Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan Najeriya kusan 1,000 sun koma gida daga ƙasashen waje

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Sudan ta sanya dokar ta ɓaci a Darfur

    Hukumomi a Sudan sun sanya dokar ta ɓaci a yammacin yankin Darfur, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

    Wannan na zuwa ne daidai lokacin da rikici ke kara ƙamari tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro bayan shafe makonni ana zanga-zanga.

    Kungiyar kasashen Afrika - hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke Darfur ta ce ta aike da wata tawaga zuwa garin Kutum sakamakon rahotannin kona wani ofishin ‘yan sanda da kuma motocinsu.

    A ranar Lahadi, jami’an tsaro sun ta amfani da harsashi domin tarwatsa masu zanga-zanga, inda rahotanni suka ce an kashe mutum biyar ciki.

    An yi ta zanga-zangar lumana da zaman daɓaro a yankuna da yawa na lardin Darfur, tare da nuna bukatar korar jami’an da aka kama da cin hanci da rashawa da kuma janye sojoji daga birnin da kuma kauyuka.

  2. Buɗewa

    Buhari Muhammad Fagge da Nasidi Adamu Yahaya ne ke muku barka da safiyar wannan rana, tare da fatan kasancewa da ku a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni.

    Abin da ya shafi Najeriya ga Ghana da Sudan da sauran kasashen Afrika har da sauran sassan duniya.