Gwamnatin Gombe za ta shuka sama da bishiyoyi miliyan ɗaya a 2020

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan za mu dasa aya a labaran da muke kawo muku kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • A rika bayar da riga-kafin korona ga waɗanda suka fi bukata - Bill Gates
    • Mutum biyar sun mutu a wani rikici a Afrika Ta Kudu
    • Ba za mu iya kulle harkokin kasuwancinmu ba - Rouhani
    • Korona ta kashe mutum 70,000 a Brazil
    • Tsohon shugaban BBC na sashen Hindi ya mutu
    • Za a bayar da tallafin miliyan $408 a Dubai
    • Pantami ya kai wa El-Rufai ziyara a Kaduna
    • Gwamnatin Mali na neman yin sulhu da masu zanga-zanga

    Ku duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai..

  2. Shirin amsoshin takardunku na wannan makon

    Bayanan sautiShirin Amsoshin takardunku 11/07/2020
  3. Jumullar mutum 44,798 korona ta kashe a Birtaniya

    Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa jumullar mutum 44,798 cutar korona ta kashe a halin yanzu a faɗin ƙasar.

    Hakan ya biyo bayan sabbin mutum 148 da aka sanar da mutuwar su a ranar Asabar bayan sun sha fama da wannan cuta.

    Mutum 288,953 suka kamu da cutar a faɗin ƙasar bayan mutum 820 an tabbatar da sun kamu da cutar a sanarwar da aka fitar a yau.

  4. Gwamnatin Mali na neman yin sulhu da masu zanga-zanga

    ..

    Asalin hoton, Boubou Cissé

    Firaiministan Mali Boubou Cisse, ya ce kofa a buɗe take don tattaunawa da yan adawa, a wani yunƙuri na kawo karshen rikici a kasar.

    Boubou Cisse ya ce akwai ma yiwuwar kafa gwamnatin haɗin gwuiwa.

    To amma a ɗayan ɓangaren, mai magana da yawun masu zanga-zanga ya ce an kama shugabanninsu biyu a Bamako.

    A ranar Juma'a ne dubbai suka bazama kan tituna inda suke kira ga shugaba Boubakar Keita da ya yi murabus, saboda taɓarɓarewar tsaro da kuma tattalin arziki.

    Rikicin ya dakatar da ayyuka a majalisa tare da rufe tashar gidan talabijin na kasa.

  5. Labarai da dumi-dumi, Amitabh Bachchan ya kamu da cutar korona

    GARETH CATTERMOLE / GETTY IMAGES

    Asalin hoton, GARETH CATTERMOLE / GETTY IMAGES

    Shahararren ɗan wasan fim ɗin Indiya Amitabh Bachchan ya kamu da cutar korona.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Bachchan ya bayyana cewa tuni aka tafi da shi asibiti kuma tuni 'yan uwansa da iyalansa da ma'aikatansa suka yi gwajin cutar.

    Ya kuma yi kira ga waɗanda suka yi mu'amula da shi kwanaki 10 da suka gabata da su yi gwajin cutar ta korona.

    Amitabh Bachchan ya shahara dai a wasan fim ɗin Bollywood, kuma ya yi fina-finai da dama da suka ratsa zukatan masu kallo.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Gwamnatin Gombe za ta shuka sama da bishiyoyi miliyan ɗaya a 2020

    Gombe State Government

    Asalin hoton, Gombe State Government

    Gwamnatin jihar Gombe ta ƙaddamar da aikinta na shuka bishiyoyi karo na biyu a yankin Wajari da ke ƙaramar hukumar Yalmatu/Deba a jihar.

    Gwamnan jihar ta Gombe Inuwa Yahaya ya ce ana shuka bishiyoyin ne domin kare muhallin jihar wanda rayuwar jama'a ta dogara a kai.

    A cewarsa, shuka bishiyoyin zai taimaka wajen daƙile kwararowar hamada da gyara ƙasa da kuma dawo da inganci da martabar ƙasar noman da ke jihar.

    Gwamnatin na da niyyar shuka akalla bishiyoyi miliyan ɗaya da dubu 200 a shekarar bana.

    Gwamnatin jihar ta kuma ce za a fara shuka bishiyoyin a makarantu da asibitoci da tituna da wuraren aiki.

    Gombe State Government

    Asalin hoton, Gombe State Government

    Gombe State Government

    Asalin hoton, Gombe State Government

  7. Pantami ya kai wa El-Rufai ziyara a Kaduna

    ..

    Asalin hoton, @FMoCDENigeria

    ..

    Asalin hoton, @FMoCDENigeria

    ..

    Asalin hoton, @FMoCDENigeria

  8. Za a bayar da tallafin miliyan $408 a Dubai

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Birnin Dubai da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya bayyana wani sabon tsarin da ya fito da shi na tallafi ga 'yan ƙasar.

    A wata sanarwa da yarima mai jiran gado na ƙasar wato Hamdan Bin Mohammed Al-Maktoum ya fitar a shafinsa na Twitter, ya ce tallafin zai taimaka wa masana'antu da kuma jama'ar ƙasar ta hanyar yi musu sassauci a ɓangarorin haraji da kuɗin haya da sassauci ga masu tara da sauran ɓangarori..

    Tallafin ya kai na kimanin dirham biliyan 1.5, kusan dalar Amurka miliyan 408 kenan a cewarsa.

    Wannan ne karo na uku da ƙasar ke fitar da irin wannan garaɓasar a lokacin korona.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Sojin Amurka a Japan sun kamu da korona

    Gwamnan tsibirin Okinawa da ke Japan ya nemi Amurka ta bashi bahasi kan gwamman sojojinta da suka kamu da cutar korona a sansanin sojin ruwanta.

    Denny Tamaki ya ce yana da kokonto game da matakan kariyar da ake dauka.

    Ya ce Amurka ba ta bayyana ainihin adadin mutanen da suka kamu da cutar ba daga cikin jami'anta.

    Rahotannin cikin gida sun bayyana cewa akalla akwai mutum 60 daga cikin sojojin da suka kamu da wannan cuta.

  10. Tsohon shugaban BBC na sashen Hindi ya mutu

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban sashen Hindi da Tamil na BBC Kailash Budhwar ya mutu yana da shekara 88.

    Mista Budhwar shi ne shugaba na farko na bangaren Asiya lokacin da aka naɗa shi a 1979.

    Ya fara wasu shirye-shirye da yaren Indiya wanda a wancan lokacin labaran sauya fassara su kawai ake daga na turanci.

    Kafin ya fara aiki da BBC a 1969, Mista Budhwar ya yi aiki a matsayin malamin makaranta.

    Ya kuma yi aiki da wani fitaccen kamfanin shirya fina-finai na kasar Indya.

  11. Ministan shari'ar Jamhuriyar Congo ya ajiye muƙaminsa

    BBC
    Bayanan hoto, Rikicin siyasa na kara dabaibaye gwamnatin DRC

    Ministan Shari'a na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya yi murabus daga mukaminsa lokacin da ake tsaka da rikin kan wata doka ma masu suka suka ce za ta rage karfin ikon bangaren shari'a.

    Celestin Tunda bai bayyana dalilinsa na ajiye aikin ba, amma ya samu kansa a tsaka mai wuya na rikicin da ke faruwa tsakanin shugaban kasar Felix Tshisekedi da kuma wanda ya gabace shi tsohon shugaban kasar Joseph Kabila.

    Duk da ya bar kan mulki a zaben da ya gabata, Mista Kabila na ci gaba da jan akalar kasar saboda jam'iyyarsa ce ke da 'yan majalisa mafiya rinjaye da yawan mukamai a gwamnatin kasar.

    Magoya bayan shugaba Tshisekedi sun ta fitowa zanga-zangar rashin amincewa da sauye sauyen da Mista Kabila ke iza wutar kawo su.

  12. Kananan hukumomi 102 ne 'ke cikin haɗarin ambaliyar ruwa a Najeriya'

    NEMA

    Asalin hoton, NEMA

    Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce kananan hukumomi 102 ne ke fuskantar hadarin ambaliyar ruwa a jihohi 28.

    Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na tuwita hukumar ta ce an bayyana wannan hasashe ne lokacin wani taro na shiryawa tunkarar hadarin ambaliyar ruwa da za a iya fuskanta a 2020.

    Shugaban hukumar AVM Muhammadu Mhuammedya ce an gudanar da taron ne domin nemo bakin zare yadda za a iya rage radadin wannan annoba da kuma matakan da za a iya dauka gabanin saukarta.

    Kananan hukumomi 275 ne ke fuskantar madaidaicin hadarin ambaliar ruwan ciki har da wasu a babban birnin tarayyar Abuja.

    Kazalika wasu kananan hukumomi 379 sune ba sa fuskantar hadarin annobar sosai, in ji Muhammad.

    Yayin taron an gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ba da agajin gaggawa da hukumar lura da yanayi ta kasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Korona ta kashe mutum 70,000 a Brazil

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Wadanda korona ta kashe a Brazil sun haura 70,000, in ji hukumomin kasar.

    Mutum 1,200 ne suka rasa rayukansu cikin awa 24 a kasar.

    Brazil ce kasa ta biyu da cutar korona ta fi yin kisa a cikinta a duniya, kwararru na cewa babu wata alama da ke nuna raguwar cutar a kasar.

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa har yanzu cutar ba ta kai makurarta ba a Brazil har sai nan da watan gobe.

    Tuni dai wasu jihohi irinsu São Paulo da Rio suka fara bude shaguna da sauran harkokin kasuwancinsu.

    A farkon wannan makon ne shugaban kasar Jair Bolsonaro ya sanar da cewa cutar ta kama shi amma a ranar juma'a ya ce ya dan samu sauki.

  14. Ba za mu iya kulle harkokin kasuwancinmu ba - Rouhani

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi gargadin cewa kasar ba za ta iya rufe harkokin kasuwancinta ba yayin da ake tsaka da fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar korona.

    Mutum 221 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar a ranar Alhamis, rahoton kwana daya kenan da aka samu na kasar. Sama da mutum 12,400 ne suka mutu a kasar tun lokacin da cutar ta bulla a kasar.

    Ya yin wani taro da ya gabata ta intanet, Rouhani ya ce kasar za ta "ci gaba da harkokin kasuwanci na yau da kullum da kuma sauran mu'amaloli amma tare da tabbatar da bin dokokin mahukunta a fannin lafiya."

    An janye dokar kulle a kasar daga watan Afirilu. Ministan lafiya na kasar Said Namaki ya ce sake buɗe harkokin kasuwanci a kasar wani mataki ne na farfado da tattalin arzikin da ke neman durkushewa".

    Takunkumin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa Iran na daga cikin abubuwan da suka kara ta'azzara cutar a kasar.

  15. Mutum biyar sun mutu a wani rikici a Afrika Ta Kudu

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a Afrika Ta Kutu sun ce an kashe mutane biyar yayin wata garkuwa da aka yi da wasu mutane a wata coci da ke wajen birnin Johannesburg.

    Masu shiga tsakanin sun halarci cocin ta International Pentecostal Holiness da ke Zuurbekom a yammacin Rand.

    Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa wani rikicin shugabanci ne ya barke a cocin.

    'Yan sanda sun ce sun kama mutum talatin da ake zargi tare da kwace gwamman makamai.

    Hotunan da aka nuna sun hadar da na bindigogi da kuma wasu sauran makamai.

  16. Zanga-zanga ta barke a Rasha

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Rahotanni daga Rasha na cewa dubban mutane ne suka shiga wata zanga-zana kin jinin kama gwamnan yakin Khabarovsk da aka yi.

    A ranar Juma'a ne wata kotu a Moscow ta bayar da umarnin tsare Sergei Furgal gabanin sauraren shari'ar da zai fuskanta ta kisan kai.

    Ana zarginsa da bayar da umarnin kashe wasu mutane 'yan kasuwa shekara 15 baya.

    Mista Furgal ya zama gwamnan yankin Khabarovsk ne shakara biyu da ta gabata, bayan nasarar da ya samu kan dan takarar jam'iyyar shugaba Putin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. A rika bayar da riga-kafin korona ga waɗanda suka fi bukata - Bill Gates

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitaccen mai ba da taimakon nan kuma mai kamfanin Microsoft Bill Gates ya yi kira da a rika bayar da riga-kafin cutar korona ga kasashe da kuma mutanen da suka fi bukatarta maimakon wadanda suka fi yawan kudi.

    Da yake bayani a wani taro da ya gudana ta intanet ya ce, " idan muka kyale magunguna da kuma riga-kafin suka ta fi zuwa ga wadanda suka fi yawan kudi, maimakon wadanda suka fi bukatarta, to za mu yi dogon jira. mai yawa na rashin adalaci ga wadanda suka mutu sakamakon annobar."

    Ana dai ta ci gaba da bincike kan wannan annoba da ta gallabi duniya baki daya kuma kasashe da yawa na ta yin gwaji domin dacewa.

    Amurka ta sanya kudade masu yawa kan binciken, kuma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wasu manyan jami'an Amurkan na cewa idan an samu maganin sai amurkawa sun gama morar shi kan ya tsallaka ko ina.

  18. An samu adadi mafi yawa na masu korona a rana daya a Amurka

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu adadi mafi yawa na waɗanda suka kamu da cutar korona a Amurka, inda sama da mutum 63,643 aka tabbatar sun kamu da cutar a ranar Juma'a.

    A dai ranar Juma'ar mutum 774 ne suka mutu sakamakon cutar in ji bayanan jami'ar Johns Hopkins da ke tattara bayanai kan cutar.

    Sama da mutum miliyan uku ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Amurka tun lokacin da ta fara bulla.

    Ana fuskantar karuwar cutar a jihohi 29 na kasar idan aka kwatanta da makon jiya, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta bayyana.

    Texas da Florida na cikin in da cutar ta fi ƙamari.

  19. Shahararren dan wasan Ingila Jack Charlton ya rasu

    PA Wire

    Asalin hoton, PA Wire

    Tsohon dan wasan Ingila da ya lashe kofin duniya kuma tsohon wanda ya horas da kasar Jamhuriyar Ireland Jack Charlton ya mutu yana da shekara 85 a duniya.

    Tsohon dan wasan bayan kungiyar Leeds ya yi ta fama da cutar kansa ne a shekarar da ta gabata da kuma cutar mantuwa.

    Daya daga cikin manyan ‘yan wasan ingilan ya yi matukar samun shuhura, saboda yana cikin tawagar da ta lashe kofin duniya a filin wasa na Wembley a 1966, tare da dan uwansa Bobby Charlton.

    A wata sanarwa da iyalansa suka fitar “ Ranar Juma’a 10 ga watan Yuli Jack ya mutu cikin kwanciyar hankali yana da shekara 85 a gidansa da ke Northumberland, zagaye da iyalansa”.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barka da safiyar ranar Asabar da fatan mun wayi gari lafiya.

    Buhari Muhammad Fagge ne ke fatan kasancewa da ku a cikin yinin wannan rana domin kawo muka labarai da rahotanni da suka shafi Najeriya da Nijar da Ghana da Sudan da dai sauran kasashen Afrika har ma da duniya baki daya.