Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Amitabh Bachchan ya ƙaryata warkewarsa daga korona

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Mustapha Musa Kaita

  1. Cutar korona ta yi kisa mafi girma a Afirka ta Kudu

    Afirka ta Kudu ta bayyana cewa cutar korona ta kashe mutum 572 a cikin kwana guda, wanda shi ne adadi mafi girma tun da cutar ta barke a kasar.

    Cutar ta kashe mutanen ne ranar Laraba, inda yanzu jimulla mutum 5,940 suka mutu sanadin cutar a Afirka ta Kudu.

    Kusan rabin mutanen da suka mutu suna zaune ne a lardin Western Cape.

    Sai dai galibin mutanen da suka kamu da cutar suna zaune a lardin Gauteng province, cibiyar kasuwanci kuma inda cutar ta fi kamari a kasar.

    Lardin na Western Cape shi ne na biyu a mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Afirka ta kudu.

    Kasar ta tabbatar cewa mutum 394,948 suka harbu da korona.

  2. Yadda mayakan Boko Haram suka yanka ma'aikatan agaji a Borno

    Masu ikirarin Jihadi da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun yanka ma'aikatan agajin da suka sace a arewa maso gabashin kasar a watan jiya.

    Kungiyoyin agaji na Action against Hunger da International Rescue Committee sun tabbatar cewa ma'aikatansu na cikin wadanda aka kashe. Mayakan sun sace ma'aikatan agajin ne a jihar Borno a watan Yuni.

    Wani bidiyo da aka fitar a watan jiya ya nuna ma'aikatan agajin da aka kama suna yin bayani.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dora alhakin kisan kan kungiyar Boko Haram. Shugaba Buhari ya sha alwashin hukunta makasan.

    Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an ga bayan kungiyar Boko Haram.

    Action Against Hunger ta ce ta yi matukar kaduwa da kisan da aka yi wa ma'aikatanta duk da rokon da ta yi na a sake su.

    Ita ma kungiyar The International Rescue Committee ta ce ta yi matukar bakin cikin samun labarin kashe mata ma'aikata.

    Mayakan boko Haram sun sha far wa ma'aikatan agaji kuma sau da dama suna kashe su.

  3. Barkanmu da safiya

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Muna fatan za ku bibye mu a shafukan sada zumunta don tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a BBC Hausa.