Abin da ke cikin kudurin dokar cin zarafin mata na Najeriya

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh, Buhari Muhammad Fagge and Sani Aliyu

  1. Mun kawo karshen wannan shirin

    Da fatan an ji dadin kasancewa da mu, za kuma ku iya tara wa gobe don kawo muku labarai kai tsaye daga sassa na duniya.

    Duk lokacin da muka gabatar da wannan shiri na kai-tsaye, za ku iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook da Twitter da kuma Instagram.

  2. Batun Ibrahim Magu ya jefa gwamnatin Najeriya a tsaka mai wuya

    A Najeriya, wasu masu fafutukar yaƙi da cin hanci sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan makomar Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon-kasa, bayan gwamnatin kasar ta dakatar da shi.

    An dai dakatar da shi ne bayan wani binciken da wani kwamiti ya fara a kan zargin da ake masa na yin nuƙu-nuƙu game da ainihin kudi da kuma ƙadarorin da hukumar ta ƙwato daga hannun wasu jami'an gwamnati.

    Daga kafa hukumar EFCC zuwa yanzu dai ta yi shugabanni hudu, kuma babu ɗaya daga cikinsu da yayi rabuwar mutunci da hukumar. Shugaban hukumar na farko Malam Nuhu Ribado, an yi masa kora da hali ta hanyar tura shi kwas na rana tsaka, daga nan ya yi bankwana da kujerar.

    Sai Farida Waziri, wadda ta gaje shi, haka aka raba ta da muƙamin, duk da cewa gwamnatin wancan lokacin ta ce dalilan cire ta na sirri ne.

    Shi ma Ibrahim Lamurde, wato magajin Farida Waziri wata rabuwa ya yi ba tare da sallama ba, a daidai lokacin da majalisar dattawan Najeriyar take nemansa domin ya yi bayani a kan wani kuɗin da hukumar ta ƙwato, da ake zargin ya salwanta.

    Masu fafutukar yaƙi da cin hancin dai na ganin cewa wannan dambarwa da ake yi a kan Ibrahim Magu ya jefa gwamnatin Najeriya a mawuyacin hali, ko da kwamitin bincike ya same da laifi ko akasin haka.

    Ibrahim Magu

    Asalin hoton, TWITTER/EFCCOFFICIAL

  3. Gwamnatin Kamaru ta karyata tattaunawar zaman lafiya da ƴan awaren Ambazonia

    Julius Ayuk Tabe Cameroon separatist leader

    Asalin hoton, SISIKU AYUK/FACEBOOK

    Bayanan hoto, Madugun ƴan awaren Ambazonia Julius Ayuk Tabe

    Gwamnatin Kamaru ta yi watsi da labarin da aka watsa a shafukan sada zumunta da ke cewa ta fara tattaunawa da shugabannin ƴan aware domin samun mafita game da rikicin da yankin renon ingila yake fama.

    Gwamnatin ta ce gaskiyar lamarin ta sha bamban da ainhin abin da yake gudana.

    Amma kakakin gwamnatin kasar Rene Emmanuel Sadi, wanda kuma shi ne ministan sadarwa na Kamaru ya bayyana cewa gwamnatin kasar na "kaunar samun mafita" game da wannan rikici.

    Wannan labari na ganawa da bangaren gwamnati ya fito ne daga madugun ƴan aware Julius Ayuk Tabe wanda yake tsare a kurkuku yanzu haka.

    Majalisar Dinkin Duniya wadda ke shiga tsakani a kan batun samar da zaman lafiya a yankin renon Ingila na Kamaru ta dade tana yin kira ga bangarorin biyu su hau teburin tattaunawa domin sasanta tsakaninsu.

    Sai dai kakakin gwamnatin ta Kamaru ya ce kofa na bude wajen samar da mafita kan wannan batu da yaki ci, yaki cinyewa.

  4. Majalisar dokokin jihar Ondo tana shirin tsige matamakin gwamna

    Agboola Ajayi, mataimakin gwamnan jihar Ondo

    Asalin hoton, NNN NEWSPAPER

    Bayanan hoto, Agboola Ajayi, mataimakin gwamnan jihar Ondo

    Majalisar Dokokin jihar Ondo ta aikawa Agboola Ajayi, mataimakin gwamnan jihar takardar shirin tsige shi daga kan mukaminsa. Kamar dai yadda ƴan majalisar su ka bayyana, sun dauki wannan mataki ne sakamakon wasu laifuka da suka ce mataimakin gwamnan ya aikata.

    Cikin wasikar, ƴan majalisar sun tuhumi mataimkin gwamnan da laifukan haifar da tarnaki ga gudanar da ayyukan gwamnatin jihar, kana sun tuhume shi da rashin biyayya ga gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu.

    Sai dai mataimakin gwamnan ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, inda ya ce matakin da majalisar jihar ta dauka ba wani abu ba ne face siyasa domin takun sakar da ke tsakaninsa da gwamnan jihar.

    Ƴan majalisa 14 cikin 26 na majalisar jihar ne suka rattaba hannu kan takardar tsige mataimakin gwamnan, yayin da tara daga cikinsu ba su amince da kudurin tsige shi ba, amma wasu mambobi uku cikinsu sun kauracewa daukar wani mataki kan batun.

    Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu dai na takun saka da mataimakin nasa Agbola Ajayi wanda a yanzu ya koma jam’iyyar adawa ta PDP.

  5. Abin da ke cikin kudurin dokar cin zarafin mata na Najeriya

    sexual assault

    A yau Talata ne Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wani kudurin doka da zai ba da kariya ga dalibai a manyan makarantun kasar, bayan yi masa karatu na uku.

    Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Ovie Omo-Agege ne ya gabatar da kudurin dokar mai take ''Wani shirin doka wanda zai hana da ba da kariya da kuma hukunta masu fasikanci da dalibai a manyan makarantu, da kuma wasu harkokin masu alaka da shi na shekara ta 2019.

    An dai amince da kudurin dokar ne bayan duba da nazarin da majalisar dattawan ta yi a kan rahoton kwamitin da ke kula da abubuwan da suka shafi shari'a da take hakkin bil adama wanda ke da alhakin yin garanbawul akan dokar tare da kuma shirya yadda za a saurari bahasin jama'a a kan dokar.

    A dai sake gabatar da kudurin a gaban majalisar dattawan tun a watan Oktoban da ya wuce inda kuma har aka yi masa karatu na biyu a watan Nuwamba.

    Kudurin dokar ya kunshi abubuwa da dama da suka hada da hukuncin shekara 14 koma fiye da haka ga duk wanda aka samu ya ci zarafin daliba, akalla dai mutum zai iya shekara biyar a gidan yari ba tare da beli ba.

    Daga cikin tanade-tanaden da ke kudurin akwai batun cewa:

    • Duk malamin da ya yi tarayya da daliba ko kuma ya bukaci yin tarayya da ita akwai hukunci akansa na shekara 14 ko kuma mafi kankantar hukuncin yin hakan shi ne shekara biyar ba tare da tara ko beli ba.
    • Haka duk wanda ya tursasawa daliba yin lalata da wani ma irin wannan hukunci zai fuskanta, sannan duk malamin da aka samu ya rungumi ko sumbata ko taba wani bangare na jikin daliba ma akwai hukunci akansa.
    • Sannan duk malamin da aka samu ya aika da wani sako na batsa ko ta hannu ko kuma ta wata kafar sadarwa ga daliba akwai hukunci akansa.
    • Haka duk malamin da yi zancen batsa da kifta idanu da nufin wani batanci ga daliba akwai hukunci akansa.

    An dai sake gabatar da wannan kudurin ga majalisar dattawan ne kwana biyu bayan BBC ta yi wani rahoton na musamman inda aka bankado asirin wasu malaman jami'a biyu a jami'ar Legas da kuma wani malamin jami'a a Ghana da suke cin zarafin dalibansu mata domin neman makin jarrabawa.

    Wannan rahoton na BBC ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu yan Najeriyar suka bayyana wannan halayya a matsyain rashin tarbiyya a jami'oin kasar.

    A yayin sauraron bahasin jama'a akan kudurin dokar, malaman jami'oi da ma'aikatan jami'o'i da kungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana damuwa tare da bukatar a yi gyara akan kudurin dokar don kawo karshen cin zarafin dalibai a makarantu.

  6. Jair Bolsonaro: Shugaban ƙasar da ke ƙaryata korona ya kamu da ita

    Jai Bolsanaro

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya kamu da cutar korona.

    Wannan ne karo na hudu da aka yi masa gwajin, wanda aka yi masa a ranar Litinin bayan nuna alamun kamuwa da cutar ciki har da zafin jiki.

    Mista Bolsonaro ya sha nuna wannan cutar ba wata aba ba ce, yana kiranta 'yar karamar mura yana kuma cewa ba za ta taɓa kwantar da shi ba.

    Ya kuma umarci gwamnonin yanki da su sassauta dokar kullen da aka sanya saboda shawo kan annobar korona, wanda ya ce tana hana ci gaban tattalin arziki, a ranar Litinin ne kuma ya sassauta dokar sanya takunkumi.

    Idan muka koma watan Afirilu, ya ce idan cutar ta kama shi ba zai damu kanshi ba saboda ba zai ji komai ba, ''abin da zan iya ji shi ne kamar wata 'yar mura nake.''

    Lokacin da ya yi wannan maganar, mutanen da cutar ta kashe ba su fi 3,000 ba a kasar, kuma 40,000 ne suka kamu duka.

  7. EU za ta tsuke bakin aljinhunta

    gETTY

    Asalin hoton, Getty Images

    Tarayyar Turai ta fara gudanar da sauye sauye kan kasafin kudinta na bana, saboda tasirin cutar Korona kan tattali arzikin kasashenta.

    Cikin wani rahoto da kungiyar ta fita ta ce, ta yi hasashen cewa zai yi wahala ta iya gudanar da abubuwan da ta shata daga nan zuwa badi.

    Rahoton ya kuma yi hasashen karin sauye sauye lura da yadda cutar korona ke kokarin dawowa a karo na biyu. Wani rahoto na daban ya bayyana cewa za a samu rashin aikinyi sosai a kasashe masu karfin tattalin arziki.

    Wakilin BBC ya ce wani bincike ya nuna cewa rashin aikinyi da za a fuskanta zai ninka so goma akan wanda aka fuskanta a shekarar 2008.

  8. An fitar da jadawalin jarrabawar WAEC

    Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma, WAECE,ta fitar da jadawalin shekarar 2020.

    Babban jami'in hukumar Mr. Patrick Areghan ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

    "An aika jadawalin karshe na WAEC ga ofisoshin yankuna da rassa ga makarantun ilimi da ma'aikatu na gwamnatin tarayya da jihohi," in ji babban jami'in.

    Ya jaddada cewa za a gudanar da jarrabawar ne ranar 3 ga watan Agusta sannan a kammala 5 ga watan Satumba.

    Ya ce dalibai 1,549,463 ne za su rubuta jarrabawar daga makarantu 19, 129 da ke fadin kasar, yana mai gargadi ga dalibai su guji satar jarrabawa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Nan ne garin da korona ta samo asali

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    A tsakiyar watan Janairu ne China ta sanar da mutuwar mutum uku. A yau akwai sama da mutum miliyan 11 da suka kamu da wannan cuta a fadin duniya, ta kuma kashe a kalla wasu rabin miliyan - kuma cutar ta janyo sanya dokar kulle ga tattalin arzikin duniya baki daya.

    A birnin Wuhan ne aka fara samun bullar cutar, a lardin Hubei - yau kuma gata anan muma, inda za yi bincike kan asalin wannan cuta, wadanda za su janyo wasu manyan tambayoyi a garesu, wanda kuma ake ta yada jita-jitar cewa wani karin rikici ne tsakanin Amurka da China.

    Shin ko wannan cuta gaskiya ce - kamar yadda wasu masana kimiyya suke tambaya - ko kuma kirkirarta aka yi a dakin bincike?

  10. Ba za a koma makaranta ba sai 2021 - Kenya

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Ma'aikatar Ilimi ta Kenya ta ce za a sake bude makarantun firaimari da sakandire ne a 2021.

    Ma'aikatar Ilimin ta ce duka daliban za su koma ajujuwan da suke ne a lokacin da aka tafi hutu.

    Ministan ilimi George Magoha ya ce babu jarrabawar karshe ga dalibai firaimari da skandire.

    Ana dai yin wadannan jarrabawar ne a watannin Oktoba da Nuwamba na ko wacce shekara.

    Amma ya ce Kwaleji da jami'o'i su shirya domin sake budewa a watan Satumbae wannan shekaar amma da wasu sharuda, kuma ya ce wadanda suka cika sharudan ne kawai za a bari su bude.

    An rufe makarantu a Kenya ne a watan Maris bayan kasar ta samu mai dauke da korona na farko.

  11. Ana kama ma'aikatan jinya da ke yajin aiki a Zimbabwe

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Ma'ikatan jinyar na son a rika biyanzu da dalar Amurka ne

    Kungiyar ma'aikatan jinya a Zimbabwe ta ce 'yan sanda sun kama gwamman mambobinta da wasu wakilai da ke zanga-zanga kan rashin biyansu kudin da ya dace.

    Ma'aikatan jinyan na bukatar a rika biyansu da dalar Amurka, suna cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasar wanda yakai kusan kashi 800 cikin dari na yin kaca-kaca da albashinsu.

    "Akalla an kama mambobinmu 13 da shugabannin kungiyarmu yayin zanga-zangar da muka yi a babban asibitin Harare," in ji Enock Dongo, shugaban kungiyar ya shida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    "Suna ofishin 'yan sanda lokacin da muka yi magana amma ban san wacce irin tuhuma ake musu ba," ya kara da cewa.

    Kungiyar ma'aikatan jinya ta Zimbabwe wadda take wakiltar kimanin sama da ma;aikata 15,000 a jihar ta yi kiran mabobinta da su fito zanga-zanga a makon jiya saboda rashin biyansu kudi yadda ya kamata.

    Mutum 716 aka tabbatar suna dauke da cutar kuma ta kashe mutum takwas ya zuwa yanzu.

  12. Amurka za ta daina bai wa ɗaliban ƙasashen waje biza

    Dalibai

    Asalin hoton, Getty Images

    Ba za a rika kyale daliban kasashen waje su rika zama a Amurka ba da zarar an koma ba da karatu ta intanet baki daya, sai dai idan za su halarci wasu darussan da ake bukatar ganinsu a zahiri.

    Ma'aikatar da ke lura da shige da fice da ta hana fasakauri sun ce za a rika mayar da mutane kasashen da suka fito matukar ba su cika ka'idojin zama a Amurka ba.

    Da yawa daga cikin jami'o'in kasar sun mayar da bayar da darussa ta kafar intanet saboda annobar korona. Babu wanda ya san adadin daliban da wannan lamari zai shafa.

  13. Coronavirus: An hana 'yan jagaliyar siyasa zuwa filayen jirgin sama a Najeriya

    Najeriya ta haramta wa magoya bayan siyasa shiga wuraren da ake zama kafin jirage su tashi da ke filayen jiragen saman kasar, a yayin da kasar ke shirin sake bude harkokin tafiye-tafiye.

    A wani sako da ma'aikatar zirga-zirgar jirage saman kasar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ambato Minista Hadi Sirika ya ce an dauki matakin ne domin dakile yaduwar cutar korona ga mutanen da ke dandazon zuwa filayen jiagen na sama.

    Ya kara da cewa matafiya kawai za a bari su shiga filayen jiagen sama.

    “Daga yanzu, ba za a bar dukkan manyan mutane su je filin jiragen sama da wadanda ba matafiya ba ne. Mun fadi hakan ne musamman ga gwamnoni da ministoci, da 'yan majalisun dokokin tarayya, da alkalai da kuma sojoji, a cewarsa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Chelsea na son Rice, Madrid ba za ta saye 'yan wasa ba

    Rice

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Chelsea Frank Lampard na son dauko dan wasan tsakiya naWest Hamda Ingila Declan Rice, mai shekara 21.(Times - subscription required)

    Manchester City da Manchester United suna son dan wasan baya na Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, da kuma dan Milan Skriniar, da ke taka leda aInter Milanda Sloviakia.(Independent)

    Chelsea da Real Madrid na son shan gaban Manchester United da Paris St-Germain kan dan wasan tsakiya na Lazio Sergej Milinkovic-Savic mai shekara 25.(Gazzetta dello Sport, via Express).

  15. An aika tsoffin 'yan tawaye don shawo kan rikicin DR Congo

    Katanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta aka tsofaffin 'yan tawayen kasar, ciki har da biyu daga cikin wadanda Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka, ICC da ke Hague ta samu da laifin yaki, domin su rarrashi masu tayar da kayar baya da ke yankunansu su ajiye makamansu.

    Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta mayar da hankali kan wasu daga cikin manyan mutanen da suka taka rawa a rikice-rikicen kasar na baya domin yunkurin dakile rikice-rikicen da ake yi yanzu, inda ta aika da tawaga yankin Ituri makon jiya.

    Cikin wadanda aka tura har da Germaine Katanga, wanda Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kama da laifin cin zarafin bil adama a 2014 da kuma laifuka hudu na yaki a Lendu a 2003 inda ya jagoranci kai hari a kauyen wanda ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 200.

    Wani daga cikin 'yan tawagar shi ne Mathieu Ngudjolo, wanda Kotun ICC ta tuhuma amma daga bisani ta wanke shi bisa rawar da ya taka a wancan harin.

    A Ituri, 'yan bindiga sun kashe mutum 11 ciki har da sojoji da jami'an gwamnati a wani kanton-bauna da aka dora alhakinsa kan CODECO, wato kungiyar masu tayar da kayar baya da aka zarga da kashe-kashen gilla, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP reported.

    • An tsayar da mace takarar mataimakiyar shugaban kasar Ghana

      Naana Opoku Agyeman

      Asalin hoton, Getty Images

      Babbar jam'iyyar hamayya a Ghana ta tsayar da mace a matsayin 'yar takarar mataimakiyar shugaban kasa a karon farko a kasar.

      Naana Opoku Agyeman za ta yi aiki tare da tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama a yayin da yake yunkurin sake darewa karagar shugabancin kasar a zaben watan Disamba mai zuwa.

      Farfesa Opoku Agyeman tsohuwar ministar ilimi kuma tsohuwar shugabar jami'ar Cape Coast ce.

      Idan jam'iyyar hamayya ta NDC ta yi nasara a zaben wannan shekarar, za ta zama mace ta farko da ta kasance mataimakiyar shugaban kasar Ghana.

      Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar sun ce Farfesa Agyeman mace ce mai karamci da sanin ya kamata kuma kwararriya a faninta.

      Ana sa ran za a yi fafatawa mai zafi a zaben a ranar 7 ga watan Disamba tsakanin Shugaba Nana Akufo-Addo, wanda ke neman wa'adi na biyu, da kuma mutumin da ya mika masa mulki John Dramani Mahama.

    • Barka da wannan lokaci

        • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
        • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

      Muna yi wa masu bibiyarmu a wannan shafi barka d warhaka.

      Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

      Kamar kullum, za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

      A ko da yaushe za ku iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta da muhawara a BBC Hausa.