Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Covid-19: An kwantar da surukar Amitabh, Aishwarya Rai a asibiti
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Rahoto kai-tsaye
Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita
Pogba zai sabunta zamansa a Man Utd, sai karshen Agusta Havertz zai koma Chelsea
Dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, 27, yana dab da amincewa da sabon kwantaragin shekara biyar a Manchester United.(Sun)
Bayer Leverkusen ta amince da matakin da dan wasan Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, ya dauka na komawa Chelsea amma tana so ta jinkirta tafiyarsa sai karshen watan Agusta.(Daily Star)
Manchester City na son dauko dan wasan Ajaxda Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27, a bazara.(Sports Illustrated)
Dan wasan Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29, yana da kwarin gwiwar kammala tafiya Liverpool bayan ya ki amincewa ya sabunta kwangilarsa a Bayern Munich.(Daily Mirror)
Karanta ci gaban labarin wasannin a nan:
Amurka za ta ƙwace gidan da Yahya Jammeh ya saya $3.5m
Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta sanar cewa tsohon Shugaban Gambia Yahya Jammeh ya yi amfani da kuɗaɗen al’ummar ƙasar da ya samu ta haramtacciyar hanya wajen sayen wani babban gida a wajen birnin Washington yayin da yake mulkin ƙasar.
Kamar yadda wasu takardu da aka bayyana suka tabbatar, Mista Jammeh ya sayi gidan a kan $3.5m shekara 10 da ta gabata.
Bayanai sun nuna ya sayi gidan ne a fakaice, ta hanyar amfani da wata gidauniya da matarsa Zineb Jammeh ta kafa.
Tsohon Shugaban ya mulki Gambia na tsawon shekara fiye da 20.
Ya tsere daga ƙasar bayan ya sha kaye a zaben shugaban ƙasar na 2017, kuma a yanzu yana zaune a ƙasar Equatorial Guinea ne.
Barkanmu da Juma'a
Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da Juma'a.
Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.
Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.