Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi
Masu bibiyarmu nan muka kawo ƙarsehn rahotannin kai-tsaye na wannan rana.
Zai yi kyau ku kasance da mu gobe da safe domin sanin abubuwan da ke faruwa a duniya kai-tsaye.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Masu bibiyarmu nan muka kawo ƙarsehn rahotannin kai-tsaye na wannan rana.
Zai yi kyau ku kasance da mu gobe da safe domin sanin abubuwan da ke faruwa a duniya kai-tsaye.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya ta bayar da rahoton samun adadi mafi ƙaranci na waɗanda suke mutuwa kullum sakamakon cutar korona cikin mako biyu, inda mutum 20 suka rasu cikin awa 24 da suka gabata.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa an kuma samu mutum 2,852 da suka kamu da cutar, abin da ya sa jumillar adadin waɗanda suka kamu a ƙasar ya kai 235,111, a cewar ma'aikatar lafiya ranar Litinin.
Saudiyya na samun mutum 30 zuwa 56 da ke mutuwa a kullum tsawon mako biyu da suka gabata, kamar yadda bayanai daga ma'aikatar lafiya suka nuna.
Yanzu haka jumillar mutanen da suka mutu sakamakon cutar sun kai 2,243 a Saudiyya.
A gefe guda kuma, adadin waɗanda suka warke daga cutar ya kai 169,842 bayan an samu ƙarin 2,704 da suka warke, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar, Dr. Muhammad Al-Abdel Ali.
Shugaban rundunar sojan Somalia ya tsallake rijiya da baya bayan wani harin bam da aka kai wa rukunin motocinsa a babban birnin ƙasar, Mogadishu.
Wani ɗan ƙunar bakin wake ya tayar da bam ɗin da yake ɗauke da shi bayan masu tsaron lafiyar babban hafsan sojan sun buɗe masa wuta yayin da ya yi yunƙurin zuwa kusa da su.
Lamarin ya faru ne a kusa da sansanin sojoji na Gordon ranar Litinin kuma an yaɗa hotunan wurin da abin ya faru a shafukan sada zumunta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Janar Odawa Yusuf yana dawowa ne daga hedikwatar tsaro da ke Ma'aikatar Tsaro a birnin Mogadishu lokacin da aka kai harin.
Sai dai ya tsallake ba tare da jin rauni ba.
Zuwa yanzu babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin amma ƙungiyar al-Shabab mai ikirarin jihadi ta sha harar jami'an gwamnati.
Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Katsina da ke area maso yammacin Najeriya da aka kafa ya fara gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa gwamnatin jihar na almubazzaranci da maƙudan kuɗaɗen da suka kai naira biliyan 52.
Waɗansu kungiyoyin farar hula ne suka buƙaci majalisar da ta gudanar da binciken bayan wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Mahdi Shehu ya bijiro da zargin.
Hon Abduljalal Runka, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya shaida wa BBC cewa sun shiga binciken ne da zummar hukunta gwamnatin idan an same ta da laifi ko kuma hukunta Alhaji Mahdi Shehu idan ƙazafi ya yi mata.

Asalin hoton, Getty Images
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Ibadan babban birnin Jihar Oyo a kudancin Najeriya ta yanke wa wani mutum da ya yi sojan gona a matsayin jami'in hukumar DSS hukuncin shekara 12 a gidan yari.
Daga cikin laifukan da aka zargi Ademola Lawal da aikatawa akwai damfarar kuɗi naira miliyan 1.85 da sunan wani jami'in hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.
Da take bayyana hukuncin, Mai Shari'a Patricia Ajoku ta ɗaure Ademola Lawal bisa hujjojin da aka gabatar mata sannan kuma mai laifin ya amsa abubuwan da ake zarginsa da su, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.
"Na aminta cewa mai laifin ya nuna nadama da kuma zummar zai sauya halinsa ta hanyar amfanar da al'umma," in ji Patricia Ajoku.
"Duk da haka, an yanke wa Lawal hukuncin shekara biyu kan kowanne laifi guda shida da ake zarginsa da su domin ya zama darasi ga sauran jama'a."
Sai dai mai shari'ar ta ce zai yi zaman gidan yarin ne a lokaci guda.

Asalin hoton, @FAAN_Official
Daga yanzu matafiya a Najeriya za su riƙa isa filayen jirgin sama awa ɗaya da rabi kafin lokacin tashin jirginsu, a cewar Hadi Sirika Ministan Sufurin Jiragen Sama na ƙasar.
Ministan ya bayyana haka ne ranar Litinin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Gwamnatin Najeriya ta saka wasu sharuɗa ga kamfanonin jirage da ma matafiya a yunƙurinta na daƙile yaɗuwar annobar cutar korona.
A ranar 8 ga watan Yuli ne jiragen da ke zirga-zirgar cikin gida suka ci gaba da aiki bayan wata uku da aka shafe ba tare da aiki ba saboda annobar.
"Ni da abokan aikina mun sake duba tsarin yin tafiya a filayen jirgin sama kuma ina mai farin cikin shaida muku cewa daga yanzu matafiya za su riƙa isa filin jirgi awa ɗaya da rabi kafin lokacin tashin jirginsu," in ji Hadi Sirika.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Annobar korona "za ta ta'azzara matuƙa" idan wasu gwamnatoci ba su ɗauki ƙwararan matakai ba domin daƙile yaɗuwar cutar, a cewar wani gargaɗi da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi.
Shugaban hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce "muna ci gaba da ganin ƙaruwar masu kamuwa da cutar a ƙasashen da ba a ɗauki matakan kare yaɗuwarta ba".
"Bari ku ji, ƙasashe da yawa ba su ɗauki hanyar gyara ba," Dr Tedros ya faɗa a wurin wani taro da aka gudanar a birnin Geneva ranar Litinin.
"Cutar ta zama abokiyar gabar al'umma lamba ɗaya, sai dai ayyukan wasu gwamnatoci ba su nuna hakan ba."

Asalin hoton, AFP
Kamfanin Google ya bayyana shirinsa na zuba jarin dala biliyan 10 a Indiya cikin shekara biyar zuwa bakwai masu zuwa.
Shugaban kamfanin wanda haifaffen Indiya ne mai suna Sundar Pichai ya ce matakin na nuna karfin gwuiwar da Google ke da shi kan tattalin arzikin Indiya ta bangaren fasahar zamani.
Ya kuma ce Google na son nunka yawan masu amfani da intanet a kasar zuwa mutum biliyan daya a fannukan kasuwancin intanet da ilimi da kiwon lafiya.
Facebook da Amazon na cikin kishiyoyin Google da tuni suka narka biliyoyin daloli cikin tattalin arzikin Indiya a bangaren fasahar zamani.
A farkon wannan watan gwamnatin Indiya ta haramta amfani da wasu manhajojin China ciki har da na Tik Tok mai matukar farin jini saboda damuwar da ta ke da ita cewa ana iya yin kutse da su..

Asalin hoton, AMINU ADO BAYERO/INSTAGRAM
A naɗe-naɗen farko da ya yi tun bayan zamansa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya naɗa ɗan uwansa Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano, kuma Ɗan Majsalisar Sarki.
A baya dai, Sanusi Lamido Ado Bayero ne ke riƙe da muƙamin Ciroman Kano, wanda tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya sauke shi saboda ya ƙi yi masa mubaya'a bayan zamansa sarkin Kano.
Hakan ta sa Sarki Sanusi ya maye gurbinsa da Nasiru Ado Bayero a matsayin Ciroman Kano, wanda yanzu shi ne Sarkin Bichi.
Tuni Sunusi Ado Bayero ya je ya yi mubaya'a ga Sarkin Kano Aminu Ado, wanda hakan kamar wata sanarwa ce ga sarkin cewa ya dawo gida da zama.
Wata sanarwa da Alhaji Sarki Waziri, Ɗan Rimin Kano ya aike wa Sakataren Gwamnatin Kano ta kuma tabbatar da naɗa Aminu Babba Ɗan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba, wanda Marigayi Sarki Ado Bayero ya sauke daga muƙamin Sarkin Dawaki Mai Tuta shekara 16 da suka gabata.

Asalin hoton, Reuters/Getty Images
China ta sanar da saka takunkumin ramuwar gayya akan manyan yan siyasar Amurka da ke kunfan banki kan cewa ta tauye hakkin bil'adama a Xianjiang.
Sanata Marco Rubio da Ted Cruz da kuma wasu yan majalisa na daga cikin wadanda matakin ya shafa.
To sai dai ma'aikatar harkokin wajen China bata fito ta cikakken bayani ba kan abinda takunkumin ya kunsa.
A mako da ya gabata ne gwamnatin Amurka ta sanar da hana visa da kuma karbe kadarorin wasu yan jami'an China da take zargi da hannu a muzgunawa Musulmin Uighur da ke yankin Xianjiang.

Asalin hoton, AFP
Tsohon firaiministan Somaliya Hassan Abshir Farah ya mutu yana da shekara 75 a Turkiyya.
Ya rike matsayin ne a tsakanin 2001 da 2003 karkashin gwamnatin rikon kwarya shugaba Abdiqasim Salat Hassan.
Ya kuma rike matsayin magajin garin babban birnin kasar Mogadishu a farkon shekarun 1970.
Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo ne ya sanar da mutuwarsa, yana cewa Mista Farah "ya matukar taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban gwamnati da kuma bunkasa Somaliya".
Gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai zagoranci jana'izarsa, sai dai ba a sanya lokacin hakan ba.

Asalin hoton, Amnesty
Kungiyar Amnesty International ta ce gwamnatocin kasashen duniya ne ke da alhakin mutuwar ma'aikatan lafiya da ke aiki lokacin annobar korona wadanda aka gaza samar musu da kayayyakin kariya.
Hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da kiungiyar ta saki a ranar Litinin wanda ke kunshe da bayanan ma'aikatan lafiya a fadin duniya na abin da suka shaida.
Rahoton ya ce daga bayanan da suke a hannu yanzu akwai sama da ma'aikatan lafiya 3,000 da suka mutu a fadin duniya sakamakon annobar ta korona - wanda wannan wani adadi ne mai girma da ba za a dauke ido akai ba.
Kungiyar ta Amnesty ta tattara bayanai inda ma'aikatan lafiyar da suka nuna damuwa kan halin da suke ciki kan cutar, aka yi musu barazanar kama su da kora daga aiki da dai sauransu.
Yayin da cutar Covid din ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, muna shawartar gwamnatoci da su rika daukar rayuwar ma'aikatan lafiya da mahimmanci.
Kasashen kuma da cutar ba ta yi ƙamari ba su dauki matakan da suka dace na kaucewa maimaita irin wannan kuskure.

Asalin hoton, AFP
An kara tsawaita dokar hana zirga-zirga a birnin Tangier da ke arewacin Morocco bayan rahoton ƙara samun masu dauke da cutar.
Tun da farko an sanya dokoki a wani mataki na kare yaduwar cutar a wasu sassan birnin, amma yanzu a faɗaɗata zuwa sauran sassan kasar kuma za ta fara aiki daga tsakiyar ranar Litinin, in ji kamfanin dillancin labarai na Morocco.
An hana tafiye-tafiye da kuma dakatar da ayyukan motocin haya, yayin da aka shaida wa mutane kada su bar gidajensu sai dai in da bukata ta musamman.
Tun a watan Maris Morocco ta fara sanya dokar hana zirga-zirga kuma ta fara sassauta ta ne a 'yan makonnin baya.
Akwai mutum sama da 15,000 da aka ruwaito sun kamu da cutar a kasar kuma wasu 253 sun mutu tun farkon bullar cutar.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ma'aikatan lafiya 16 a Sudan ta Kudu sun ajiye ayyukansu bayan an gwada su sun kamu da cutar korona, kamar yadda ministan lafiya na kasar ya bayyana.
Ma'aikata takwas ne suka bar aiki a makon jiya saboda matsin lamba daga iyalansu, wadanda suka nuna damuwa kan za su iya shigar musu da annobar gida wadda kuma za ta iya mamaye gidan maki daya, in ji ministan.
Wasu kuma sun ajiye aikin ne ba tare da sanarwa ba ganin yadda marasa lafiya ke mutuwa sakamakon cutar.
Rahotanni sun ce hudu ma'aikatan tsafta ne sauran hudun kuma na jinya ne.

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Mali, da kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar tarayyar Afirka da kuma kungiyar kasashen yammacin Afira ta ECOWAS, duka sun yi soki hukumomin Mali saboda amfani da kazamin karfi wajen tunkarar masu zanga-zangar.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kungiyoyin sun sun kuma yi Allah wadai da barnata kadarorin gwamnati da masu zanga-zangar suka yi, kana suka yi kira ga dukkan bangaoin da su yi taka-tsantsan tare da mayar da hankali ga afarkin tattaunawar sulhu.
Suna kuma yi kira ga gwamnatin Mali da ta saki shuwagabannin ‘yan adawa da aka kama a karshen mako.
Hukumoin Mali dai sun ce mutane akalla hudu aka kashe ranar Juma’a, amma ‘yan adawa sun ce ‘yan sanda sun kashe karin mutune takwas a ranar Asabar a lokacin zanga-zangar.
Masu zanga-zamgar dai na bukatar shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ne ya sauka daga mulki saboda abin da suka kira gazawara gwamnatinsa wajen kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe shekaru ana fuskanta daga mayaka masu alaka da Al-qaeda da kuma IS, sannan da matsalar tattalin arziki da kuma takaddama kan zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a watan Maris.
‘Yan adawa sun yi fatali da matakan sassauci da gwamnati ta dauka, da kuma ta yi da ta masu ciki har da kiran kafa gwamnatin hada kan kasa da kuma rusa kotun tsarin mulkin kasar wacce ke a tsakiyar rikicin siyasar bayan da ta sauya sakamkon zaben.
‘Yan adawar dai na cewa ba za ta sabu ba, lallai sai shugaban ya yi murabus.
Ana dai fargabar rikicin na siyasa ka iya kafar ungulu ga yunkurin da kungiyoyi da kasashen duniya da na Afirka ke yin a yaki da kungoiyoyin masu dauke da makamai a yankin.
Majalisar Dinkin Duniya dai na da sojojin kiyaye zaman lafiya fiye da dubu goma sha uku a Mali.

Asalin hoton, AFP
Zindzi Mandela, ƴar Nelson Mandela da Winnie Madikizela-Mandela, wadanda suka sadaukar da rayukansu domin yaƙar tsarin nuna bambancin launin fata ta mutu kamar yadda tashar SABC ta gwamnatin Afirka ta Kudu ta ruwaito.
Ta mutu a birnin Johannesburg ranar Litinin tana da shekara 59. Wani ɗan uwanta ya tabbatar da mutuwarta, in ji tashar ta SABC.
Ita ce jakadiyar Afirka ta Kudu a Denmark a lokacin da ta mutu, amma ba a bayyana abin da yayi sanadin mutuwarta ba.

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan na duba yiwuwar dauko dan wasan Chelsea da Faransa N'Golo Kante a bazara inda The Blues ke shirye domin jin tayin da za a yi kan dan wasan mai shekara 29.(Gazzetta dello Sport, via Metro)
Zenit St Petersburg ta bayyana sha'awar dauko dan wasanLiverpoolda Croatia Dejan Lovren, mai shekara 31.(Liverpool Echo)
AC Milan na son dauko dan wasan Real Madrid da Serbia Luka Jovic, mai shekara 22, wanda Leicester City da Arsenal suke zawarci.(Calciomercato, via Leicester Mercury)
Kai Havertz yana son barin Bayer Leverkusen saboda sun gaza samun gurbin gasar Zakarun Turai don haka akwai bukatar Chelsea ta nuna wa dan wasan na Jamus mai shekara 21 cewa za ta iya samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai kafin ya amince ya koma can.(Bild).
'Yan majalisar dokokin Madagascar biyu, daya dan majalisar dattawa daya kuma na majalisar wakilai, sun mutu sanadin cutar korona , in ji kafofin watsa labarai wadannan suka ambato Shugaba Andry Rajoelina yana bayyana hakan ranar Lahadi.
Mr Rajoelina ya kara da cewa 'yan majalisar wakilai 11 da na dattawa 14 sun kamu da cutar, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.
A makon jiya ne gwamnati ta sanya dokar kulle a daya daga cikin lardunanta, wanda ya hada da babban birnin kasar, Antananarivo, sakamakon karuwar cutar.
Hukumomi sun ce an sanya dokar kullen ce domin dakile yaduwar cutar ta korona.
An tabbatar mutum 4,578 sun kamu da cutar, yayin da ta yi ajalin mutum 34 tun lokacin da ta bulla a watan Maris, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya..
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta ceto wata Ba'amurkiya wadda 'yan damfara suka ajiye a wani otal da ke birnin Lagos fiye da shekara daya a wani yanayi na damfara bayan ta fada tarkon 'soyayya'.
Sun ce matar wacce ta yi ritaya daga aikin gwamnati ta niki gari zuwa Najeriya a watan Fabrairun 2019 domin ganawa da saurayinta mai shekara 34 wanda ya hilace ta ta hanyar Facebook.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A watan Mayun 2019 aka daura mata aure da mutumin.
'Yan sanda sun zarge shi da kwace mabudin asusun bankinta da katinta na ATM inda ya sace $48,000.
'Yan sandan sun kara da cewa sun samu bayanin ne daga wurin wasu masu kwarmata bayanai inda suka yi amfani da su wajen isa gare ta.
Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai farin jini.
Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana ta Litinin domin sanin halin da duniya take ciki.
Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.
A ko da yaushe za ku iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.