin murƙushe mayakan. Ko da yake sanarwar ta ce akwai sojoji uku da suka samu mummunan rauni.

    Majiyoyi daga garin Kukawa sun ce mayakan ISWAP sun abka garin ne ranar Talata inda suka yi awon gaba da ɗaruruwan mutane waɗanda suka dawo bayan sun gujewa gidajensu tsawon shekara biyu.

    Sanarwar da kakakin rundunar sojin Najeriya Janar John Enenche ya fitar ta ce sojoji sun kashe ƴan Boko Haram takwas yayin da wasu kuma da dama suka tsere da rauni a jikinsu.

    Rundunr sojin ta Najeriya ta ce yanzu komi ya lafa a garin na Kukawa bayan sun kori ƴan Boko Haram

  18. Ƴan sanda sun kama mutumin da ya kashe danginsa

    Ƴan sanda a Pakistan sun ce suna tsare da wani mutum da ya kashe danginsa 11 a lardin Sindh

    Wadanda ya kashe sun ƙunshi matarsa da ƴaƴansa da matar ƴarsa da kuma jikokinsa.

    An kama mutumin tare da wasu ƴaƴansa da suka taimaka masa.

    Ƴan sanda sun ce sun amsa aikata kisan, inda suka ce rikici ne tsakanin matan ƴaƴansa ya janyo kashe-kashen. Ƴan sanda yanzu haka na gudanar da bincike.

  19. Sojojin Mali sun tattauna da ƴan adawa

    Shugaban Sojin Mali da suka jagoranci juyin mulki sun tattauna da shugabannin adawa waɗanda suka yi na’am da hamɓarar da Ibrahim Boubakar Keita.

    Sun zarge shi da gazawa wajen shawo kan rikicin ƴan ta’adda da kuma matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki.

    Kanal Assimi Goita, shi ne shugaban mulkin sojan kuma ya buƙaci ma’aikata su dawo aiki.

    Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi allawadai da juyin mulkin.

    Shugabannin Ecowas sun sanar da rufe iyakokinsa a tattaunawar da suka yi kan rikicin Mali

  20. Sudan ta kori kakakin gwamnati kan Isra’ila

    Sudan ta kori mai Magana da yawun ma’aikatar harakokin waje bayan fitar da sanarwa da ba a tantance ba game da matsayin ƙasarsa kan Isra’ila.

    Haidar Badawi ya shaida wa kafofin yada labarai cewa Khartoum tana tattaunawa da Isra’ila domin farfaɗo da hulɗa tsakaninsu.

    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya yi na’am da kalaman amma sa’o’i kaɗan sai ministan harakokin wajen Sudan Omar Qamareddin ya bayyana cewa gwamnatin Sudan ma ba ta san da maganar ba.

    Daga baya mista Badawi ya ce ya bayyana haka ne a ƙashin kansa.