Rufewa
- Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Nasidi Adamu Yahaya and Mustapha Musa Kaita
Ma'aikatar harkokin waje na Indiya sun bayyana cewa jakadu daga China da kuma Indiya sun cimma matsaya inda suka amince da cire dakaru kan iyakar ƙasashen.
Duk da cewa sanarwar bata fitar da wani cikakken bayani ba, sai dai an bayyana cewa yana da muhimmanci a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Tun a watan Yuni ne aka samu rikici kan iyakar ƙasashen inda aka kashe akalla sojojin Indiya 20 a wata arangama tsakaninsu da sojojin China.
Tattaunawar da jakadun suka yi ita ce ta 17 a yunƙurinsu na kawo zaman lafiya, amma duk da haka duka ɓangarorin biyu na tara dakaru a yankin kan iyakar.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Wata tawagar likitocin dabbobi ta mutum shida ta yi nasarar cire kilogiram 50 na roba daga cikin wata saniya bayan da aka shafe sa'a uku ana yi mata tiyata a kudancin Habasha.
Daya daga cikin likitocin, Dakta Firaol Waaqoo ya shaida wa sashen BBC Afaan Oromoo cewa: ''A yanzu saniyar tana raye kuma cikin koshin lafiya.''
''Shanu ka iya cin robobi saboda rashin samun ciyawar da za su ci, kuma yadda mutane ke zubar da datti yana zama matsala ga lafiyar dabbobi,'' kamar yadda ya kara da cewa.
A watan da ya gabata ma, mai saniyar Areerii Carii ya kai wa likitocin dabbobin wata saniyar daga cikin shanunsa wacce aka cire kilogiram 20 na roba daga cikinta.
''Ya sake kawo wannan ne saboda ya amince da mu,'' in ji Dr Firaol.
Mutanen Borana na kasar Habasha da ke yankin Oromo makiyaya da suka dogara tsantsa kan kiwo amma yankin da suke din ba a samun ruwan sama sosai.


Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ɗauki mataki kan kisan da 'yan ƙungiyar ISWAP da ke iƙirarin jihadi suka yi wa wasu ma'aikatan agaji a jihar Borno.
Sakatare Janar na majalisar Antonio Guterres ne ya yi kiran bayan da wani bidiyo wanda masu iƙirarin jihadi suka saki da ya nuna su suna kashe ma'aikatan agaji huɗu da kuma wani jami'in tsaro.
An dai yi garkuwa da ma'aikatan ne tun a watan da ya gabata, sai dai a farkon wannan makon ne aka tabbatar da mutuwarsu.
Yankin arewa maso gabashin Najeriya ya shafe sama da shekaru goma yana fama da rikice-rikice masu alaƙa da masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram a ƙasar.
Sama da mutum 30,000 ne aka kashe a yankin tun bayan fara wannan rikici.

Asalin hoton, Reuters
Kotun sojoji a Sudan Ta Kudu na yi wa wasu sojoji 75 shari'a bisa zargin su da take haƙƙin bil adama.
An dai kama sojojin ne a garin Yei da ke tsakiyar ƙasar, a halin yanzu kuma ana shari'ar ne a Juba babban birnin ƙasar.
Wannan zaman shari'ar na zuwa ne bayan wata ziyara da shugaban hafsan sojojin ƙasar Janar Johnson Juma ya kai a garin Yei da kuma makwaftanta, wuraren da rikici tsakanin 'yan tawaye da kuma dakarun ƙasar ya sa mutane da dama suka rabu da muhallansu.
"Fyade da kisa da kama mutane ba bisa ƙa'ida ba da fashi da makami da kuma azabtarwa," na daga cikin zarge-zargen da ake yi wa sojojin.

Asalin hoton, Reuters
Rundunar Sojin Amurka na zargin Rasha da ci gaba da kai makamai Libiya, wanda hakan ya saɓa wa takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta saka kan kai makamai ƙasar.
Rundunar Sojin Amurka reshen Afrika a wata sanarwa da ta fitar, ta ce irin makaman da ake kai wa Libiya, shi ya nuna sa hannunta a cikin rikicin ƙasar.
An kwana biyu dai ana rikici tsakanin ɓangaren Janar Khalifa Haftar da kuma gwamnatin Libiya wadda Majalisar Dinkin Duniya ke goya wa baya.
Ko a kwanakin baya sai da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta gargaɗi ƙasashern duniya kan katsalandan da kuma ɗaukar ɓangare da suke yi a rikicin Libiya.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta buƙaci ma'aikatan gwamnati da ke zaune a Abuja da su je a yi musu gwajin cutar korona.
Jaridar Punch ta ruwaito wata sanarwa daga ofishin babbar sakatariya kan jin daɗin ma'aikata ta tarayya Dakta Evelyn Ngige inda ta buƙaci ma'aikatan da su je a yi musu gwajin
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin tarayyar ƙasar ta samar da kayayyakin gwajin cutar ta korona a wani wuri da ake kira ThisDay Dome, Mohammed Kur Avenue a Abuja babban birnin ƙasar.
Za a rinƙa gudanar da gwajin ne daga 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma.

Asalin hoton, NigGov
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya koma Jam'iyyar APC.
Mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmed ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.
A yau Juma'a ne dai Yakubu Dogara tare da Gwamnan Yobe Mai Mala Buni suka kai ziyara ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
A 2018 ne dai Yakubu Dogara tare da wasu 'yan majalisa suka sauya sheƙa daga APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, NG

Asalin hoton, NG
Gwamnatin Afganistan ta ce ba za ta saki wasu mayakan taliban kusan su dari shida ba, saboda sun aikata miyagun laifuka, tare da tauye hakin bil`adama.
Gwamnatin ta yi wannan furucin ne bayan kungiyar Taliban din ta yi tayin fara tattaunawar sulhun da aka dade ana jinkirtawa, amma da sharadin cewa za a saki ‘yan kungiyar da gwamanti ke tsare da su.
Tuni dai gwamnatin kasar ta saki `yan Taliban fiye da 4000 ta hanyar musayar fursunoni, wadda wani bangare ne na yarjejeniyar da Amurka ta kulla da `yan kungiyar Taliban din, a watan Farairun da ya wuce.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Rukunin farko na alhazai ya sauka a filin jirgi saman Sarki Abdulaziz da ke Jedda inda za su dauki aniyar gudanar da aikin Hajjin bana.
Sakon da shafin Twitter na Haramain ya wallafa, ya nuna jami'an suna tarbar maniyyatan a yayin da suke bin tsarin kula da lafiya domin kauce wa kamuwa da cutar korona.
"Rukunin farko na mahajjata ya isa filin jirgin saman Sarki Abdulaziz na kasashen duniya da safiyar yau, inda jami'ai suka tarbe su cikin daukar tsarin kariya",a cewar sakon.
A watan Yuni ne mahukuntan Saudiyya suka ce mazauna kasar ne kadai - cikinsu har da 'yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta - za a bari su yi aikin Hajjin bana.
Mutum 10,000 ne kawai za su yi aikin hajjin bana amma mazauna Saudiyya kawai, ciki har da 'yan wasu kasashen da ke zama a can.
Sai dai a baya can mazauna Saudiyya suna yin aikin hajji ne kawai duk bayan shekara biyar.
Wani ma fafutuka a India ya zama mutum na farko dan asalin Afirka da ya yi nasara a zaben kasar.
Shantaram Siddi ya fito ne daga al'ummar Siddhi - jikokin 'yan Afirka da suka je India a matsayin 'yan kasuwa ko bayi daga karni na 17 zuwa bayansa. Yanzu akwai kusan mutum 50,000 da suka rage a cikin al'ummar.
An nada Shantaram Siddi a matsayin dan majalisar dokokin jihar Karnataka. Shi ne mutum na farko da ya kammala karatun Kwaleji daga al'ummarsu.
Ya ce zai ci gaba da fafutukar ganin kabilun India sun samu 'yanci.
Mr Siddi ya shaida wa shafin intanet na The Hindu cewa: "Ina ganin wani yana zolayata."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, AFP
Bincike ya gano cewa maganin da shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya yi ta yabawa yana mai cewa zai iya warkar da cutar korona ba ya maganin cutar a kasar.
Maganin Hydroxychloroquine ya zama wani abu da aka yi ta magana a kansa a farkon shekarar nan lokacin da aka yi fatan maganin na maleriya zai iya warkar da Covid-19.
Tun daga watan Mayu, gwamnatin Bolsonaro ta bai wa asibitoci shawarar su rika bai wa masu fama da cutar korona maganin Hydroxychloroquine. Shugaban kasar da kansa ya ce yana yana amfani da maganin bayan an tabbatar ya kamu da cutar korona a farkon watan Yuli.
Shi ma Shugaba Donald Trump ya ce maganin yana da amfani.
Sai dai bayan an yi gwaji a kan maganin a Jami'ar Oxford a watan Yuni, an gano cewa hydroxychloroquine ba ya aiki wajen magani korona abin da ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya ta dakatar da shi.

Asalin hoton, Reuters
Tsohon shugaban Tanzania Benjamin Mkapa, wanda ya mutu ranar Alhamis, ya jagoranci ƙasar na tsawon shekara 10 bayan da ta koma kan tafarkin mulkin dimokradiyya mai jam'iyyu masu yawa.
Ya gaji Ali Hassan Mwinyi wanda ya dawo da ƙasar kan tsarin tattalin arziki na jaro hujja.
Amma Mista Mkapa ne ya fara aiwatar da sauye-sauyen sakin mara da buɗe tattalin arzikin ƙasar ga masu zuba jari daga waje.
An kuma ce shi ne ya bunƙasa kuɗaɗen shiga da gwamnatin ƙasar ke samu, kuma ya tsuke aljihun gwamnati bayan buɗe ƙofofi ga masu zuba jari daga ƙasashen ƙetare.
Bankin duniya da Asusun Lamuni na duniya sun yi maraba da sauye-sauyen da ya riƙa gudanarwa, wanda yana cikin dalilan da suka soke wa ƙasar wasu basussuka da ake bin ta.
Amma shirin da ya ɗora ƙasar na sayar da kamfanoni da wasu hukumomin gwamnatin ƙasar ya sha suka daga ƴan ƙasar, kuma daga baya ya amince cewa ba a aiwatar da shirin yadda y akamata ba.
A watan Nuwambar bara ya wallafa littafin tarihin rayuwarsa da ya kira "My Life, My Purpose", wato "Rayuwata, Manufata" kuma ya yi nadamar kisan wasu masu zanga-zanga 22 da ƴan sanda suka yi a shekarar 2001 a tsibirin Pemba. Ya ce lamarin "zai kasance abin takaici da ya faru a lokacin shugabanci na."
Masu zanga-zangar sun fita titunan ƙasar ne domin nuna bacin ransu kan sakamakon zaben Zanzibar na shekara ta 2000 wanda a ganinsu an murɗe shi ne. Mista Mkapa ya ce "wannan asarar rayukan ya girgiza ni."
Ya miƙa mulki ga Jakaya Mrisho Kikwete in 2005.
Ya mutu ya bar matarsa Anna da ƴaƴansa maza biyu.
Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil Adama kuma wanda ya daɗe yana sukar gwamnatin Sudan ta Kudu ya tsere daga ƙasar zuwa Amurka.
Ya sanar a wani saƙon Tiwita cewa an tura wasu su kashe shi:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Gwamnatin ƙasar ta musanta zargin, kamar yadda wani mai taimaka wa shugaban ƙasar ya gaya wa Reuters.
"Wannan ƙazafi ne. Yana cikin ƙasar nan lokacin da shugaban ƙasar ya yafe ma sa kuma ya ƙyale shi ya bar ƙasar. Bai kamata ya riƙa alaƙanta dukkan matsalolin da yake fuskanta ga gwamnatin Sudan ta Kudu ba," in ji Ateny Wek Ateny, kakakin shugaban Sudan ta Kudu a wata hira da yayi da Reuters a birnin Juba.
An kama Mista Ajak a watan Yulin 2018 kuma an yanke ma sa hukuncin ɗauri a 2019.
Amma Shugaban Salva Kiir ya yi ma sa afuwa kuma an sako shi daga kurkuku a watan Janairu.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da soke babban taron jam'iyyar Republican na kasa da aka shirya gudanarwa a jihar Florida.
An tsara gudanar da taron ne a watan Agusta, sai dai da yake sanar da matakin yayin jawabi ga 'yan kasa game da cutar korona, Mr Trump ya ce halin annobar da ake ciki ba zai bayar da damar hada dubban mutane a wuri guda da sunan taro ba.
Shugaba Trump ya ce: "Lokacin yin taron bai yi ba, dole ne na kare Amurkawa, abin da nake yi kenan, kuma shi zan ci gaba da yi; shi ne aiki na."
A lokacin ne aka tsara jam'iyyarsa ta Republican za ta sanar da shi a matsayin dan takararta na shugaban kasa, amma ya ce a yanzu za a bijiro da wata sabuwar hanya ta yin hakan, har ma ya gabatarwa 'yan kasa jawabi gabanin zaben na watan Nuwamba.

Asalin hoton, Getty Images
An gano wani wawakeken kabari da ke dauke da gawarwakin mutane 23 a Sudan wanda aka haƙa a shekarun 1990.
An gano kabarin ne a Omdurman, birni mafi yawan jama'a a Sudan.
Ofishin mai gabatar da kara na Sudan ya ce an tono gawarwakin da zummar gudanar da bincike da kuma gano ko su wanene.
Ana kyautata zaton gawarwakin wasu sojoji ne da aka zartarwa hukuncin kisa bayan samun su da yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasar na wancan lokaci Omar Albashir, wanda ya kwaci mulki a wani juyin mulkin soja shekara guda kafin faruwar lamarin.
Shekaru 30 daga bisani dai shugaban ya rasa mulkin sa bayan wani gagarumin tutsu da yan kasa suka yi, kana yanzu haka kotun kasa da kasa dake birnin Heague na naimansa ruwan a jallo saboda zargin aikata laifukan yaki.

Asalin hoton, AFP
Tsohon shugaban kasar Tanzaniya, Benjamin Mkapa ya mutu, yana da shekara 81 a duniya.
Shugaban kasar mai ci John Magufuli ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, cewa marigayin wanda shi ne shugaba na uku da ya mulki Tanzania bayan samun yancin kai 1961, ya mutu a wani asibiti dake birnin Daressalam.
Babu wani karin bayani akan cutar da ta janyo ajalinsa.
Mista Mkapa, wanda ya yi mulkin gwamman shekaru bayan hawa mulki a 1995, ya jagoranci yukurin tabbatar da zaman lafiya sau da dama a Afrika.
Tuni shugaba John Magafuli ya sanar da zaman makoki na kwanaki bakwai domin jimamin mutuwarsa.

Asalin hoton, Reuters
Jihohi a Afirka ta Kudu za su sake rufe makarantu daga ranar Litinin a wani yunkuri na dakile yaduwar da cutar korona take yi.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce yana da muhimmanci a rufe makarantun domin kada su zama cibiyoyin yaduwar cutar korona a yayin da cutar ke yaduwa cikin sauri a kasar.
Dalibai masu 'yan shekaru da dama sun koma makarantun firamare da sakandare ranar 6 ga watan Yuli.
"Bayan an tattauna da masu ruwa da tsaki, majalisar zartarwa ta yanke shawarar bai wa dukkan makarantun gwamnati hutun mako hudu," in ji Shugaba Ramaphosa.
Ya ce za a tsawaita shekarar karatu ta bana zuwa shekarar 2021 sakamakon tsaikon da cutar korona ta kawo.
Sashen Hausa na BBC ne yake yi muku barka da warhaka. Kuna tare da Nasidi Adamu Yahaya a wannan safiya ta Juma'a.
Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.
Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.
Da fatan za ku bibiye mu a shafukan sada zumunta don tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a BBC Hausa.