Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mutum 135 ne suka mutu a Beirut, 5,000 sun jikkata

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Jama'a mun kawo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. Man City ta kammala ɗaukar Nathan Ake daga Bournemouth

    Manchester City ta kammala ɗaukar ɗan wasan bayan Bournemouth mai suna Nathan Ake kan fan miliyan 40.

    Ɗan ƙasar Netherlands wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a Etihad, ya bayyana komawa ƙungiyar ta Guardiola a matsayin "mafarki".

    "Pep Guardiola kociya ne da ake ƙunarsa a duniya baki ɗaya. Abubuwan da ya yi a harkar ƙwallo suna nuna kan su," in ji ɗan wasan mai shekara 25.

    "Nasarorin da ya samu abin mamaki ne sannan salon ƙwallon da yake bugawa yana burge ni."

  3. An kama wasu 'yan jarida da karya ƙa'idar aiki a Kamaru

    Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta yanke sabbin hukunce-hukunce a kan wasu ‘yan jarida da wasu shugabannin kamfanonin yaɗa labarai.

    Bayan ta yi zama wata biyu da suka gabata, hukumar ta ce ta samu ‘yan jarida da Shugabanninsu da rashin bin ƙa’idojin aikin jarida wurin yaɗa labarai da wallafa su.

  4. Buhari ya miƙa ta'aziyyar rasuwar jagoran ɗariƙar Tijjaniya na Afirka

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna alhini da baƙn cikin rasuwar Sheikh Ahmed Tidiane Niass, Khalifa jagoran kungiyar Musulunci ta Tijjaniyya na Nahiyar Afirka.

    Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban na musamman kan kafafen yaɗa labarai, Buhari Sallau ya wallafa a shaifnsa na sada zumunta.

    Sanarwar ta ce cikin sakonsa na ta'aziyya zuwa ga Shugaba Macky Sall na Senagal da 'yan Senegal da ma mabiya ɗariƙar Tijjaniyya, Buhari ya ce mutuwar "abin baƙin ciki ne ga dukkaninmmu" sannan ya yi kira da a koyi da jagoran.

    "Shugaban kasa ya tuno cewa a watan Yuni na shekarar 2018, Sheikh Ahmed Niass ya ziyarci fadar shugaban kasa a birnin Abuja tare da wasu fitattun 'yan Najeriya ciki har da shugaban rukunin kamfanin BUA Alhaji Abdulsamad Rabi'u," in ji sanarwar.

    "A madadin ni kaina da gwamnati da kuma al'ummar Najeriya, Shugaba Buhari ya yi addu'ar samun madawwamin nutsuwa ga wannan rai da ta rasu."

  5. Mazauna karkara a Nijar sun koka kan wahalar rayuwa da ke hana 'ya'yansu zuwa makaranta

    A jamhuriyar Nijar, mazauna yankunan karkara ne ke kokawa da wahalhalun rayuwa da suka ce suna kawo masu cikas a kokarinsu na neman cigaba.

    A yankin Tahoua da Wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou ta ziyarta kwanakin baya, ta tattauna da wata mata da ta ce rashin wadata na hana yaransu zuwa makaranta.

    Hadiza Mahamadou ta ce suna yin wasu 'yan sana'o'i na cikin gida don taimakama gidajensu.

  6. Gwamnatin Bauchi ta saka yara 49,534 a makarantun allo

    Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta ɗauki yara 49,534 a makarantun almajirai da gwamnatin tarayya ta gina a jihar.

    Mallam Abdullahi Muhammad, kakakin hukumar BASUBEB ta Bauchi ne ya bayyana hakan a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na NAN ranar Talata a Bauchi.

    Ya ce an buɗe sabbin makatantun tsangaya 931 cikin shekara biyu da suka wuce domin faɗaɗawa da kuma a ƙara bai wa yara damar samun ilimi na zamani a Jihar Bauchi.

    "A cikin yara 49,534 da aka ɗauka, akwai mata 14,497 da maza 35,037, yana mai cewa an kaddamar da shirin ne a cikin ƙaramar hukuma tara a na Jihar,” in ji shi.

  7. Ɗaruruwan 'yan Lebanon na taimaka wa waɗanda suka rasa wurin kwana da gidajensu

    Ɗaruruwan 'yan Lebanon sun bai wa 'yan uwansu gidajen kwana, waɗanda hatsarin abubuwan fashewa ya rutsa da su.

    Sun yi ta amfani da maudu'in #OurHomesAreOpen wato "gidajemmu a buɗe suke" a shafukan sada zumunta da Larabci da Turancin Ingilishi domin neman waɗanda suke da buƙata.

    "Na yi niyyar na yi wani abu a kai, duk na ɗimauce," a cewar wanda ya kafa dandalin ThawraMap, wanda ake amfani da shi domin gano wuraren zanga-zanga wanda kuma yanzu ake amfani da shi don gano inda ake da gadaje da kuma otel na kyauta.

    "A yanzu mutane da yawa za su ras wurin kwana. Za su tafi wurin 'yan uwansu da abokai amma bayan kwana biyu kuma ya za su yi?" in ji wani ɗan gwagwarmaya a hirarsa da Reuters.

    Tun farko gwamnan Beirut, Marwan Aboud ya ce kusan mutum 300,000 ne suka rasa mahallansu sakamakon fashewar da ta afku ranar Talata.

  8. 'Yan Faransa 21 sun jikkata a fashewar birnin Beirut

    Ofishsin mai shigar da ƙara na Faransa ya ce 'yan ƙasar 21 ne suka jikkata a hatsarin fashewar wasu sinadarai a Bierut na Lebanon ranar Talata.

    Remy Heintz ya ce an fara gudanar da bincike kan waɗanda suka jaikkata din.

    Ministan Lafiya na Lebanon ya bayyana cewa mutum 135 ne suka mutu sannan wasu 5,000 suka jkkata sakamakon fashewar tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate - wanda ake haɗa takin zamani da shi - bayan an ajiye shi ba tare da kulawa ba a wani wurin ajiya

  9. Labarai da dumi-dumi, Mutum 135 ne suka mutu a Beirut, 5,000 sun jikkata

    Ministan Lafiya a Lebanon ya bayyana babu daɗewa cewa mutanen da suka mutu sakamakon fashewar ranar Talata sun zama 135 tare da jikkata wasu 5,000, a cewar kafar Al Manar TV.

    har yanzu akwai adadin mutanen da ba a san inda suke ba, in ji shi.

  10. Game da hatsarin da ya kashe mutum 113 a Beirut na Lebanon

    Ga abubuwan da muka sani game da fashewar sinadarai a Beirut na Lebanon ranar Talata zuwa yanzu:

    • Ministan yaɗa labarai ya sanar da saka dokar ta-ɓaci ta tsawon mako biyu
    • Majalisar ministoci ta nemi jami'an tsaro da su tabbata ba su bari wani ya je wurin da fashewar ta faru ba a ranar Talata
    • Fiye da mutum 100 ne ba a san inda suke ba kuma ana tsaka da ayyukan ceto
    • Aƙalla mutum 113 ne suka mutu sannan fiye da 4,000 suka jikkata
    • Shugaban Ƙasa Michel Aoun ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon fashewar tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate - wanda ake haɗa takin zamani da shi - bayan an ajiye shi ba tare da kulawa ba a wani wurin ajiya
  11. Al'ummar Sri Lanka na kaɗa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa

    Yau al'umar Sri Lanka za su kaɗa ƙuri'a domin zaben sabbin 'yan majalisa inda aka tanadi matakan kariya domin hana bazuwar cutar korona.

    Shugaba Gotabaya Rajapaksa na fatan ƙoƙarin da yake wajen yaƙi da annobar ta korona zai taimaka wa jam'iyyarsa ta samu nasara.

    Idan har jam'iyyar ta lashe kashi biyu bisa uku na kujerun majalisar, hakan zai ƙara wa shugaban ƙarfi kan madafun iko.

    Sai dai akwai fargaba cewa hakan zai bai wa Mista Rajapaksa da iyalinsa da ke fuskantar zarge-zargen cin hanci da take hakkokin bil adama iko sosai.

  12. Ƙarin 'yan Najeriya 306 sun koma gida daga Dubai

    Ƙarin wasu 'yan Najeriya 306 sun isa Abuja babban birnin ƙasar daga ƙasar Daular Larabawa wato UAE da misalin ƙarfe 08:44 na safiyar Laraba.

    An ɗebo su ne sakamakon maƙalewa da suka yi a ƙasashen waje saboda matakan da ake ɗauka na daƙile yaɗuwar korona.

    Hukumar 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta NIDCOM ta bayyana cewa wasu daga cikinsu za su sauka a Abuja, wasu kuma su wuce Legas.

    Dukkaninsu gwaji ya nuna ba sa ɗuke da cutar a cewar hukumar sannan kuma za su killace kansu na tsawon mako biyu.

  13. Gwamna Masari ya gana da Shugaba Buhari

    Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock da ke Abuja.

    BBC ba ta samu ƙarin bayani ba game da abin da shugabannin biyu suka tattauna. Sai dai idan ba a manta ba Jihar Katisna na shan fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da hare-haren 'yan fashin daji.

    A baya dai gwamnatin jihar ta ƙulla yarjejeniya da wasu daga cikin ƙungiyoyin maharan, sai dai da alama hakan bai hana su ci gaba da kashe mutane babu gaira babu dalili ba.

    Fadar shugaban ƙasar ta sha bayyana cewa sojojin ƙasar sun ƙaddamar da ayyukan kakkaɓe miyagun a ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji, inda sojojin ke cewa suna cin galaba a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto.

  14. Taswirar wuraren da sinadarai suka fashe a Lebanon

  15. Ƙarin kamfanin sufurin jirgin sama ya kori ma'aikata 100 a Najeriya

    Ƙarin wani kamfanin sufurin jirgin sama ya kori matuƙa da kuma injiniyoyi 100 a ci gaba da faɗi-tashin da ɓangaren sufurin yake yi sakamakon annobar korona.

    Kamfanin Bristow Helicopters ya fuskanci matsi sakamakon annobar ta korona kuma ya ce matakin ba mai sauƙi ba ne, wanda ya zama dole ya ɗauka yayin da yake ta ƙoƙarin yin garambawul ga ayyukansa.

    Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗn bayan ɗaya daga cikin manyan kamfanonin jirage a Najeriya - Air Peace - ya dakatar da matuƙa jiorgin kusan 70 sannan ya rage albashin ma'aikata.

    Kamfanonin sufurin jiragen helikwafta na samun kwastomomi ne akasari ta hanyar aiki da ɓangaren man fetur da iskar gas a Najeriya.

  16. Idan yanzu kuka shigo shafin namu, ga taƙaitattun abubuwan da muka wallafa

    • Ma’aikatan agaji a Lebanon ne kokarin zakulo daruruwan mutane da suka bace sakamakon fashewar abubuwa a kusa da Beirut babban birnin kasar a ranar Talata. A yanzu haka ana zaman makoki a kasar bayan fashewar ta kashe aƙalla mutum 100 sannan fiye da mutum 4,000 sun ya jikkata babban birnin ƙasar Beirut.
    • Sama da mutum 700,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar korona a fadin duniya, kamar yadda jami’ar Johs Hopkins mai bibiyar kididdigar korona ta bayyana. An fi samun mamatan a Amurka in da take da mutum 156,830 da suka mutu, sai Brazil da take da (95,819), da kuma Mexico da ke da mutum 48,869
    • Masar ta fice daga sabuwar tattaunawar aikin ginin samar da wutar lantarki da Habasha ke shirin yi daga kogin Nilu. Masar din ta bijire ne bayan gabatar da sabbin dokokin da Habasha ta yi. Kazalika ita ma Sudan ta yi barazanar ficewa daga tattaunawar.
    • Kocin Man United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce lashe kofin Europa abu ne mai matukar kyau ga kungiyarsa. United za ta buga karawa ta biyu a zagayen ‘yan 16 a gasar ta Europa League da kungiyar LASK anjima da karfe 8:00 agogon Najeriya.
  17. Minti Ɗaya da BBC

  18. Abin da za ku so ku sani game da sabuwar dokar kalaman ƙiyayya a Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta ce daga yanzu duk mutumin da aka samu da laifin yin kalaman kiyayya zai biya tarar Naira miliyan biyar, wato kari sau dari kenan kan tarar da a baya aka sanya kan wannan laifi.

    Ministan watsa labaran kasar Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja babban birnin kasar, lokacin da yake kaddamar da kwaskwarimar da aka yi wa dokar watsa labarai ta kasar.

    Ya ce ya dauki matakin ne bayan samun amincewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya bukaci a sauya dokar sakamakon irin kalaman kiyayya da 'yan kasar suka rika yi a lokaci da kuma bayan babban zaben kasar na 2019.

  19. Kashi daya cikin uku na 'yan Afghanistan sun kamu da korona

    Ministan lafiya na Afghanistan ya ce samfuran da aka dauka sun nuna kusan kashi daya cikin uku na yawan al'ummar kasar wanda ya kai miliyan 10 na dauke da korona.

    An kaddamar da binciken ne watanni biyu baya tare da taimakon WHO da kuma jami'ar Johs Hopkins.

    A mafi yawan lokuta, jami'an da suka kamu basa nuna alamun cutar kuma abu ne mawuyaci sun iya gano ta.

    Wani gwajin gama-gari da aka yi ya nuna cewa sama da kashi 50 cikin 100 na mazauna babban birnin Kabul sun kamu da cutar.

    Akwai a kalla mutum dubu36 da aka tabbatar suna dauke da cutar akwai kuma sama da mutum 1,200 da suka mutu ya zuwa yanzu.

  20. Sama da mutum 700,000 korona ta kashe a duniya

    Sama da mutum 700,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar korona a fadin duniya, kamar yadda jami'ar Johs Hopkins mai bibiyar kididdigar korona ta bayyana.

    An fi samun mamatan a Amurka, inda take da mutum (156,830) da suka mutu, sai Brazil da take biye mata da adadin wadanda suka mutu (95,819), Mexico na ta uku da mutum (48,869), a Burtaniya mutum (46,295) ne suka mutu sai kuma India da ke da (39,795).

    Yana da muhimmanci a gane cewa ba zai yiwu a kwatanta kasashe duka da ma'auni daya ba, saboda banbancin da ke akwai wajen yadda suke gwajin cutar da kuma yadda wasu ke kirga wadanda suka mutu dalilinta.

    Banbancin yawan al'umma na da muhimmanci yayin kwantanta kasashen.

    Burtaniya na da mutane mikiyan 66, yayin da India ke da mutane biliyan daya da digo uku.