Muna godiya da kasancewa da mu
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya tare da fatan za mu haɗu a wani shafin na labarai kai-tsaye.
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya tare da fatan za mu haɗu a wani shafin na labarai kai-tsaye.

Asalin hoton, @Fmohnigeria
Ƙasar Daular Larabawa ta United Arab Emirates (UAE) ta aike da kayan tallafi ga ƙasashen Najeriya da Sudan domin agaza musu wurin yaƙi da annobar korona, wadda ake yi wa laƙabi da Covid-19.
Sarkin Dubai Mohammed bin Rashed ne ya bayar da umarnin kai kayan, a cewar rahoton shafin jaridar The National ta Dubai a yau Lahadi.
An kai kayan tallafin ne da suka haɗa da kayayyakin kiwon lafiya da abinci daga birnin International Humanitarian City da ke Dubai.
Ƙasar da ke yankin ƙasashen Larabawa na Gulf ta sha aika irin waɗannan kayayyaki ga wasu ƙasashe domin agaza musu wurin rage kaifin annobar cutar.
A ranar Alhamis, kamfanin dillancin labaran ƙasar WMA ya ce ya zuwa yanzu UAE ta aika tan fiye da 1,277 na kayan agaji ga ƙasashe 107, inda ma'aikatan lafiya kusan miliyan ɗaya da rabi suka amfana.

Asalin hoton, Reuters
Wasu ƴan bindiga da ake tunanin mayaƙan Al-Shabab ne sun afka wa wani otal a Mogadishu, babban birnin Somalia.
Aƙalla mutum biyar ake tunanin an kashe a harin yayin da jami'an motar ɗaukar marasa lafiya suka ce sun kwashi mutum kusan 30 zuwa Asibiti.
Wani bam kuma ya tashi a wata mota a ginin otal ɗin da ba a daɗe da ginawa ba wanda rahotanni suka ce mallakin wani ɗan majalisa ne da manyan jami'an gwamnatin Somalia da baƙi daga ƙasashen waje ke sauka.
Ba a tantance adadin yawan mutanen da harin ya rutsa da su ba a otal ɗin yayin da dakarun gwamnati ke ci gaba da musayar wuta da ƴan bindigar da ke cikin ginin.
Kafofin yaɗa labaran Somalia sun ce akwai wani babban jami'i a ma'aikatar yaɗa labarai ta Somalia cikin waɗanda aka kashe.
Al-shabab dai ta sha kai hare-hare a cikin wata biyu da suka gabata a Mogadishu .

Asalin hoton, Getty Images
An saki wasu ma'aikata 'yan China huɗu da aka yi garkuwa da su a Jihar Cross Rivers da ke kudancin Najeriya, a cewar 'yan sanda ranar Lahadi.
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da 'yan Chinan ne a yankin Akpabuyo bayan sun kashe ɗan sandan da ke gadinsu a watan da ya gabata.
"Mun samu damar kuɓutar da 'yan China a Akpabuyo da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar," in ji mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar mai suna Irene Ugbo a hirarta da AFP.
Sai dai ba ta iya bayyana ko an biya kuɗin fansa ba.
"Suna ci gaba da samun kulawa a wani asibiti da ba za a faɗi sunansa ba sannan kuma ba a kama kowa ba. Ba ni da wata masaniya ko an biya wasu kuɗi kafin a sake su," in ji ta.
Akwai kamfanonin China da dama da ke ayyukan biliyoyin daloli da a Najeriya da suka haɗa da tituna da layin dogo da filayen jirgin sama.
Kashi 75 cikin 100 na matan duniya za su gamu da matsalar ƙaiƙayin gaba aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu, a cewar hukumar daƙile yaduwar cutuka ta Amurka, CDC.
Sai dai ta ce wannan matsala na da saurin warkewa idan aka yi amfani da magungunan da suka dace.
ƘaiƘayi da raɗaɗi a lokacin yin fitsari ko saduwa, fitar ruwa mai yawa ta gaba da ƙuraje na daga cikin alamomin cutar, kamar yadda Dakta Anisa Umar Ambursa, ta asibitin Federal Medical Centre da ke Jabi a Abujan Najeriya, ta yi bayani.

Asalin hoton, Others
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya taya tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida murnar cika shekara 79 da haihuwa.
An haifi Babangida a ranar 17 ga watan Agustan 1941 a garin Minna da ke Jihar Neja a Arewa ta Tsakiyar Najeriya kuma a gobe Ltinin ne tsohon shugaban na mulkin soja yake cika shekara 79.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina ya fitar a yau Lahadi ta ce shugaban ya ce za a ci gaba da tunawa da ayyukan da Babangida ya gudanar a Najeriya.
Kazalika ya yi addu'ar "Allah Ya ci gaba da ƙarfafa shi (Babangida) tare da ba shi lafiya da tsawon kwana".

Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta ce ta shaida wa Shugaban Belarus, Alexander Lukashenko cewa a shirye take ta ba shi taimakon soja idan ya zama dole yayin da masu zanga-zanga suka shirya wani gagarumin maci a ƙasar ranar Lahadi.
Dubban mutane ne a Minsk suka hau tituna domin yin Allah-wadai da sake zaɓen Mista Lukashenko a karo na biyu duk da mutuwar mutum biyu tare da kama dubbai tun bayan kaɗa kuri'a a Lahadin da ta wuce.
Reuters ya rawaito Fadar Kremlin na cewa Shugaba Putin ya faɗa wa Lukashenko cewa ƙasarsa a shirye take ta agaza wa Belarus ta hanyar ƙulla yarjejeniyar soja idan hakan ta kama sannan kuma idan ƙasashen duniya suka uzura mata.
Sai dai ba ta bayyana ko waɗanne ƙasashe ba ne.
Masu adawa da Lukashenko wanda ya shafe shekara 26 a kan mulki, sun ce an yi maguɗi domin ɓoye gaskiyar cewa jama'ar ƙasar ba sa sonsa. Ya ƙaryata batun maguɗi a sakamakon, wanda ya ba shi fiye da kashi 80 cikin 100 na ƙuri'un.
A filin Amsoshin Takardunku na wannan makon, mun amsa yadda tsarin mulkin Lebanon yake da kuma ma'anar kujerar na-ƙi.

Asalin hoton, Nigerian Police
Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou ya karɓi baƙuncin tawagar wakilai da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika ranar Asabar domin tattauna matsalar tsaro da ta addabi ƙasashen biyu.
Babban Sufeton 'Yan Sanda Mohamed Adamu ne ya jagoranci tawagar, a cewar rahoton shafin aNiamey na Nijar.
"Mun zo ne bisa umarnin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin tattauna matsalolin tsaro da suka shafi ƙasashemmu," Mista Adamu ya bayyana a wurin wani taron manema labarai.
Ya ci gaba da cewa: "Mun gana da ministan cikin gida da kuma sufeton 'yan sanda (na Nijar) da kuma jami'an rundunar tattara bayanan sirri. Mun cimma muhimman abubuwa game da yadda za mu kare ƙasashenmu."
Nijar da Najeriya na fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi musamman a jihohin da ke kan iyakar ƙasashen biyu na Borno (a Najeriya) da Difa, sai kuma Jihar Tilaberi da ke kan iyakar Mali, wadda aka tsawaita dokar ta-ɓaci a baya-bayan nan.
Ƙungiyar ‘yan kasuwar Najeriya mai suna National Association of Nigerian Traders (NANTS) ta yi kira ga mahukunta da masu ruwa da tsaki da su taimaki ‘yan ƙasar da aka rufe wa shagunan kasuwanci a ƙasar Ghana.
Shugaban ƙungiyar Dr Ken Ukaoha ya yi kiran ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito.
Mahukunta a Ghana sun fara rufe shagunan kasuwancin ‘yan ƙasashen waje mafi yawansu ‘yan Najeriya waɗanda suka ce ba su da cikakkun takardu tare da cin alwashin za su ci gaba da yin hakan har sai sun yi abin da ya dace.
An yaɗa wani bidiyo a shafukan zumunta ranar Asabar, wanda aka yi zargin cewa 'yan Najeriya ne ake wulaƙantawa a Ghana.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ukaoha wanda masanin shari’ar tattalin arziki ne, ya bayyana rashin jin daɗinsa, yana mai cewa “wulakancin ya gaza bayar da damar samar da mafita kuma ma ya fi ƙarfin ƙungiyar cigaban tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS.

Asalin hoton, EPA
A ranar Juma'a 14 ga watan Agustan 2020 ne aka cika wata shida da ɓullar cutar korona a Afrika inda aka samu mutum na farko da ya kamu a Masar cikin watan Fabrairu.
Kawo yanzu dai, fiye da mutum miliyan ɗaya ne suka kamu da cutar a nahiyar Afrika, kuma har yanzu ana samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar a ƙasashen nahiyar.
Dakta Nasir Sani Gwarzo, wani ƙwararren likita ne kuma masani kan cutuka masu yaɗuwa, kuma ya bayyana wasu dalilai a ya ke ganin suka sa cutar ta korona ba ta yi wa ƙasashen Afirka kamun kazar kuku ba duk da a cewarsa ba a tabbatar da dalilan ba kimiyyance

Asalin hoton, Getty Images
An zaɓi ɗan wasan tsakiyar Manchester City, Kevin de Bruyne a matsayin gwarzon ɗan wasan gasar Premier League na bana.
Ɗan ƙwallon mai shekara 29 ya ci ƙwallo 13 yayin da Man City ta ƙare a mataki na biyu bayan Liverpool, zakarun gasar.
Kazalika ɗan wasan ya bayar an ci ƙwallo 20, abin da ya sa ya kamo ɗan wasan Arsenal Thierry Henry a kakar wasa guda da ya cimma a gasar 2002-2003.
Shi ne ɗan ƙasar Belgium na uku da ya lashe kyautar cikin shekara tara bayan Vincent Kompany da Eden Hazard.

Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE
Babban Sifeton 'Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bayar da umarni ga kwamishinonin 'yan sanda 36 da ke fadin ƙasar, da su yi duk mai yiwuwa wurin ganowa da kama duk wani ko kuma wata ƙungiya da ke rike da makaman da aka haramta amfani da su.
A sanarwar da rundunar 'yan sandan ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an bayar da wannan umarnin ne sakamakon shirye-shirye na zaɓen da za a gudanar a jihar Edo da Ondo da kuma yunƙurin rundunar na daƙile bazuwar muggan makamai.
Babban sifeton ya kuma bayar da umarni ga duka kwamishinonin 'yan sanda da su kira taron wayar da kai wanda za a yi wa ƙungiyoyin 'yan banga da na bijilanti domin tabbatar da cewa suna aikinsu bisa tsari.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sulhun da aka yi tsakanin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Isra'ila ya yi sanadiyar buɗe hanyoyin sadarwa na wayoyin salula tsakanin ƙasasehn biyu.
A baya dai, mutumin da ke a Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ba zai iya kiran wanda ke a Isra'ila ba.
Ministan sadarwa na Isra'ila, Yoaz Hendel, ya yi murna kan matakin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan ta ɗauka na cire wannan takunkumi, kuma ya ce ƙasashen za su amfana ta hanyar tattalin arziƙi.
A wata yarjejeniya da ƙasashen kuma suka saka wa hannu, sun amince kan wani batu da ke da alaƙa da gudanar da bincike kan cutar korona.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Saudiyya ta yanke shawawar cewa ɗalibai za su fara karatu daga gida ta intanet a maimakon zuwa makaranta.
Jaridar Saudi Gazette ce ta ruwaito hakan inda ministan ilimi na ƙasar Dakta Hamad Al-Sheikh ya ce ɗaliban za su fara karatun ne na tsawon makonni bakwai, "idan akwai buƙatar a tsawaita, sai a tsawaita" in ji shi.
Ma'aikatar ilimi ta ƙasar ta bayyana cewa za a ƙaddamar da wata manhaja mai suna 'Madarasati', kuma da manhajar ce ɗaliban za su rinƙa amfani wurin karatu.
Ana sa ran ɗaliban za su fara darasi a ranar 30 ga watan Agusta.
Gwamnatin ƙasar dai ta ɗauki wannan matakin ne a yunƙurinta na daƙile yaɗuwar annobar korona.
Tun a ranar 9 ga watan Maris din 2020 aka rufe duka makarantu a ƙasar

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Afrika Ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya bayyana cewa za a sassauta kusan duka dokokin da aka ƙaƙaba a kasar sakamakon annobar korona a gobe Litinin.
Shugaban ya bayyana hakan a daidai lokacin da cutar ke ƙara ƙaruwa a ƙasar.
Cikin dokokin da za a sassauta, har da dokar da aka saka mai taƙaddama da ta haramta sayar da barasa a ƙasar.
Haka kuma, za a ci gaba da tafiye-tafiye da taron mutanen da ba su da yawa da kuma buɗe wuraren kasuwanci.
A wani jawabi da ya yi ta talabajin, shugaban ya ce sassaucin zai taimaka wurin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.
Wakilin Amurka na musamman a Afghanistan Zalmay Khalilzad, ya yi kira ga gwamnatin Afghanistan da ƙungiyar Taliban da su fara tattaunawa kan zaman lafiya ba tare da ɓata lokaci ba.
A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kuma yi Allah wadai da wani hari da 'yan bindiga suka kai wa wata fitacciyar 'yar kare haƙƙin bil adama ta Afghanistan, Fawzia Koofi, inda ya ce waɗanda suka kai wannan harin sun yi ne domin kawo tarnaki ga shirin da ake yi na sulhu tsakanin ɓangarorin biyu.
Ƙungiyar Taliban dai ta musanta cewa ita ta kai wannan hari.
Ms Koofi ta samu rauni a kafaɗarta. A ranar Juma'a, gwamnatin Afghanistan ɗin ta saki fursunonin Taliban 400, inda ake sa ran fara tattaunawar sulhu ba da jimawa ba bayan sakin na su.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, MANBAR.ME
'Yan ƙungiyar Al-Qaeda a Yemen sun kashe wani likitan haƙori wanda suka zarga da yi musu leken asiri.
Hotunan gawar likitan na ta yawo a kafafen sada zumunta, inda aka gicciye shi a wurin aikinsa a lardin al-Bayda da ke ƙasar.
'Yan tayar da ƙayar bayan suna zargin cewa likitan na aiki da Amurka inda ya ke ba su bayanai da za su kai ga kama manyan jagororinsu.
A farkon shekarar nan, Amurkar ta bayyana cewa ta kashe wani shugaban ƙungiyar wato Qasim al-Raymi.

Asalin hoton, Getty Images
Fadar White House ta sanar da mutuwar ƙanin Shugaba Donald Trump, Robert a wani asibitin New York.
Robert Trump yana da shekaru 71 sannan an bayyana cewa ya samu matsala a ƙwaƙwalwa bayan wata faɗuwa da ya yi a baya-bayan nan.
A ranar Juma'a ne Shugaba Trump ya ziyarci marigayin a asibiti.
A 'yan kwanakin nan kafin ya fara rashin lafiya, Mista Robert ya je kotu a ƙoƙarinsa na hana buga wani littafi da wata 'yar uwarsa Mary ta rubuta kan Shugaba Trump.
Masu bibiyarmu a wannan shafin barkanmu da wannan safiya ta Lahadi, 16 ga watan Agustan 2020.
A yau ma za mu ci gaba da kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye a wannan shafin, za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko Instagram domin bayyana ra'ayoyinku ko kuma tafka muhawara dangane da labaran da muke wallafawa.