Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Zan koma limanci tun da an kawar da Keita – Mahmoud Dicko

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. ASUU za ta ci gaba da yajin aiki har sai an biya mata buƙatunta

    Ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta ƙaddamar da wani sabon tsari a madadin wanda gwamnatin Najeriya ta ce tilas sai jami'o'in sun fara amfani da shi.

    Kazalika ASUU ta ce yajin aikin da take yi zai ci gaba har sai an biya musu buƙatunsu.

    ASUU ta fito da tsarin University Transparency and Accountability Solution (UTAS) a madadin Integrated Personnel Payroll Information System (IPPIS) wanda gwamnatin ta amince da shi.

    Jaridar Leadership a Najeriya ta rawaito shugaban ƙungiyar Biodun Ogunyemi yana cewa har yanzu UTAS yana nan daram ba wai kawai a matsayin madadin IPPiS ba, "tsarin da bai mutunta ɗabi'a da salon aikin koyarwar jami'o'in Najeriya ba".

    A cewarsa: "Mun sha yin alƙawarin cewa za mu samar da wata manhaja da za ta dace da tsarin jami'o'in Najeriya da kuma biyan albashinsu haɗi da tattara bayanan malamai."

  2. Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Mali

    Jagororin juyin mulkin da ya sauke Shugaban Mali Ibrahim Keïta ranar Talata sun haɗa da mataimakin shugaban barikin soja da kuma wani janar da ya samu horo a ƙasar Faransa.

    Ga guda uku daga cikin jagororin:

    1 - Col Malick Diaw

    Shi ne mataimakin shugaban barikin soja na Kati, inda aka fara shirya juyin mulkin.

    Babu wasu cikakkun bayanai a kansa baya ga cewa bai daɗe da dawowa daga ƙasar Rasha ba daga samun horo.

    2- Col Sadio Camara

    Kanar Camara, shi ne tsohon shugaban sansanin Kati.

    Shafin jaridar Tribune ta Mali ya rawaito cewa an haife shi a shekarar 1979 a Kati da ke kudancin yankin Koulikoro.

    3. Gen Cheick Fanta Mady Dembele

    Gen Cheick Fanta Mady Dembele, shi ne shugaban cibiyar Alioune Blondin Beye mai aikin tabbatar da zaman lafiya.

    An ɗaukaka muƙaminsa zuwa birigediya janar a watan Mayun 2018 kuma ya karɓi shugabancin cibiyar ne a watan Disamban 2018.

  3. Sojoji sun yi alƙawarin gudanar da zaɓe a Mali

    Sojojin da suka hamɓarar da Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta sun bayyana aniyarsu ta kafa gwamnatin riƙon ƙwarya kafin gudanar da sabon zaɓe a ƙasar.

    Wannan ya biyo bayan bayyanar shugaban a kafar talabijin, inda ya ce ya sauka daga muƙaminsa.

    Sojojin sun yi awon gaba da shi tare da firaministansa daga babban birnin ƙasar zuwa wani sansanin soja.

    Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka ta AU da Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

  4. An saka dokar hana fita a Mali, an rufe iyakokin ƙasar

    Shugabannin rundunar sojojin Mali sun bayar da umarnin rufe iyakokin ƙasar tare da sanya dokar hana fita da dare, a cewar wata sanarwa da mataimakin shugaban ma'aikatan sojojin sama na ƙasar.

    "Daga yau, 19 ga watan Agustan 2020, an rufe dukkanin iyakoki na sama da na ƙasa har sai baba ta gani. An saka dokar hana fita daga ƙarfe 9:00 na dare zuwa 5:00 na asuba har sai baba ta gani," in ji Kanar-Manjo Ismaël Wagué a wani jawabin talabijin.

    Kazalika ya miƙa goron gayyata ga 'yan adawa - waɗanda suka riƙa yin zanga-zangar neman sauyi - domin tattaunawa kan giudanar sabon zaɓe.

    "Ana gayyatar ƙungiyoyin farar hula da na siyasa da su haɗa kai domin samar da sauyi na siyasa ta hanyar zaɓe sahihi da zai kai ga ƙirƙirar sabuwar ƙasar Mali," a cewarsa.

  5. Abin da ya faru a Mali daren Talata

    Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keïta ya yi murabus daga mulki, bayan sojoji sun tsare shi ranar Talata, kamar yadda gidan talbijin ɗin ƙasar ya ruwaito.

    A wani jawabi ta aka yaɗa ta kafar talbijin, Ibrahim Keïta ya ce ya kuma rusa gwamnatin ƙasar da majalisar dokoki.

    Ya ƙara da cewa: "Ba na son a zubar da jini don ganin na ci gaba da mulki".

    Al'amarin na zuwa ne bayan sojoji sun ɗauke su, shi da Fira Minista Boubou Cissé zuwa wani sansanin soji da ke kusa da babban birnin ƙasar Bamako, abin da ya janyo Allah-wadai daga ƙasashen yankin da kuma Faransa.

  6. Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye

    Maraba da shigowa wannan shafi da zai riƙa kawo labarai kai-tsaye a tsawon yau Laraba game da abubuwajn da suke faruwa a duniya, musamman rikicin siyasar da ƙasar Mali ke ciki - kun san cewa sojojin ƙasar sun yi wa Ibrahim Boubacar Keïta juyin mulki.

    Umar Mikail ne zai kasance tare da ku a yanzu.