Najeriya ta sanar da ranar dawo da jigilar jiragen ƙasashen waje

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Halima Umar Saleh and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Muna godiya da kasance da mu a wannan shafin inda muka shafe yini muna kawo maku labarai da rahotannin abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta da ma sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe domin ci gaba da samun rahotanni daga Najeriya da sassan duniya.

  2. An kori shugaban ƴan sanda a Iraƙi bayan kashe wani mai fafutika

    Firaministan Iraƙi Mustafa al-Kadhimi ya kori babban jami’in ƴan sanda a kudancin lardin Basra bayan zanga-zanga kan kisan wani mai fafutika.

    A makon da ya gabata ne wasu ƴan bindiga da ba a tantance ba suka harbe harbe Tahseen Usama.

    Kisan shi ne ya haifar da zanga-zanga inda masu zanga-zangar suka buƙaci gwamnati ta gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da yin kiran a kori babban jami’in ƴan sanda.

    Ƴan bindiga sun sha kashe masu fafutikar siyasa a Iraƙi

    Iraq

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Sojojin Nijar sun kuɓutar da yara da Boko Haram ta sace

    Sojoji a Nijar sun ce sun kubutar da wasu mutane 11, kuma huɗu daga cikinsu yara ne ƙanana da Boko Haram ta yi garkuwa da su.

    Sakataren gwamnati a yankin Diffa ya tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa an ceto mutanen ne a kusa da tafkin Chadi kusa da wani sansanin Boko Haram.

    Jami’in ya ce sun ƙunshi mata uku kuma daga cikin yaran akwai jarirai da Boko Haram ta sace.

    An sace mutanen ne a ranar 11 ga Agusta a ƙauyen Gueskerou da ke kusa da tafkin Chadi.

  4. An tsinci ƙunshin bom a wani ginin gwamnatin Kamaru

    Jami’an ma’aikatar kula da ma’aikatan Gwamnati sun ce sun gano wani kunshi a boye a cikin kayan wani kwali da ya kunshi takardun wasu malaman makarantu da aka dauka aiki.

    An gano kunshin ne yana kara a wani ofishin da ke ma’aikatar.

    Tuni aka kira jami’an tsaro na ‘yan sanda da na Jandarma suka fitar da kunshin da ake tunanin bom ne.

    Bayan binciken da aka yi an gano cewa wani abin fashewa ne da aka yi niyyar tadawa a cikin ginin ma’aikatar.

    Ku saurari rahoton wakilin BBC a Kamaru Mohaman Babalala da ya aiko daga Yaounde.

    Bayanan sautiAn tsinci ƙunshin bom a wani ginin gwamnatin Kamaru
  5. Barcelona ta sallami kocinta

    Barcelona ta sanar da sallamar kocinta Quique Setien.

    Barcelona ta ce nan da ƴan kwanaki za ta sanar da sabon kocinta daga cikin matakan da ta ke ɗauka na sake gina ƙungiyar kamar yadda ta sanar a Twitter.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Najeriya ta kira jekadiyar Ghana kan rufe shagunan ƴan ƙasarta

    Gwamnatin Najeriya ta kira jami'ar diflomasiyar Ghana a Najeriya kan batun rufe shagunan ƴan Najeriya a Ghana.

    Ministan harakokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama wanda ya tabbatar da matakin a Twitter ya ce gwamnatin Najeriya ta gana da Ms Iva Denoo domin nuna fushinta kan rufe shagunan ƴan Najeriya a Ghana.

    Gwamnatin ta kuma buƙaci Ghana ta gaggauta ɗaukar mataki kan matakin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Malamai za su yi wa ɗalibai rabon maki kyauta a Ingila

    Hukumar da ke shirya jarabawa a Ingila ta janye matakinta na ba ɗaruruwan ɗalibai maki kyauta saboda annobar korona bayan rashin amincewa da tsarin da ɗaliban suka nuna.

    Yanzu malaman ɗaliban ne za su yi hasashen makin da ya kamata a ba ko wane ɗalibi saboda sanin ƙwazon kowannensu. Tuni sauran yankunan Birtaniya suka sanar da ɗaukar matakin.

    Shugabannin shirya jarawabar sun nemi afuwar ɗaliban.

    Ɗaliban sun nuna fushinsu kan yadda aka yi rabon maki inda aka rage masu kusan kashi 40 na makin da suke tsamani.

    Dalibai a Ingila

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Najeriya ta sanar da ranar dawo da jigilar jirage zuwa ƙasashen waje

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranar dawo da jigilar jiragen sama na ƙasashen waje.

    Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya wallafa a Twitter cewa za a fara jigila zuwa ƙasashen waje daga ranar 29 ga Agusta.

    Sai dai ya ce za a fara ne da Legas da Abuja kamar yadda aka fara da dawo da jigilar jirage a cikin Najeriya.

    Ya ce za a sanar da matakai da ka'idoji nan gaba kaɗan

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Sudan

    ƴan Sanda a Khartoum sun harba hayaki mai sa ƙwalla inda suka tarwatsa masu zanga-zanga

    Rahotanni sun ce ƴan sandan sun yi arangama da masu zanga-zangar da ke yin kira ga gwamnatin riƙon ƙwarya ta hanzarta aiwatar da sauye sauye da kuma tabbatar da adalci ga waɗanda aka ci zarafinsu.

    Dubban masu zanga-zanga ne suka fito saman titi a daidai lokacin da ake cika shekara ɗaya da ƙulla yarjejeniyar raba madafan ikon gwamnati da tsarin karɓa-karɓa tsakanin sojojin Sudan da suka hamɓarar da tsohon shugaba Omar al Bashir da kuma ɓangaren ƴan adawa da ke zanga-zanga.

  10. Yariman Daular Larabawa ya ziyarci Isra'ila

    Yariman Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Israela Rueven Rivlin ya gayyaci mai jiran gadon sarautar Hadaddiyar Daular Larabawa Muhammad bin Zayed wanda kai ziyara kasar ta Isra'ila.

    Gayyatar ta biyo bayan yarjejeniyar daidaita dangantaka tsakanin kasashen biyu da shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta.

    A wasikar gayyatar Mr Rivlin ya ce yana fata yarjejeniyar za ta kawo habakar tattalin arziki da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

    A wani labarin kuma, Firaraministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatinsa na aiki don samar da zirga-zirgar jiragen sama tsakani biranen Abu Dhabi da Tel Aviv ta sararin samaniyar Saudi Arabia.

  11. Ali Nuhu na son a buɗe gidajen kallon fim

    Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood Ali Nuhu ya buƙaci a diba buƙatunsu na buɗe wuraren kallon fina-finai a sinima.

    Jarumin ya ce har yanzu ba su dalilin da ya sa gwamnati ba ta amince a buɗe wuraren kallon ba bayan kuma tuni aka buɗe wurare da dama da ke haɗa taron jama’a.

    Ya ce dukkanin gidajen kallon sun ɗauki matakai na kariya amma ba wani ci gaba a tattaunawa da aka ɗauki lokaci ana yi tsakanin hukumomi da masu sinima.

    Ya kuma ce suna jiran tallafin da gwamnati za ta ba masana’antarsu wadda ya ce ta samarwar miliyoyin ƴan Najeriya ayyukan yi a tsawon shekaru 20.

    Kauce wa Instagram
    Ya kamata a bar bayanan Instagram?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a Instagram

  12. Ɗalibi ya kamu da korona a Gombe

    Hukumomin lafiya a Gombe sun sanar da cewa an samu wani ɗalibi da ya kamu da korona a yayin da ake rubuta jarabawar kammala sakandare.

    Hukumar kula da lafiyar al'umma ta jihar Gombe ta wallafa a twitter cewa gwaji ya tabbatar da dalibin ya kamu da korona inda aka killace kafin rubuta jarabawar lissafi a ranar Litinin.

    Ya rubuta jarabawar daga ɗakin da aka killace shi yayin da kuma aka yi tanadin kayan kariya ga jami'in da ke kula da ɗalibin a yayin rubuta jarabawar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. An ɗebo mata 'yan Najeriya 71 da aka yi safararsu zuwa Lebanon

    'Yan matan Najeriya

    Asalin hoton, NIDCOM

    Hukumomi a Najeriya sun ceto wasu mata guda 71 da aka gani a bidiyon da ya karaɗe shafukan zumunta suna roƙon a ceto su bayan an yi safararsu zuwa ƙasar Lebanon.

    Da safiyar yau Litinin ne suka isa Abuja, babban birnin ƙasar.

    Wani bidiyo da aka wallafa a Twitter ya nuna yadda 'yan matan suka isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito Mista Bitrus Samuel, shugaban hukumar agajin gaggawa ta NEMA reshen birnin Abuja, yana bayyana haka.

    Kazalika, bayanai sun nuna cewa za a kuma ɗebo wasu ranar 29 ga watan Agusta.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya ya kai kashi 15.48 cikin 100

    Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Hauhawar farashin kayayyaki na shekara a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 12.82 cikin 100 a watan Yuli, a cewar alƙaluman Hukumar Ƙididdiga ta National Bureau of Statistics (NBS).

    Wani rahoton NBS kan farashin kayan abinci na daban ya nuna tashin farashin kayayyakin abinci zuwa kashi 15.48 cikin 100 a watan Yuli, wanda ya fi na watan Yuni na kashi 15.18 cikin 100.

    Su ma alƙaluman na shekara sun ƙaru ne a kan 12.56 cikin 100 da aka samu a watan Yuni.

    Najeriya na fama da rikicin tattalin arziki da faɗuwar farashin mai ta haifar sakamakon annobar korona da kuma karyewar darajar Naira.

  15. 'Yan sanda sun kama mutumin da ya 'kashe' abokinsa a Lokoja

    'Yan sandan Najeriya

    Asalin hoton, NAN

    'Yan sanda a Lokoja babban birnin birnin Jihar Kogi sun kama wani mai suna Murtaala Dare bisa zargin kashe abokinsa yayin wata taƙaddama.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito kakakin rundunar ‘yan sandan Kogi, DSP Willliam Aya, ya shaida wa manema labarai ranar Litinin a Lokoja cewa an kama wanda ake zargin a maɓoyarsa a safiyar Litinin.

    Aya ya ce Dare mai shekara 32 kuma mai aikin walda, ya kashe abokinsa mai suna Lukman a unguwar Jackies da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 16 ga watan Agusta.

    A cewarsa, Dare da Lukman suna tare da wasu abokan hirarsu a lokacin da wata husuma ta ɓrke tsakaninsu, abin da ya janyo naushe-naushe tsakanin abokan.

    Sai dai, an ce Dare ya fi ƙarfin Lukman, inda ya ɗaga shi sannan ya buga shi da ƙasa kuma ya fito da wuƙar da aka ce ya yi amfani da ita wurin kisan.

  16. 'Tambayoyin Jarrabawar WAEC da ke yawo na jabu ne'

    WAEC

    Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Makarantar Sakandare Ta Afrika Ta Yamma WAEC ta gargaɗi ɗalibai cewa satar amsar Jarrabawar Lissafi da ke yawo a shafukan sada zumunta ta jabu ce.

    Hukumar WAEC ta shaida wa sashen Pidgin na BBC cewa masu zamba ne suka samar da irin waɗannan takardun jabun inda suke so su yi amfani da su don karɓar kuɗaɗe daga hannun mutane.

    A yau Litinin ɗaliban ajin ƙarshe na sakandare a faɗin Najeriya ke soma rubuta jarrabawarsu ta kammala karatu bayan da aka samu jinkiri na watanni saboda annobar cutar korona.

    Ɗalibai fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar ne ake sa ran za su ɗauki tsawon makwanni suna rubuta jarrabawar da ake kira WAEC wadda kuma a kan yi a wasu ƙasashen yammacin Afirka.

    ''Duk wani ɗalibi da ya karɓi takardun jabun zai sha mamaki a yayin da ya shiga ɗakin jarrabaw ya ga ta sha bamban da wacce za a ba shi,'' in ji WAEC.

    Mai magana Hukumar da yawun WAEC Demianus Ojijeogu ya ce ɗliban Ghana ba su zana jarrabawar Lissafi ta WAEC ta bana ba kamar yadda mutane ke faɗa.

    WAEC ta faɗi haka ne bayan da aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa irin tambayoyin da aka yi w ɗaliban Ghana ne za a yi wa na Najeriya a takardar jarrabawar.

    "Na ga takardu uku na jabu a jiya,'' in ji Mr. Ojijeogu.

  17. China na yin gwajin rigakafin korona a mataki na uku

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    China ta sahale yin gwajin rigakafin korona da ta samar a mataki na uku.

    Kamfanin CanSino Biologics ne ya samar da ƙwayar tare da haɗin gwiwar rundunar sojan ƙasar ta People's Liberation Army.

    Tuni aka yi gwajin a matakai daban-daban, yanzu kuma za a yi a mataki na uku, inda aka yi wasu gwaje-gwajen a ƙasashen waje.

    A makon da ya gabata ne Rasha ta ce ta bayar da umarnin fara amfani da wani rigakafin cutar da ta samar da kanta.

  18. Masu zanga-zanga sun yi wa shugaban ƙasa ihu a Belarus

    Belarus

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikata sun yi ta yi wa Shugaban Ƙasar Belarus Alexander Lukashenko ihu a yayin da ya kai ziyara wata ma'aikata yayin da mutane ke sake yin fushi da shi kan aben da aka gudanar mai cike da ruɗani.

    Ma'aikata sun yi ta yin ihun ''ka tafi'' ga shugaban Belarus da ya daɗe a kan mulki a yayin da ya kafe cewa ba zai bari a yi sabon zaɓ ba bayan da ake zargin wanda aka yi na cike da maguɗi.

    An fara yahjin aiki a ƙasar inda har gidan talbijin mallakin gwamnati ya bi sahu, har ma'aikata suka yi tafiyarsu a ranar Litinin.

    Ƴar takarar jam'iyyar hamayya Svetlana Tikhanovskaya ta ba da shawarar cewa za ta iya tsayawa a matsayin shugabar riƙon ƙwarya. Mutane da dama ne aka sa ran za su fara yajin aiki a Belarus, bayan da aka shafe karshen mako ana zanga-zangar neman shugaba Alexender Lukashenko ya sauka daga kan mulki.

    An kiyasta cewa kusan mutane dubu dari ne suka mamaye babban birnin Minsk a ranar Lahadi, su na kira da a sake gudanar da zaben shugaban kasar da aka yi a makon jiya, kana shugaban ya sauka daga kan mukaminsa.

  19. Labaran rana cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Minti Ɗaya da BBC na Rana
  20. Hukumomi a Kamaru na fargabar ɓarkewar annobar korona karo na biyu

    Kamaru

    Asalin hoton, INEC

    Hukumomi a Kamaru sun ce akwai fargabar sake ɓullar sabon zango na kamuwa da annobar korona a dalilin sakacin da jama’a suke yi wurin sanya makarin fuska.

    Ministan Lafiya Manaouda Malachie ya bayyana hakan.

    Sakamakon haka ne hukumomin suka ce nan gaba za a kai ga matakin hukunta duk wani wanda yake yawo a bainar jama’a ba tare da ya sanya makarin fuska ba.