Korona: China ta yi watsi da buƙatar wasu lauyoyi ta biyan Najeriya diyyar biliyan $200

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Halima Umar Saleh

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau.:

    • An hango gwaggwan birrai dauke da jarirai a Najeriya
    • Za a rika boye sunaye mutanen da aka yi wa fyade a Masar
    • Cutar korona ta yi ajalin Sarauniya a Afirka ta Kudu
    • An sake bude zirga-zirgar jiragen sama a Sudan ta Kudu
    • An fallasa 'yan majalisar da ke ɗumama kujera a Kenya
    • Korona za ta jawo yunwa ta kashe mutum 12,000 kullum a karshen 2020 - Oxfam
    • 'Yan sandan Najeriya sun kama gungun 'yan fashi a Ondo
    • An kama mutum 4 da zargin 'lalata' yara a Nasarawa

    Ku duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da wasu muhimmai..

  2. Ilhan Omar: Dole Amurka ta biya diyya ga 'yan Somalia kan hare-haren jirage

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yar majalisar wakilan nan ta Amurka kuma 'yar asalin ƙasar Somalia wato Ilhan Omar, na ƙoƙarin ganin cewa Amurka ta biya diyya ga waɗanda hare-haren jirage marasa matuƙa suka kashe a Somalia.

    "Jirage marasa matuƙa na kai hari ne da dare. Ba su kashe 'yan ta'adda, sai dai farar hula, da iyalai a lokacin da suke bacci," a cewarta yayin wata hira da BBC.

    "Abin da muke ƙoƙarin yi shi ne dakatar da hakan da tabbatar da cewa ana abin da ya kamata, kuma abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne biyan diyya ga iyalan waɗanda suka mutu."

    "Muna amfani da dokar ƙasa da ƙasa, hakan ya sa idan aka kashe wani ba bisa ƙa'ida ba, dole a biya diyya." in ji ta.

  3. Zanga-zanga: Firaiministan Sudan ya sauke ministoci 7

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Firaiministan Sudan ya sauya manyan ministocinsa bakwai bayan zanga zangar adawa da ta danganci yadda gwamnatin rikon ƙwarya ke mulki a ƙasar.

    Al'ummar Sudan na korafin cewa basu ga alamun samun sauyin siyasa da suka yi fafutukar samarwa ba.

    Rahotanni sun ce Firaiminista Abdallah Hamdok ya sauke ministan lafiya, kafin daga baya ministoci shida da suka haɗa da na kuɗi da makamashi da kuma harkokin ƙasashen waje suka ajiye aiki da kansu.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne Mista Hamdok ya sauke shugaban 'yan sanda na ƙasar da mataimakinsa.

  4. Korona: China ta yi watsi da buƙatar wasu lauyoyi na biyan Najeriya diyyar biliyan $200

    ..

    Asalin hoton, NIGERIAN BAR ASSOCIATION

    Ƙasar China ta yi watsi da yunƙurin wasu lauyoyin Najeriya 11 inda suka nemi Chinar ta biya Najeriya diyyar kuɗi sakamakon irin ɓarnar da cutar korona ta yi.

    Ofishin jakadanci na China da ke Najeriya ya bayyana wannan yunƙurin a matsayin "abin takaici".

    Lauyoyi 11 na Najeriyar sun buƙaci Chinar ta biya Najeriya diyya ta dala biliyan 200 sakamakon rayuka da aka rasa da kuma matsin tattalin arziƙi da ruɗani da kuma ƙunci da cutar wadda ta samo asali daga China ta kawo wa Najeriya.

    A wata sanarwa, ofishin jakadancin ya bayyana cewa "Cutar Covid-19 ta bazu a duka ƙasashen duniya, ita kanta China ba ta tsira daga wannan cuta ba, mun yi iya ƙoƙarinmu domin kare mutane daga wannan cuta".

    Lauyoyin Najeriyar dai na ƙoƙarin shawo kan ƙasar da ta gurfanar da China gaban kotun ƙasa da ƙasa, sai dai har yanzu ba a ji wannan yunƙurin nasu an fara maganar shi a kotun Najeriyar ba.

  5. An kama mutum 4 da zargin 'lalata' yara a Nasarawa

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron tattaunawar BBC da wani kwamanda a hukumar NSCDC

    Hukumar tsaron al'umma a Najeriya ta Nigeria security and Civil Defence Corps wato NSCDC, ta yi nasarar cafke wasu mutum huɗu tare da gurfanar da su a gaban kotu, waɗanda ake zargi da lalalata ƙananan yara.

    Daga cikin waɗanda aka kama akwai ɗan shekara 35 wanda ake zargi da lalata yarinya 'yar shekara shida, sai kuma wani ɗan shekara 30 wanda ake zargi da lalata 'yar sjekara shida, inji wani babban kwamanda a hukumar Muhammad Gidado.

    Ya kuma bayyana cewa akwai wani ɗan shekara 39 da aka kama wanda ake zargi da lalata yarinya 'yar shekara bakwai sa'annan kuma akwai wani ɗan shekara 41 wanda ake zarginsa da lalata wani yaro ɗan shekara 10.

  6. Ku saurari labaran duniya cikin minti daya da BBC Hausa

    Ku saurari labaran duniya cikin minti daya da BBC Hausa ta hanyar latsa kasa:

    Bayanan sautiLabaran Duniya Cikin Minti Daya Da BBC Hausa 09/07/2020
  7. Coronavirus: Me ke faruwa a duniya?

    • A halin yanzu, sama da mutum miliyan 12 suka kamu da cutar korona a faɗin duniya, sama da mutum 550,000 suka mutu, kamar yadda ƙididdigar jami'ar Johns Hopkins ta nuna.
    • Amurka ce ke da kashi uku cikin huɗu na yawan waɗanda suka kamu da cutar ta korona, sai Brazil ce ta biyu da mutum miliyan 1.7 sai kuma Indiya da sama da mutum 760,000.
    • Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce za ta kafa kwamiti domin sake bitar yadda ƙasashen duniya ke tunkarar annobar korona. Tsohuwar Firaiministar New Zealand Helen Clark tare da Tsohuwar Shugabar ƙasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ne za su jagoranci kwamitin.
    • Ƙungiyar bayar da agaji ta Oxfam ta yi gargaɗin cewa zuwa ƙarshen wannan shekara, mutum 12,000 za su iya mutuwa a rana ɗaya sakamakon yunwa da ke da alaƙa da talaucin da korona ke haddasawa.
    • Mutum 221 suka mutu a Iran inda ake zargin mutuwar na da alaƙa da cutar korona - wannan ne karo na farko da aka samu adadi mai yawa a ƙasar irin haka tun bayan ɓarkewar cutar.
  8. Yadda 'yan Legas ke karyata korona duk da can ne cibiyar cutar a Najeriya

    Yawan masu cutar korona na karuwa a Afrika. Amma har yanzu a wasu kasashen mutane ba su ma yarda cewa annobar gaskiya ce ba.

    Ku latsa hoton da ke kasa don kallon bidiyon:

    Bayanan bidiyo, Yadda 'yan Legas ke karyata korona duk da can ne cibiyar cutar a Najeriya
  9. An tanadi kaburbura miliyan daya da rabi don masu fama da korona a Afirka Ta Kudu

    South Africa Graves

    Asalin hoton, EPA

    Yayin da cutar korona ke kara yaduwa, sannan ake gudanar da shirye- shirye daban-daban na dakile ta, jami'ai a Afrika Ta Kudu na neman kwantar da hankulan fargabar cewa gwamnati na tsammanin za a sami mace- macen cutar koronar fiye da Miliyan daya.

    Sun ce za a samu hakan ne a daya daga cikin manyan Lardunan kasar, kamar yadda wasu kafafen yada labarai na cikin gida suka bayyana.

  10. 'Yan sandan Najeriya sun kama gungun 'yan fashi a Ondo

    Mohammed Adamu

    Asalin hoton, NPF

    Jami'an 'yan sanda na runduna ta musamman a Najeriya sun kama gungun 'yan fashi na mutum bakwai da suka kai hari tare da yin fashi a wasu bankuna uku da ke jihohin Ondo da Ekiti a kudu maso yammacin Najeriya a tsakanin shekarun 2019 da 2020.

    Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar 'yan sanda kasar ta aike wa manema labarai a ranar Alhamis, inda ta ce a yayin ta'addancin 'yan fashin sun kashe mutum shida da suka hada da 'yan sanda tare da sace miliyoyin naira.

    Bincike ya nuna cewa 'yan fashin masu tsakanin shekaru 36 zuwa 50, sun yi fashin ne a wani bankin kasuwanci da ke Ile-oluji, a jihar Ondo ranar 7 ga watan Fabrairun 2020, inda aka kashe 'yan sanda hudu.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen na da hannu a fashin da aka yi a wani bankin ba da rance da ke Idanre, a jihar Ondo a watan Disamban 2019 da kuma wani bankin kasuwanci da ke Oye Ekitia jihar Ekiti, inda 'yan sanda biyu suka rasa rayukansu.

    Rundunar ta ce ana ci gaba da kokarin kama sauran mutanen da ke cikin gungun don kwato muggan makamai da suke amfani da su.

    A wani lamarin mai kama da haka kuma, rundunar ta ce an kama wasu mutum 23 masu hannu a laifuka kamar satar mutane don kudin fansa da fashi da mallakar muggan makamai.

    ''Nan gaba kadan za a gurfanar da mutanen a kotu bayan an kammala bincike,'' a cewar sanarwar.

  11. Ana ci gaba da zakulo mutanen da abtarewar kasa ya rutsa da su a Japan

    Hukumomin ba da agajin gaggawa na ci gaba da aikin zakulo jama'ar da ibtila'in ambaliya da zabtarewar kasa ya rutsa da su a Japan.

    Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 58 da kuma lalata dubban gidaje musamman a yankin Gifu da ke tsakiyar Japan.

    Hasashen yanayi ya nuna cewa za a ci gaba da fuskantar ruwan sama mai karfi.

    A kan haka aka gargadi al'umma da su zama cikin shiri don akwai yiwuwar wata ambaliyar.

    Ko a shekarar 2018 sama da mutum 200,000 suka mutu a yammacin Japan a irin wannan yanayi na ambaliya da zabtarewar kasa.

  12. Wasu Amurkawa na yi China kallon abokiyar gaba - China

    Trump da Xi

    Ministan harkokin wajen China Wang Yi, ya ce akwai wasu jama'a a Amurka ke wa Chinar kallon babbar abokiyar gaba.

    Ya ce kasashen biyu ba su taba fuskantar tsamin dangantaka ba kamar a wannan karon.

    Gwamnatin Shugaba Trump na matsa wa China lamba kan harkokin kasuwanci da tauya hakkin bil'adama da kuma annobar Korona.

    Mr Wang ya bayyana cewa Amurka na wa shirye-shiryen Chana mummunar fahimta, amma yana da tabbacin cewa za su dinke barakarar da ke tsakaninsu.

    Amurka na yi wa Chana kallon marar gaskiya, shi yasa duk wani abu da ya shafi gwamnatin China take ganin babu gaskiya a ciki, kuma ba ta da hujja kan hakan.''

  13. Korona za ta jawo yunwa ta kashe mutum 12,000 kullum a karshen 2020 - Oxfam

    Africa coronavirus hunger

    Asalin hoton, EPA

    Kungiyar agaji ta OXFAM ta yi hasashen cewa mutum 12,000 za su mutu a kowace rana daga karshen shekarar da muke ciki a kasashen duniya sakamakon tangardar da annobar korona ta janyo a fannin walwala da tattalin arziki.

    Oxfam ta ce adadin ya zarce yawan mace-macen mutane a kowace rana sanadin cutar korona inda an rika samun mutum 10,000 da suka rika mutuwa tun daga watan Afrilun da ya gabata.

    Matakan dakile bazuwar cutar da aka sanya a kasashen Afrika da sauran kasashen duniya sun sa mutane da dama sun rasa ayyukansu, kuma sun sa ba a yi noma domin samar da abinci ballantana mutane su saya ba.

    Kungiyar ta Oxfam ta ce matsalar za ta yi kamari a kasashe irin su Sudan Ta Kudu da Sudan da Habasha da Jamhuriyar Dimokaridiyyar Kongo da kuma kasashen yammacin Afrika da ke yankin Sahel.

    Al'ummomin wadannan kasashe na fuskantar yunwa sakamakon sauyin yanayi da rikice-rikice da kuma farin dango da suka afka wa gonaki a yankin Gabashin Afrika

    Sai dai Oxfam ta ce annobar korona za ta kara jefa rayuwarsu cikin halin ni 'yasu.

  14. Kotun Kolin Amurka ta bayar da umarni a binciki Shugaba Trump

    Kotun Kolin Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun Kolin Amurka ta ce masu shigar da kara a New York na iya duba takardun haraji da sauran harkokin kudin Shugaba Donald Trump.

    A wata shari'a mai alaka da wannan, kotun ta ce ba lallai ne a mika bayanan takardun harkokin kudin shugaban da majalisar Amurka ba.

    Mista Trump ne shugaban Amurka na farko tun zamanin Shugaba Richard Nixon a shekarun 1970 da ya ki bayyana yawan harajin da yake biya.

    Lauyoyinsa sun ce shugaban na da kariya a yayin da yake rike da mukamin shugaban kasa, kuma majalisar Amurka ba ta da hurumin duba harkokin kasuwancin shugaban.

    Bayan yanke hukuncin, Mista Trump bai bata lokaci ba sai ya mayar da martani ta shafinsa n Twitter: "Kotun Koli ta sake mayar da wannan shari'ar ga wata kotu da ke kasanta domin a ci gaba da shari'ar. Wannan ba komai ne ba face cin mutunci a siyasance."

    A shari'ar da ake yi da masu shigar da kara daga New York suka shigar, alkalan Kotun Kolin bakwai sun ce kariyar da shugaban yake da ita ba ta hana a bincike shi ba idan ya aikata laifi.

    Amma alkalai biyu sun goyi bayan Shugaba Trump.

    Kotun Kolin ta ce: "Shekara 200 da ta gabata, wani shahararren alkalin wannan kotun ya kafa wata hujja cewa babu dan Amurka, ko da shugaban kasa ne kuwa da yafi karfin a nemi ya mika shaida ga kotun da ke shari'a kan wani batu da ya shafi aikata laifi. Kuma a yau muna jaddada wannan hujjar."

  15. An fallasa 'yan majalisar da ke ɗumama kujera a Kenya

    Majalisar dokokin Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan majalisar dokokin Kenya 21 ba su taba cewa ko da uffan ba a zauren majalisa a cikin kusan shekara daya, a cewar wata kungiya da ke sanya ido a kan majalisun dokokin kasar.

    Jerin sunayen 'yan majalisar, wanda kungiyar Mzalendo, wacce a harshen Swahili ke nufin "Masu kishin kasa, ya nuna cewa maza ne suka kankane shi - 'yan majalisar wakilai 16 da dan majalisar dattawa daya ba su ce uffan ba.

    Biyu daga cikin 'yan majalisar - Oscar Sudi da Samuel Arama - ba su bayar da kowacce irin gudunmawa ba tun daga 2017.

    A tattaunawar da ake yi a shafin Twitter wasu sun ce babu wani abu idan dan majalisa bai yi magana ba idan dai yana raya mazabarsa, sai dai wasu sun ce ya kamata 'yan majalisa su rika magana domin wakiltar mutanensu a zauren majalisar

    Caroline Gaita, wacce ta jagoranci Mzalendo, ta shaida wa shirin Newsday na BBC cewa, jerin 'yan majalisar ya fito da irin gudunmawar da kowannensu ya bayar a shekarar 2019.

    Ta kara da cewa hakan wata hanya ce ta tabbatar da cewa 'yan majalisar sun yi aikin da aka zabe su domin su gudanar.

    'Yan majalisun dokokin Kenya suna cikin 'yan majalisar da aka fi bai wa albashi a duniya, inda kowanne yake karbar fiye da $6,000 duk wata.

  16. An sake bude zirga-zirgar jiragen sama a Sudan ta Kudu

    Sudan ta Kudu

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukunta a Sudan ta Kudu sun sake bude zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasashen nahiyar Afirka da ma kasashen duniya.

    A watan Maris aka dakatar da zirga-zirgar jiragen saman kasar domin dakile yaduwar cutar Covid-19.

    Kur Kuol, darakta janar na babban filin jiragen saman Juba, ya shaida wa manema labarai ranar Laraba cewa kamfanin jirgin saman Ethiopia shi ne na farko da ya koma jigilar mutane a babban birnin kasar.

    Kamfanin jirgin yana daukar fasinjoji kullum daga Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

    Kazalika kamfanin jiragen saman Badr Airlines na kasar Sudan da ke daukar kaya da fasinja, da kuma Egypt Air sun ya koma zirga-zirga.

    Ranar Juma'a ake sa ran jiragen saman FlyDubai zai koma zirga-zirga daga Juba.

  17. Cutar korona ta yi ajalin Sarauniya a Afirka ta Kudu

    Sarauniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Gidan sarautar Afirka ta Kudu ya tabbatar da rasuwar Sarauniya Noloyiso Sandile sanadin cutar Covid-19.

    'Yar uwa ce ga Sarkin Zulu Goodwill Zwelithini, kuma tana rike da sarautar amaRharhabe a gidan sarauta.

    Sarauniya Noloyiso ta auri Sarkin amaRharhabe, Maxhoba Sandile, fiye da shekara har lokacin da ya mutu a 2011.

    Daga nan ne ta zama sarauniya saboda danta, Jonguxolo Sandile, ya yi kankanta sosai a nada shi sarauta.

    An kwantar da sarauniya mai shekara 56 a asibiti sanadin Covid-19, a cewar kafar yada labarai ta SABC.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana ta a matsayin "mai kare al'adun kasar kuma shugaba mai kwazo ga al'ummarta".

  18. Za a rika boye sunaye mutanen da aka yi wa fyade a Masar

    Majalisar zartarwar Masar ta amince da wani gyara ga dokokin kasar inda za a rika boye sunayen mutanen da aka yi wa fyade.

    Za a rika bayyana sunayensu kadai ga kotu da kuma lauyoyin da ke kare su idan suka bukaci hakan, a cewar datfarin dokar.

    Sau da dama mutanen da aka yi wa fyade suna fuskantar kyama a kasar Masar.

    Mau'idin da ke da taken "Farkon sauyi kan dokokin mata" a harshen Larabci ya mamaye shafin Twitter na kasar, inda fitattun taurari suke amfani a shi wurin nuna murna kan wannan sabuwar doka, suna kira ga mata su bayana halin da suka shiga game da fyade.

  19. Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan harajin Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun Kolin Amurka za ta yanke hukunci kan ko majalisun dokoki da masu shigar da kara za su iya yin bincike kan haraji da sauran harkokin kudin Shugaba Donald Trump - hukuncin zai yi babban tasiri kan harkokin siyasa.

    Mr Trump ya ki bayyana takardun da ke bayani kan harkokin kasuwancinsa.

    Lauyoyinsa sun ce yana da kariyar da ta hana shi nuna takardun tun da yana kan mulki.

    Hukuncin zai tabbatar ko ya yi watsi da wannan ikirari na lauyoyin Mr Trump sannan ya bayyana irin karfin da 'yan majalisun dokokin Amurka suke da shi na gudanar da bincike na shugaban kasa.

    Ko a hukuncin ya goyi bayan 'yan majalisun dokoki, hakan ba ya nufin dole ai Shugaba Trump ya bayyana harajinsa ga bainar jama'a kafin yunkurinsa na sake zama shugaban kasa a atan Nuwamba.

    Mr Trump, wanda ya samu galibin dukiyarsa daga sayar da gidaje, shi ne shugaban kasa na farko tun baan Shugaba Richard Nixon a shekarun 1970 da bai bayyana wa 'yan kasar kudin da yake samu ba.

    Ya bayana matakin gudanar da bincike kan harkokin harajinsa a matsayin "bi-ta-da-kulli" kuma yana kallon matakin majalisar a matsayin yunkurin shafa masa kashin kaji a siyasance.

  20. Norwich za ta sayar da Ben Godfrey kan £50m, Havertz yana son tafiya Chelsea

    Ben Godfrey

    Asalin hoton, Getty Images

    Norwich City tana son a biya ta kusan £50m kan dan wasan da ke tsaron baya Ben Godfrey, 22, a yayin da Borussia Dortmund da RB Leipzig suke zawarcin dan kwallon na Ingila da ke buga gasar Under-21.(Sky Sports)

    Dan wasan Kai Havertz, mai shekara 21, ya shirya domin shigar da bukatar barinsa Bayer Leverkusen bayan ya shaida waChelseacewa yana son komawa can a bazara.(Star)

    Chelsea tana fatan yin amfani da damar sha'awar da Havertz ya nuna ta haduwa da 'yan kasarsa ta Jamus Timo Werner, mai shekara 24, da Antonio Rudiger, mai shekara 27, a Stamford Bridge.(Telegraph)

    Wakilin Kevin de Bruyne ya yi watsi da maganganun da ake yi cewa dan wasan na Belgium mai shekara 29 yana shirin barin Manchester City domin komawa Real Madrid ko Paris St-Germain.(Sporza, via Star).