Cutar korona ta kashe mutum fiye da dubu 50 a Mexico
Hukumomin lafiya a Mexico sun ce yawan mutanen da suka mutu sanadin annobar korona ya karu zuwa fiye da dubu 50.
Amurka da Brazil ne kadai kasashen da suka fi yawan wadanda wannan cuta ta shafa.
A farkon makon nan ne Shugaba Andres Manuel Lopez ya sanar cewa zai rika yin shiru na minti daya duk rana domin tunawa da wadanda suka mutu.