Amurka ta bai wa Ethiopia taimakon na'urar ventilators
Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin na’urar taimakawa numfashi 250 ga kasar Habasha domin taimaka mata wajen yaƙi da annobar korona.
An bayar da taimakon ne bayan wani alkawari da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Firaiminista Abiy ta waya a watan Afrilu.
Jakadan Amurka a ksar Michael Raynor ya ce taimakon wani kokari na karfafa gwiwa ga mutanen Ethiopia.
Ministan lafiya na Ethiopia Dakta Lia Tadesse ya nuna farin cikinsa da wadannan kayan aiki da aka bai wa kasarsa.
A wata sanarwa da Amurka ta fitar ta ce za ta fitar da tsarin yadda za a yi aiki da kayan da kuma samar da horo ga ma’aikatan lafiya na Habasha domin samun kwarewa.