Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Indiya ta zama ta uku a yawan masu korona a duniya

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labarai da rahotanni da muka wallafa a wannan shafin:

    • COVID-19: Shugaban ƙasar Ghana ya killace kansa
    • Mexico ta zama ƙasa ta biyar da korona ta fi kashe mutane a duniya
    • Ana binciken 'yar takarar jam'iyyar adawa a Singapore
    • Yadda za a nemo sauran yaran da aka sace a Kano
    • Korona ta kashe sama da mutum 10,000 a Rasha
    • Ban yi nadamar yin sulhu da 'yan bindiga ba – Matawalle
    • Musulmai a Sri Lanka na kuka kan umarnin ƙona gawa
    • Shugaban kasar Mali ya tattauna da gamayyar 'yan adawa
    • An sallami shugaban 'yan sanda da mataimakinsa a Sudan

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Jirgin ruwa zai sauke 'yan cirani 180 a Italiya

    Italiya ta ba wani jirgin ruwan ceto damar sauke 'yan cirani 180, bayan shafe mako guda ana ƙoƙarin cimma matsaya.

    Jirgin ya ceto yan ciranin ne da suka maƙale a Tekun Mediterranean.

    Tun da farko jirgin ruwan na Ocean Vikings ya buƙaci ya sauke su a ƙasar Malta amma ta ƙi yarda.

    A yanzu zai sauke yan ciranin da suka haɗa da mata da ƙananan yara a tashar ruwa da ke Sicily, inda za a killace su tsawon makonni biyu.

  3. Kazakhstan ta sake sa dokar kulle a faɗin ƙasar

    Ƙasar Kazakhstan ta zama ƙasa ta farko da ta fara komawa cikin dokar kulle saboda korona.

    Hakan ya faru ne bayan jama'a da dama sun sake kamuwa da cutar a ƙasar.

    A halin yanzu, za a kulle wuraren wasanni da rukunin shaguna da dakatar da kasuwanci iri daban-daban na akalla makonni biyu.

    An sassauta dokar kulle a ƙasar a ƙarshen watan Mayu a lokacin da ƙasar ke da ƙasa da mutum 9,000 da suka kamu da cutar.

    Amma a halin yanzu, yawan waɗanda ke kamuwa da cutar ya ƙaru zuwa 47,000. Kusan mutum 200 cutar ta kashe a ƙasar.

    Sabbin matakan da aka saka na kullen ba su kai na farkon tsanani ba, sakamakon an bar mutane su rinka shige da fice a ƙasar.

    Shugaban ƙasar Kassym-Jomart Tokayev ya bayar da umarnin ƙarin gadajen asibiti da kashi 50 cikin 100 a makon da ya gabata da kuma bayar da umarnin mayar da wani filin kwallo cibiyar killace masu cutar korona na wucin gadi.

  4. An sallami shugaban 'yan sanda da mataimakinsa a Sudan

    Gwamnatin haɗaka ta Sudan ta sallami shugaban 'yan sanda na ƙasar da mataimakinsa, kwanaki kaɗan bayan da zanga-zanga ta ɓarke a faɗin ƙasar.

    Jama'ar ƙasar dai sun gudanar da zanga-zangar inda suke yin kira da a ƙara kawo sauyi ga yanayin siyasar ƙasar.

    Sojojin ƙasar ne suka hamɓarar da gwamnatinsa bayan an shafe watanni ana zanga-zanga.

    A halin yanzu gwamnatin haɗaka ce ta farar hula da kuma soji ke mulkin Sudan.

    A lokacin da aka yi zanga-zangar ranar Talata, dubban mutane ne suka fito kan tituna inda akasarinsu ke cikin fushi kan rashin ci gaba da ake samu a ƙasar tun bayan hamɓarar da gwamnatin al-Bashir.

  5. Indiya ta zama ta uku a yawan masu korona a duniya

    Ƙasar Indiya ce ta uku a halin yanzu da ke da yawan masu cutar korona a faɗin duniya.

    Yawan ƙaruwar masu kamuwa da cutar a cikin 'yan kwanakin nan ya sa ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta gano kusan mutum 690,000 waɗanda suka kamu da cutar.

    Yanzu dai ƙasar ta Indiya ta zarta Rasha a yawan masu cutar inda ta zama ta uku a duniya.

    Sama da mutum dubu tara suka mutu sakamakon cutar a ƙasar. Hukumomi a ƙasar sun buɗe wata cibiya mai gadajen kwali 10,000 a Delhi babban birnin ƙasar da za a rinƙa kula da waɗanda suka kamu da cutar amma ba su nuna alamomi.

    Masana sun bayyana cewa yawan gwajin cutar da ake yi a Indiya ya yi kaɗan kuma ba a san ainahin yawan masu ɗauke da cutar ba a halin yanzu a ƙasar.

    Amurka ce ƙasar da cutar ta fi ƙamari sai Brazil sai kuma yanzu Indiya.

  6. Shugaban kasar Mali ya tattauna da gamayyar 'yan adawa

    Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta ya tattauna da shugaban sabuwar gamayyar adawa da ke shirya zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar.

    Wannan tattaunawa da shugaban mai ra'ayin rikau Mahmoud Dicko ya yi, na zuwa ne kwanaki bayan gamayyar ta ce ba za ta sanya murabus din shugaba Keita ya zama daya daga cikin sharudan tattaunawar sulhu da shi ba.

    Dubban mutane ne suka halarci zanga-zangar a Bamako babban birnin kasar a watan jiya saboda nuna damuwa kan karuwar matsalolin tsaro, tattalin arziki da kuma kira a sauya fasalin siyasar kasar.

    Masu sukar gwamnatin na kukan cewa ta gaza yin abin da ya dace domin shawo kan karuwar hare-haren masu ikirarin jihadi da kuma matsalar rikicin kabilanci.

  7. An fara gasar Formula 1 ta bana

    A karon farko tun bayan barkewar annobar korona za a fara gasar tseren mota a Austria.

    An dai dakatar da duka wasannin tseren mota ne kimanin watanni hudu baya.

    Sauran tseren da aka tabbatar za su gudana ya zuwa yanzu sun hadar da Hungary, Burtaniya, Spaniya, Belgium, da Kuma ta Italiya

    Ana sa ran za a fara British Grand Prix ranar 31 ga watan Yuli a kuma kammala ta a ranar 2 ga watan Agusta.

    Yayin gasar 'yan kallo ba za su halarci filayen wasan ba.

    Sama da matukan F1 4,000 alka yi wa gwajin cutar korona amma babu mai dauke da ita.

    Before the race started, drivers were pictured in t-shirts which read "End Racism" with some taking a knee.

    Kafin fara ko wacce gasa, matukan za su fito sanye da rigar da aka rubuta "End Racism" A kawo karshen wariyar launin fata wasu kuma za su durkusa kan gwiwowinsu.

  8. An binne kwarangwal din mutanen da suka yi yaƙin neman 'yanci a Aljeriya

    A ranar bikin samun 'yancin kanta, Aljeriya ta binne sauran kashushuwan mutum 24 da suka yi yakin kwatar 'yanci bayan an dawo da su gada kasar Faransa.

    Kwarangwal din mayakan da aka harbe kuma aka fille kawunansu yayin da Faransa ta fara mamaye kasar sama da shekara 150 an binne su ne a makabartar Shahidai ta El Alia da ke birnin Algiers.

    A ranar Lahadi an yi dogon layi a wajen gidan raya al'ada da ke birnin duk da ranar da ake fama da ita, inda buba kashushuwan nasu.

    Ana yiwa mamatan kallon wata nasara yaki da dakarun mulkin mallakar Faransa suka samu, kuma an ta ajiye kwarangwal din mutanen ne a gidan tarihi na Paris.

  9. Musulmai a Sri Lanka na kuka kan umarnin ƙona gawa

    Hukumomin Sri Lanka sun dage kan cewa sai dai a kona gawar duk wanda ya mutu dalilin cutar korona - wanda kuma hakan haramun ne a musulunce.

    Musulman kasar da basu da rinjaye sun ce ana fakewa da wannan annoba ana nuna musu wariya.

    A ranar 4 ga watan Mayu, aka kwantar da Fatima Rinoza wata mahaifiyar yara uku wadda ta fito daga al'ummar musulman kasar da basu da rinjaye, aka kwantar da ita a aibiti sakamakon zargin tana dauke da cutar korona.

    Fatima da ke zaune a Colombo babban birnin kasar ta yi ta fama da matsalar numfashi abin da hukumomin ke kallo a matsayin Covid-19.

    A ranar da aka kwantar da ita a asibiti, mijinta Mohamed Shafeek da 'ya'yanta suka fara fuskantar muzgunawa, in ji mijin.

    " 'Yan sanda da sojoji da wasu jami'ai suka iso kafar gidanmu, suka ce mu fita daga ciki suka fesa maganin kashe kwayoyin cuta a ko ina. Dukanmu mun tsorata amma ba su ce mana komi ba. Hatta yarinya 'yar wata uku sai da aka yi wa gwaji suka tisa keyarmu kamar kanuka har cibiyar killace mutane."

  10. Madrid za ta sayar da Rodriguez, Chelsea na tattaunawa da Willian

    Chelsea ta kara samun kwarin guiwar dauko dan wasan tsakiya na Jamus Kai Havertz daga Bayer Leverkusen bayan shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce ba zai iya sayen dan wasan ba.(Sun on Sunday)

    Inter Milan ta fara tattaunawa da Chelsea kan dan wasan baya Emerson Palmieri, mai shekara 25 daga Stamford Bridge.(Observer)

    Chelsea ta bude tattaunawa da dan wasan Brazil Willian, wanda Arsenal da Tottenham, ke zawarcinsa bayan dan wasan na gaba mai shekara 31 ya yi watsi da tayin wani kulob din China.(Goal)

  11. Ban yi nadamar yin sulhu da 'yan bindiga ba – Matawalle

    Gwamnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Bello Mohammed (Matawallen Maradun), ya ce ba ya nadamar matakin da ya dauka na yin sulhu da 'yan fashin dajin da suka addabi jihar.

    Gwamman ya bayyana haka ne a sanarwar da mai magana da yawunsa Zailani Bappa ya fitar ranar Lahadi.

    A cewarsa, sulhun shi ne hanyar da ta fi dacewa wajen kawo karshen hare-haren da 'yan fashin dajin suka kwashe shekara da shekaru suna kai wa a jihar da ma wasu jihohin arewa maso yammacin kasar.

    "Mun yi tattaunawar zaman lafiyar ce a matsayin hanyar gaskiya ta magance matsalolin jihar Zamfara kuma mun samu ci gaban da ba a yi tsammani ba a shekara daya da ta wuce", in ji Matawalle.

    Sai dai ya kara da cewa dole dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiyar jihar su kasance masu gaskiya idan ana son dorewar zaman lafiya.

    Wasu na ganin matakin gwamnan na yin sulhu ba shi da amfani ganin cewa 'yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na Zamfara.

    Ko a watan jiya, Mazauna garin Ruwan Tofa cikin ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara sun auka cikin tashin hankali bayan 'yan fashin daji sun yi wa yankinsu tsinke.

  12. Korona ta kashe sama da mutum 10,000 a Rasha

    Mutanen da suka mutu a Rasha sanadin cutar korona sun kai 10,161, kamar yadda jami'an lafiyar kasar suka bayyana a ranar Lahadi.

    Sun ce an samu sabbin masu dauke da cutar da suka kai 6,736 cikin awa 24, kuma wasu 134 sun mutu.

    Moscow wanda shi ne babban birnin kasar, cutar tafi kamari a cikinsa sama da ko ina.

  13. Yadda za a nemo sauran yaran da aka sace a Kano

    Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin zartarwa kan bincike da aka gudanar game da yaran da aka sace a jihar.

    Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya kaddamar da kwamitin domin zartar da shawarwarin da gwamitin binciken yadda aka sace yaran ya rubuta.

    A wata hira da BBC ta yi mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai a safiyar Lahadi ya ce, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa mai shari'a Wada Abubakar Umar Rano a matsayin shugaban kwamitin.

    Ya kara da cewa, mutanen da suka gabatar da bincike game da sace yaran sune aka kara nadawa cikin kwamitin zartarwar domin zartar da abubuwan da suka zayyana da in an bi za su iya kawo karshen faruwar irin wannan abu.

    Cikin shawarwarin da kwamitin binciken da aka kafa a watan Oktoba 2019 ya bayyana yadda za a iya nemo sauran yaran da ake zargin har yanzu ba akai ga ganowa ba.

    Da yake kaddamar da kwamitin gwamna Ganduje ya ce, " Matukar laifuka na karuwa to kuma aikinku zai ci gaba da karuwa, ba mason muga an yi watsi da wannan rahoto da kuka tattaro shi yasa muka sahale muku cewa ku zartar da shi."

    Cikin wannan kwamitin akwai jami'an 'yan sanda da masu fafutukar kare hakkin dan adam da kungiyoyin fararen hula da wakilan kungiyar malaman muslinci da na kungiyar kiristoci da dai sauransu.

    A watan Oktoban 2019 ne, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta ceto wasu kananan yara 'yan asalin jihar kano da shekarunsu suka kama daga biyu zuwa 10 wadanda aka yi garkuwa da su a jihar Anambra da ke kudancin Najeriya bayan an sace su daga Kano.

  14. Ana binciken 'yar takarar jam'iyyar adawa a Singapore

    'Yan sanda a Singapore na bincike kan wani bayani da daya daga cikin 'yan takarar birnin a zaben mai zuwa ta wallafa a shafin intanet, bayan ta yi jayayyar cewa 'yan sanda na da hannu cikin nuna wariyar launin fata da ake yi a kasar.

    Raessah Khan ta rubuta a 2018, kan zargin tsare shugabanin muslmai marasa rinjaye da ake yi da da kuma cin zarafinsu.

    Wata sanarwa da 'yan sandar suka fitar ta ce ana binciken Misis Khan kan rura gaba tsanin al'ummomi.

    'Yar shekara 26 na takara ne karkashin jam'iyyar Workers, wadda ke kalubatantar jam'iyyar PA mai mulki a zaben ranar juma'a.

  15. Korona ta yi ajalin tauraruwar fina-finan Masar Rajaa Al-Jeddawi

    Shahararriyar 'yar wasan kwaikwayon nan ta Masar Rajaa Al-Jeddawi ta mutu tana da shekara 82 bayan fama da ta yi da cutar korona.

    A watan Mayu ne Al-Jeddawi ta kamu da wannan cuta, wadda daga baya aka mayar da ita asibiti domin ci gaba da karbar magani.

    'Yarta Amira Moktar ce ta fara bayyana mutuwar mashahuriyar a shafinta na Facebook.

    Ta fito a wani shirin talabiji da ake kira "Oblivion Game", wanda kuma shi ne shirinta na karshe da ta yi, wanda ake haska wa a lokacin watan Ramadana.

    Bayan zama wata abar ko yi tsakanin 'yan uwanta, Rajaa Al-Jeddawi ta fara samun daukaka ne tun a farkon shekarun 1950.

    Na tsawon kusan shekara 60 da ta yi tana fim, ta yi fina-finai sun kusa 400, ta kuma rika gabatar da shirin talabijin tare da wasu daga cikin manyan masu nishadantarwa a Masar.

  16. Mexico ta zama ƙasa ta biyar da korona ta fi kashe mutane a duniya

    A hukumance sama da mutum 30,000 ne suka mutu a Mexico dalilin annobar korona, yayin da annobar ke ci gaba da yi wa kasar da ke ci gaba da yin barna a Latin Amurka.

    Ministan lafiya na kasar ya ce mutum 523 ne suka mutu a ranar Asabar, tare da wallafa addain wadanda suka mutu a kasar baki daya da suka kai 30,366.

    Kasar da ke da yawan mutane da suka kai miliyan 116 yanzu ita ce ta biyar a duniya da cutar ta fi kashe mutane, yanzu ma kuma ta wuce Faransa inda mutum 29,000 suka mutu sakamakon cutar.

    A ko wacce rana akan samun sabbin mutum 6,914 da ke kamuwa da cutar, wanda ya kai adadin masu cutar 252,165.

  17. Da alamun ƙara sanya dokar kulle a Afrika Ta Kudu

    Hukumomi a lardin Gauteng na Afrika Ta Kudu na yunkurin kara sanya dokar kulle biyo bayan karuwar masu kamuwa da cutar korona da ake fuskanta.

    Yankin wanda ya hadar da Johannesburg shi ne kashin bayan tattalin arzrikin kasar.

    Bandile Masuku wanda na daya ne daga cikin manyan jami'ai, shi ne ya nemi a kara dokar ko da ta mako biyu ce, domin dakatar da abin da ya kira yaduar da cutar ke yi kamar wutar daji a yankin.

    Akwai sama da kumu dubu 50 da ke da cutar a lardin Gauteng, wanda da yiwuwar ya maye gurbin yammacin birnin Cape wanda ya zama cibiyar annobar a kasar.

    Sai dai ba za a zartar da shawarar ba har sai mukarraban gwamnati sun rattaba hannu.

  18. COVID-19: Shugaban ƙasar Ghana ya killace kansa

    Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana cewa zai killace kansa tsawon kwana 14 bayan ya yi mu'amala da wani mutum da ke dauke da cutar korona.

    Gwamnaatin kasar ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ministan yada labaran kasar Kojo Oppong Nkrumah ya sanya wa hannu ranar Asabar.

    "Bisa shawarar likitoci, shugaban kasa, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, daga yau, 4 ga watan Yuli, 2020, zai killace kansa tsawon kwana 14 a matsayin wata hanyar kare kai daga COVID-19 kamar yadda ya kamata", in ji sanarwar.

    Ta kara da cewa: "Shugaban kasa ya ce ya dauki matakin ne bayan wani mutum da ke aiki da shi ya kamu da COVID-19 a yau."

  19. Barkanmu da safiyar Lahadi

    Buhari Muhammad Fagge ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.