Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Amurka na tuhumar China kan leken asiri ta intanet kan riga-kafin Covid-19

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. Sai 'yan Najeriya sun so za a kawo ƙarshen rashin tsaro – Buratai

    Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa ta Najeriya, Janar Yusuf Tukur Buratai ya ce 'yan Najeriya za su iya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da kansu tun da "su ne suke zaune da 'yan bindigar".

    Buratai ya faɗi haka ne ranar Litinin jim kaɗan bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa, inda ya ce 'yan ƙasa ba sa ba su goyon baya ta hanyar ba su bayanai amma suna zargin jami'an tsaro da gazawa.

    Kafafen yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito shi yana cewa satar mutane da garkuwa da su, da fashi da ta'addanci za su zo ƙarshe ne kawai idan 'yan Najeriya sun ga dama.

    Kazalika Buratai ya ce kashi 99 cikin 100 na miyagun 'yan Najeriya.

    Buratai yana wannan batu ne yayin da aka kashe aƙalla mutum 192 cikin wata uku da suka gabata a Najeriya, a wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar.

  2. Buhari na ganawar sirri tare da Jonathan

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya soma wata ganawar sirri tare da tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan a fadarsa ta Aso rock da ke Abuja.

    Kawo yanzu babu cikakkun bayanai kan abin da shugabannin ke tattaunawa a kai.

    Bayanai sun ce Mr Jonathan ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 11 na safe kuma take ya wuce ofishin shugaba Buhari.

    A makon da ya wuce ne Jonathan ya jagoranci tawagar wakilai na musamman na kungiyar Ecowas zuwa kasar Mali domin sasanta rikicin siyasa a kasar.

  3. Shugabanni a Najeriya na ta'ziyyar Isma'ila Isa Funtua

    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta bayyana mutuwar Mallam Isma'ila Isa Funtua, makusancin Shugaba Buhari kuma tsohon shugaban ƙungiyar Masu Gidajen Jaridu a Najeriya a matsayin "abu mai ciwo".

    Shugaban ƙunigyar kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana hakan a cikin wani saƙon ta'aziyya da mai taimaka masa kan kafafen yaɗa labarai ya fitar a Jos, babban birnin jihar.

    Sanawarwar ta kuma bayyana rasuwar Mallam Isma'ila Isa a matsayin rashi ga ƙasa baki ɗaya.

    Shi ma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, kuma ya yi addu'ar Allah ya ji ƙansa.

    Kazalika Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya miƙa ta'aziyyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Katsina.

    Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabeamila ma ya ce bayyana marigayin a matsayin "wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga al'umma baki ɗaya".

  4. An fara yi wa Omar al-Bashir shari'a kan juyin mulkin da ya yi a 1989

    An fara yi wa Omar al-Bashir - tsohon shugaban Sudan - shari'a a babban birnin ƙasar Khartoum.

    Ana tuhumarsa ne game da juyin mulkin da ya ba shi damar hawa mulki a shekarar 1989.

    Idan aka samu tsohon shugaban da laifi - wanda ya mulki Sudan tsawon shekara 30 - za a iya yanke masa hukuncin kisa.

    Ita ma Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (International Criminal Court) ta zargi al-Bashir da aikata laifukan yaƙi da kisan ƙare-dangi a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.

    A shekarar da ta gabata ne aka tumɓuke shi daga kan mulki bayan an shafe watanni ana zanga-zangar neman mulkin dimokuraɗiyya.

  5. Minista ta harba bindiga a wurin rajistar zaɓe a Ghana

    Ministar Ayyuka na Musamman a Ghana, Hawa Koomson ta amsa cewa ta harba bindiga a wurin yin rajistar zaɓe a mazaɓarta ranar Litinin "domin ta kare kanta".

    Ta faɗa wa wata tashar talabijin mai suna Adom News cewa ta yi "harbin gargaɗi" ne saboda "babu 'yan sanda a wurin".

    Ministar ta ce ta je cibiyar rajistar ne saboda ta samu labarin ana kai wasu waɗanda ba 'yan mazaɓar ba suna yin rajistar.

    "Yan mintuna bayan haka ne kuma wasu mutane da ke ɗauke da makamai suka shiga wurin, inda suka yi lalata wasu babura, a cewar rahoton wata kafar yaɗa labarai a ƙasar.

    Hukumar zaɓen ta soke aikin yin rajistar a cibiyar.

    Za a gudanar da babban zaɓe a Ghana a watan Disamba, inda Shugaba Nana Akufo-Addo zai nemi wa'adi na biyu.

  6. Shugabannin ƙungiyar EU sun amince da tara yuro biliyan 750 don gyara tattalin arziƙinsu

    Jagororin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) sun amince da wani wani gagarumin shiri na tayar da komaɗar tattalin arzikinsu sakamakon durkushewar da cutar korona ta haifar.

    Ministocin na EU sun shafe kwana huɗu suna tattaunawa a Brussels, babban birnin ƙasar Belgium.

    Manyan jami'an sun sake komawa teburin tattaunawa ne domin rattaba hannu kan yarjejeniyarr samar da tallafin yuro biliyan 750 domin bunƙasa tattalin arzikisu.

    Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana lamarin a matsayin rana mai ɗumbin tarihi ga EU.

    Wakilan kuma suna ƙara tattaunawa kan samar da kasafin kudi na tsawon shekara bakwai masu zuwa.

  7. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyarmu a wannnan kafa, barkammu da safiyar Talata.

    Umar Mikail ke muku barka da shigowa wannan shafi da zai riƙa kawo labarai kai-tsaye game da abin da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Kazalika muna nan a shafukan zumunta; Facebook da Twitter da Instagram, inda za ku bayyana mana ra'ayoyinku.