Goodluck Jonathan ya isa Mali don sasanta rikicin siyasa
Goodluck Jonathan - tsohon shugaban Najeriya - ya isa Bamako, babban birnin ƙasar Mali domin shiga tsakani a rikicin siyasar da ke ci gaba da ruruwa a ƙasar.
Ana sa ran zai tattauna da manyan masu ruwa da tsaki cikinsu har da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta da shugabannin jam'iyyun hamayya da ƙungiyoyin fararen hula da kuma malaman addini.
Mali ta faɗa cikin rikicin siyasa a makonnin baya-bayan nan, inda masu zanga-zanga suke kira ga Shugaba Keïta ya sauka daga mulki kan batutuwa da dama ciki har da zaben da ake ce-ce-ku-ce a kansa.
Masu zanga-zangar sun samu kwarin gwiwa ne musamman saboda gazawar gwamnati wajen shawo kan rikicin kabilanci da na addini da ke addabar kasar.
Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, Jean-Claude Kassi Brou ne ya sanar da nadin Mr Jonathan.