An kama sanatocin Kenya game da raba kudi ga yankunan ƙasar
Sanatocin Kenya sun ce an kama abokan aikinsu uku a daren Lahadi game da zaɓen raba kudade ga ƙananan hukumomi.
Kaɗa ƙuri'a a kan raba kudade da za a yi ranar Litinin, an daga shi sau takwas yanzu game da rashin jituwa a kan tsarin raba biliyan 316.5 na kuɗin Kenya (dalar Amurka biliyan $2.9) a tsakanin ƙananan hukumomi 47.
Tsohon shugaban masu riinjaye Kipchumba Murkomen ya faɗa wa Majalisar Dattijai cewa an kama Cleophas Malala da Christopher Langat a gidajensu a babban birnin Nairobi, shi kuma Ltumbesi Lelegwe an kama shi a kan hanyarsa yta zuwa majalisar.
Har yanzu 'yan sanda ba su ce komai ba kan batun ba.
Sanatocin sun kira da a sake gabatar da ƙara don yin mahawara game da kama abokan aikinsu.