Shugaban Mali ya rage yawan ministocinsa
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta ya rage yawan mambobin majalisar zartarwarsa a yayin da yake yunkurin kafa gwamnatin hadaka, a cewar sanarwar da ta fito daga ofishinsa.
Sanarwar ta kara da cewa sabuwar majalisar zartarwar za ta kunshi Firaiminista Boubou Cissé da ministoci shida.
Ya dauki matakin ne sa'o'i kadan bayan kammala taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS wanda ya yi kira a kafa gwamnatin hada kan kasa da gudanar da sabon zabe, bayan zaben da aka yi kwanakin baya mai cike da ka-ce-na-ce.
Ba a yi jawabi kan sauran shawarwarin da ECOWAS ta bayar ba, wadanda suka hada da sauke 'yan majalisar dokoki 31 wadanda ake takaddama kan zabensu, daga kujerunsu da kuma kwaskwarima ga kotun tsarin mulkin kasar.
Tun da farko gamayyar jam'iyyun hamayyar Mali sun yi watsi da tayin da aka yi musu na shiga gwamnatin hada kan kasa, suna masu dagewa cewa dole shugaban kasar ya sauka daga mulki.