Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Covid-19: An kwantar da surukar Amitabh, Aishwarya Rai a asibiti

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye a wannan shafin, sai kuma gobe Asabar idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau.

    • Dubban ma'aikatan jinya a Ghana sun kamu da cutar korona
    • Yadda aka gudanar da addu'o'in neman zaman lafiya a Katsina
    • Mace ta zama firaiminista karon farko a Gabon
    • Ɗaliban Najeriya sun gaji da zaman gida
    • Firaiministan Mali ya nemi afuwa a kan kashe masu zanga-zanga
    • Shugaban Turkiyya ya caccaki Masar kan rikicin Libya
    • Sokoto za ta kashe biliyan 1.65 wurin gina cibiyar wasanni
    • Sojoji sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su a Benue
    • Ana zanga-zanga kan sauya dokokin Musulunci a Sudan

    Ku duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai..

  2. Yara biyar 'yan gida ɗaya sun mutu a Saudiyya

    Wasu yara biyar 'yan gida ɗaya sun mutu a Saudiyya.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Al Ahsa inda aka samu wani matashi da kuma ƙannensa mata huɗu a mace a gida.

    Wani kawun yaran ya shaida cewa lamarin ya faru ne bayan iyayen yaran sun je duba sabon gidan da za su tare.

    Bayan iyayen sun dawo, mahaifin ya ta ƙoƙarin buɗe ƙofar amma ba ta buɗe ba, wanda hakan ya sa ya ɓalle ta, ya kuma ga gawarwakin yaran.

    'Yan sanda sun ce ana nan ana gudanar da bincike kan mutuwar yaran.

  3. Covid-19: An kwantar da surukar Amitabh Bachchan a asibiti

    An kwantar da Aishwarya Rai Bachchana asibiti kwanaki kaɗan bayan ta kamu da cutar korona, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ANI a ƙasar ya ruwaito.

    Shaharariyyar 'yar wasan fim ɗin Indiyar ta killace kanta a gida tun bayan da ɗiyarta mai shekaru takwas ta kamu da cutar a ranar 12 ga watan Yuli.

    A makon da ya gabata ne dai aka kwantar da mijinta Abhishek da kuma surukinta Amitabh Bachchan a asibiti bayan sun kamu da korona.

    Rai Bachchan mai shekaru 46, na daga cikin shahararrun 'yan wasan fim ɗin Indiya.

    Ta taɓa yin nasara a gasar kyau ta duniya a 1994

  4. Masu zanga-zanga sun toshe bututun mai a Tunisia

    Masu zanga-zanga a kudancin Tunisia, sun toshe wani bututun mai yayin da suke kira kan ƙara haɓaka ci gaban yankin da ake haƙo mai a ƙasar.

    Bututun da suka toshe na ɗauke da kashi 50 cikin 100 na mai da ƙasar ke haƙowa.

    Ɗaruruwan mutane ne suka afka wurin samar da mai na El-Kamour da ke kudancin Tataouine, makonni biyu bayan masu zanga-zangar sun kafa sansani, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    A 2017, gwamnatin ƙasar ta yi alƙawarin saka maƙudan kuɗi domin kawo ci gaba a yankin, sai dai masu zanga-zangar sun ce ba a yi hakan ba.

  5. Japan na buƙatar a yi wa sojojin Amurka gwajin korona

    Ministan tsaro na Japan Taro Kono, ya buƙaci a rinƙa yin gwajin cutar korona ga sojojin Amurka masu zuwa ƙasar, bayan samun ɓarkewar cutar a tsibirin Okinawa.

    Amurka dai na yin gwajin cutar ne kaɗai ga waɗanda suka nuna alamominta, amma duk da haka ƙasar za ta duba wannan buƙatar ta Japan, in ji Mista Kono.

    Zuwa ranar Alhamis, sojoji 138 ne aka tabbatar da sun kamu da korona a sansanonin soji daban-daban da ke tsibirin Okinawa a Japan, kuma a nan ne akasarin sojojin Amurka da ke Japan ke zaune.

    Dangantaka tsakanin mazauna Okinawa da kuma sojojin Amurka ta fara tsami. Mazauna yankin sun shafe shekaru da dama suna kira da sojojin su bar tsibirin.

  6. An kama wani da ake zargi kan kisan Fahim Saleh

    'Yan sanda a birnin New York na Amurka sun kama wani wanda ake zargin da hadin bakinsa aka kashe Fahim Saleh.

    Mista Fahim kafin rasuwarsa shi ne mai kamfanin Gokada, wani kamfanin da ke samar da baburan haya a Najeriya.

    An gano gawar Fahim a wani gida da ke Manhattan na birnin.

    Mista Fahim ya kafa kamfanin Gokada 2018 - wanda ya kawo sauyi ta fuskar fasahar zamani ga harkar sufuri a babban birnin kasuwancin Najeriya wato Legas

    Jarin kamfanin ya kai dala miliyan 5.3 a lokacin da ya fara aiki cikin watan Yunin 2019.

    .

  7. Ana zanga-zanga kan sauya dokokin Musulunci a Sudan

    Gwamman mutane da ke goyon bayan tsarin Shari'ar Musulunci a Sudan sun gudanar da zanga-zanga a Khartoum babban birnin ƙasar.

    An gudanar da zanga-zangar ne sakamakon wasu sauye-sauye da aka yi kan tsarin ƙasar inda aka bayar da dama ga waɗanda ba Musulmai ba su sha barasa da kuma cire hukuncin riddah da kuma hana duka ga masu laifin zina ko sata a bainar jama'a.

    Masu zanga-zangar dai sun ci gaba da kwarmato kan cewa "ba za a iya shafe dokokin Allah ba," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    Ƙarƙashin sabbin dokokin, ba dole bane mata su nemi izini wurin mazajensu kafin su yi tafiya da yaransu.

    A yanzu dai an bayar da dama ga waɗanda ba Musulmai ba su sha barasa a ɓoye, sai dai haramcin shan barasar na nan har yanzu ga Musulmai a ƙasar

  8. Sojoji sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su a Benue

    Sojojin Najeriya sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su a Jihar Benue sannan suka kashe shugaban gungun masu garkuwar, a cewar wata sanarwa da hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar.

    Sanarwar ta ce dakarun runduna ta musamman ta Operation Whil Stroke ne suka yi nasarar ceto su a wani hari da suka kai a Ƙaramar Hukumar Logo ranar 16 ga watan Yuli.

    An sada dukkanin waɗanda aka ceto ɗin da iyalansu, a cewar sanarwar.

    Kazalika sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da kwanson harsashinta guda ɗaya.

  9. Sokoto za ta kashe biliyan 1.65 wurin gina cibiyar wasanni

    Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da ware naira biliyan 1.65 domin gina wata cibiyar wasanni da kuma wani rufaffen ɗakin wasa a babban birnin jihar.

    Wata sanarwa da Muhammad Bello, mai bai wa Gwamna Aminu Tambuwal shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar ranar Alhamis ta ce an amince da hakan ranar Laraba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.

    Bello ya ƙara da cewa za a kashe biliyan 1.2 na kuɗin da Majalisar Zartarwa ta Jihar ta sahhale wurin gina filin wasan, inda za a kashe miliyan 447 a ginin rufaffen ɗakin wasan.

    "Za a yi ayyukan guda biyu ne a Sokoto New City kuma kamfanin Qualitrend Global Solution aka bai wa kwangilarsa," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa: "Yayin da za a gina cibiyar wasannin cikin mako 44, za kuma a gina ɗakin wasan cikin mako 20."

    Sanarwar ta ce majalisar ta kuma amince da ƙirƙirar hukumar kula da ƙwayoyi da kuma kayan aikin lafiya a jihar.

  10. Za a yi wa Tolulope Arotile jana'izar ban-girma

    Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce za yi jana'izar ban-girma ga matukiyar jirgin saman yaki ta farko Tolulope Arotile wadda ta mutu sakamakon hatsarin mota a Kaduna da ke arewacin kasar.

    Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Ibukun Adaramola ya fautar ranar Juma'a ta ce za a yi mata jana'izar ranar Alhamis 23 ga watan Yuli a makabartar sojoji da ke Abuja babbar birnin kasar.

    Ranar Talata 14 ga watan nan ne rundunar sojin ta sanar da mutuwar Tolulope Arotile.

    An bayyana marigayiyar, wacce ƴar asalin jihar Kogi ce, da cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaki da ƴan bindiga masu fashin daji a jihar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina mata bisa sadaukarwar da ta yi wajen ci gaban kasar.

    Babban hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya ce mutuwar jami'ar babban rashi ga rundunar tare da jajantawa iyalanta a madadin dukkanin jami'an rundunar sojin sama na Najeriya.

  11. Shugaban Turkiyya ya caccaki Masar kan rikicin Libya

    Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdowan ya yi tir da sa hannun da kasar Masar ta yi a cikin rikicin da ake fama da shi a kasar Libiya.

    Ya ce goyon bayan da kasar Masar ke yi wa kwamandan `yan tawaye, Janar Khalifa Haftar ya saba wa ka`ida.

    Kasar Turkiyya dai ta ba da gudummuwar sojoji da za su tallafa wa bangaren da majalisar dinkin duniya take mara wa baya a kasar.

    Shugaba Erdowan dai ya yi wannan furucin ne bayan kasar Masar ta ce za ta tura sojojinta kasar Libiya.

    Shugaban Masar, Abdelfatah Al Sisi ya ikirarin cewa sojojin kasarsa za su iya sauya al`umara a Libiya cikin gaggawa.

  12. Firaiministan Mali ya nemi afuwa a kan kashe masu zanga-zanga

    Firaministan Mali ya nemi afuwa game da kisan da jami'an tsaro suka yi wa masu zanga-zanga kwanakin baya.

    A watan hira da France 24, Boubou Cissé ya ce an soma bincike kan batun amma ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Ibrahim Boubakar Keïta ya sauka daga kan mulki.

    Jami'an tsaro sun kashe akalla mutum 11 lokacin zanga-zangar adawa da gwamnati ranar Juma'ar da ta gabata kuma an ci gaba da ba-ta-kashi har karshen makon jiya.

    Gamayyar malaman addini, da 'yan siyasa da kungyiyoyin farar hula ta zargi Shugaba Keïta da hannu wajen tabarbarewar tattalin arziki da kuma gaza dakatar da hare-haren da masu ikirarin kishin addini suke yi.

    Wata tawagar kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas tana babban birnin kasar, Bamako, a yunkurin yin sulhu kan rikicin kasar.

  13. Matar Sarki ta zama mace mafi girman muƙami a 'yan sandan Najeriya

    Aisha Abubakar, mataimakiyar babban sufeto janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, ta ce tana matukar tsoron dan sanda lokacin tana yarinya.

    A tattaunawarta da BBC, mace ta biyu daga arewa mafi girman matsayi a rundunar 'yan sandan kasar, ta kara da cewa iyalinta sun karfafa mata gwiwar shiga aikin na dan sanda.

    A cewarta, babu abin da ke sanya ta dariya kamar 'ya'yanta.

  14. 'Yar Saudiyya ta zama gwarzuwar duniya a gasar FIFA 20 e-Football

    Najd Fahd - matashiyar da ake yi wa laƙabi da "'Yar Saudiyya" - ta zama gwarzuwar duniya bayan ta doke Cristina Batista Pereira da ci 8-0 a wasan ƙarshe na gasar ƙwallon ƙafar intanet ta 2020 ranar Alhamis.

    Gasar FIFA 20 e-Football World Championship, ita ce ta farko da cibiyar International Federation of University Sports ta shirya, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

    An buɗe gasar ne ranar 6 ga watan Yuli, inda mutum 44 suka fafata - maza 32 da mata 12 daga faɗin duniya.

    Najd Fahd, wadda ta wakilci jami'o'in Saudiyya, na cikin rukunin B tare da sauran mutum biyar daga ƙasashen duniya.

    Manufar haɗa gasar baya ga ƙarfafa shiga harkokin wasanni a irin wannan lokaci na yin nesa-nesa da juna, ita ce ta bai wa ɗaliban jami'o'i damar yin walwala ta hanyar yin mu'amala da junansu.

  15. 'Yadda masu kutsen intanet suka galabaita ni'

    Manyan attajiran duniya irinsu Jeff Bezos da Bill Gates da Elon Musk sun wayi gari da mummunan labarin yin kutse a shafukansu na sada zumunta musamman Twitter a ranar Laraba.

    Ba attajirai kaɗai ba kawai, har da taurari irinsu Kanye West da matarsa Kim Kardashian, da 'yan siyasa irinsu Barack Obama - tsohon shugaban Amurika.

    An wallafa saƙwannin jabu a shafukan mutanen da kutsen ya shafa, inda aka buƙaci mutane su aika gudunmawar dala 1,000 na kuɗin bitcoin da fatan samun ribar ninkin kuɗin.

    Bayan masu kutsen sun ƙwace iko da shafin Ismail Mudi na Facebook, sai suka fara tura wa abokansa buƙatar neman kuɗi da zummar harkar kasuwanci da ka iya ba su riba - kamar dai yadda aka yi wa waɗancan manyan attajiran.

    Ismail ya yi yunƙurin shiga shafin nasa Facebook amma abu ya gagara.

    "Kawai sai abokaina na kusa suka fara kirana suna tambaya; 'wai me abin da ka turo mana yake nufi ne?," in ji Ismail.

  16. Ko za ku iya tuna Zainab Aliyu?

    Zainab wata 'yar Najeriya ce da aka tsare a gidan yarin Saudiyya bisa kuskure kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

    A watan Afrilun shekarar 2019 ne aka sake ta bayan gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa da Saudiyya cewa wasu ne suka saka mata ƙwayoyin a cikin jaka.

    Yanzu dai Zainab ta kammala aikin hidimar ƙasa (NYSC) a wannan mako a Jihar Kano, jiharta ta asali.

  17. Ɗaliban Najeriya sun gaji da zaman gida

    Da alama ɗaliban Najeriya sun gaji da zama a gida bayan wata kusan huɗu da rufe makarantunsu a ƙasar saboda ɗakile yaɗuwar annobar cutar korona.

    Tun a watan Maris ne gwamnatin Najeriya ta bayara da sanarwar rufe dukkanin wasu harkoki a Abuja da jihohin Legas da Ogun da zummar hana yaɗuwar cutar da ɓulla ƙasar ranar 27 ga watan Fabarairu.

    An yi amfani da maudu'in #SAVENIGERIANSTUDENTS wato "a ceci ɗaliban Najeriya" sau fiye da 4,160 a yau a shafin Twitter, inda da dama suke kira da a buɗe makarantun tun da an buɗe sauran harkoki.

    Naheem ya ce: Abin kunya ne a buɗe harkokin zaɓe da na addini amma a ce har yanzu cibiyoyin gina ƙasa na kulle."

    Iheadinma ya ce: "An buɗe kasuwanni, to a buɗe makarantu ma."

  18. Mace ta zama firaiminista karon farko a Gabon

    An nada mace a mukamin firaministan Gabon a karon farko.

    Ranar Alhamis shugaban kasar ya nada Rose Christiane Ossouka Raponda domin tafiyar da gwamnatinsa.

    Matar mai shekara 56, 'yar jam'iyyar da ke mulkin kasar ce kuma a baya ta rike mukami ministar tsaron kasar.

    Raponda ta kware a fannin harkokin kudi kuma ta kammala digirinta ne a kan tsimi daga Cibiyar Gabonese Institute of Economy and Finance.

    Ba wannan ne karon farko da take zama ta daya a kan mukami ba.

    A shekarar 2014, ta zama mace ta farko da ta yi gwamna a Libreville, babban birnin kasar.

  19. Yadda aka gudanar da addu'o'in neman zaman lafiya a Katsina

    Masu ruwa da tsaki da suka hada da sarakuna, hakimai masu rike da kananan hukumomi da kuma malama sun gudanar da adduo'in neman zaman lfy karo na uku a birnin Katsina.

    An gudanar da adduo'in ne ranar Alhamis a dukkan fadin kananan hukumomin da ke jihar ta Katsina.

    Mahalarta wurin addu'ar sun yi karatun Al-Qur'ani da neman gafarar Allah kan matsalolin da suka addabi jihar ta Katsina.

    Rashin tsaron da ke addabar jihar ta Katsina da wasu jihohin da ke arewa maso yammacin kasar na ci gaba da tayar hanakulan jama'a.

    'Yan bindiga sun kashe daruruwan mutane a shekarar nan kawai, inda a wannan makon Uban kasar Batsari da ke jihar ta Katsina ya shaida wa BBC cewa akwai daruruwan mata da aka bari da marayu sakamakon hare-haren 'yan bindiga da suka kashe mazajensu.

  20. Dubban ma'aikatan jinya a Ghana sun kamu da cutar korona

    Ma'aikatan lafiya 2,065 a Ghana sun kamu da cutar korona, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta sanar.

    Babban shugaban ma'aikatar Patrick Kuma-Aboagye ya ce ma'aikatan jinya shida sun mutu, amma 1,870 cikin waɗanda suka kamun sun warke.

    Sauran na samun kulawa a cibiyoyin da hukumomin ƙasar suka tanadar.

    Alƙaluma daga yankin Greater Accra, wanda babban birnin ƙasar ke cikinsa, sun nuna a can yawancin ma'aikatan lafiyan da suka kamu suka fito.

    Hukumomin ƙasar sun ce suna ƙoƙarin samar da kayayyakin kariya domin rage yawan ma'aikatan jinyan da ke kamuwa da cutar.

    Ghana na da kimanin mutum 26,000 da suka kamu cutar korona kuma wasu mutum 136 sun rasa rayukansu.

    Ƙasar ta gudanar da gwaje-gwajen cutar ta korona 339,491 kan al'ummar kasar.