An kashe mutum 30 yayin satar shanu

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labarai da rahotanni da muka wallafa a wannan shafin:

    • An kashe mutum hudu a wani harin bam a Somaliya
    • Korona ta sake ɓulla a Barcelona
    • Matar gwamnan Benue ta kamu da cutar korona
    • Gwamnan Ebonyi ya kamu da korona
    • Sri Lanka ta girke 'yan sanda don bin dokar sanya takunkumi
    • Ma'aikatan kamfanin Bajaj 250 sun kamu da korona
    • Bikin samun 'yancin kai: An gargaɗi Amurkawa kan wuce gona da iri
    • Za mu dakatar da gwajin hydroxychloroquine – WHO

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Yawan masu kamuwa da korona na ƙaruwa a kullum – WHO

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa an samu ƙaruwa a yawan masu kamuwa da cutar korona a faɗin duniya.

    Hukumar ta bayyana cewa a alƙaluman da aka tattara a sa'o'i 24 da suka gabata, an samu mutum 212,326 da suka kamu cutar korona idan aka kwatanta da alƙaluman da hukumar ta bayar a ranar 28 ga watan Yuni inda ta bayyana 189,077 sun kamu da cutar.

    Ƙasar Amurka da Brazil da Indiya ne kan gaba a wurin yawan waɗanda suka kamu da cutar ta korona.

    Ana ci gaba da samun mutuwa kamar yadda aka saba inda kusan mutum 5,000 ke mutuwa a kullum kamar yadda hukumar ta WHO ɗin ta bayyana.

  3. An tsinci gawar wani na kusa da mataimakiyar shugaban Argentina

    An tsinci gawar tsohon mai bai wa mataimakiyar shugaban kasar Argentina Cristina Kirchner a wani yanayi mai ɗaure kai.

    Marigayi Fabian Gutierrez ya taɓa zama sakataren Misis Kirchner a lokacin da take shugabancin kasar.

    Masu bincike sun ce an tsinci gawarsa ne a garin El Calafate da ke gundumar Santa Cruz.

    Mista Gutierrez na daga cikin shaidun da ake bai wa kariya, da ke da masaniya kan badaƙalar cin hanci da rashawa na miliyoyin daloli da ake zargin gwamnatin Misis Kirchner da yi.

  4. Za mu dakatar da gwajin hydroxychloroquine – WHO

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya ta duniya ta bayyana cewa za ta dakatar da gwajin da ake yi mai cike da ruɗani na maganin Maleriyan da Shugaba Trump ya yi iƙirarin yana maganin cutar korona.

    Hukumar WHO ta ce sakamakon binciken da suka yi kan magungunan hydroxychloroquine da na cutar HIV wato lopinavir da ritonavir ba su sa an samu raguwar mace-macen da ake samu ba a yayin da aka rinƙa ba masu dauƙe da cutar magungunan.

    Tun a farko a daina ba masu ɗauke da korona magungunan domin gudun wata illa, sai dai daga baya an ci gaba da basu bayan wani bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar suna maganin korona.

  5. An kashe mutum 30 yayin satar shanu

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Sudan ta Kudu sun tabbatar da kashe mutum 30 yayin wani hari da aka kai a jihar Jonglei da ke ƙasar a yunƙurin satar Shanu.

    Shugaban gudanarwa na yankin Elijah Manyok ya shaida cewa an shafe sama da sa'o'i biyar ana ɗauki ba daɗi a harin da aka kai a ranar Juma'a a "Duk Padiet Payam".

    Ya bayyana cewa sama da mutum 40 ne suka samu raunuka kuma an sace shanu dubbai.

    A wannan shekarar dai an samu hare-haren ramuwar gayya da aka kai tsakanin al'ummomin Murle da kuma Lou Nuer.

    Tsakanin watan Fabrairu zuwa Mayu na wannan shekara, an bayar da rahoton cewa an kashe sama da mutum 800 sakamakon rikici a yankin.

  6. Bikin samun 'yancin kai: An gargaɗi Amurkawa kan wuce gona da iri

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An buƙaci Amurkawa da su rage burin da suka cimmawa na murnar zagayowar samun 'yancin kai a yau 4 ga watan Yuli a daidai lokacin da ƙasar ke cikin matsalar cutar korona.

    Tuni aka rufe wuraren shaƙatawa na bakin teku, aka kuma soke batun fareti da wasan wuta da kuma dakatar da taron mutane da ake yi a duk shekara yayin murnar zagayowar ranar.

    An yi hakane domin guje wa ƙara bazuwar cutar ta korona a ƙasar ta Amurka.

    A ranar Juma'a, ƙasar ta bayyana cewa mutum 57,562 suka kamu da cutar korona.

    Sai dai duk da fargabar yaɗuwar cutar da Magajin Garin Washington yake yi, Shuagaba Trump na da niyyar haɗa wata ƙwarya-ƙwaryar liyafa a Fadar White House.

    Ana sa ran ɗaruruwan likitoci da malaman jinya waɗanda ke kan gaba wurin yaƙi da cutar a ƙasar za su halarci liyafar.

  7. Ma'aikatan kamfanin Bajaj 250 sun kamu da korona

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikata a kamfanin Bajaj Auto, wanda shi ne kamfanin da ke kan gaba wurin ƙera babura da Keke Napep a Indiya, sun buƙaci shugabannin kamfanin da su rufe shi na ɗan wani lokaci, sakamakon mutum 250 da suka kamu da cutar korona.

    Cikin waɗanda suka kamu, tuni biyu suka mutu. Shugabannin ƙungiyoyi a jihar Maharashtra sun ce mutane na tsoron zuwa wurin aiki. Kamfanin na da ma'aikata kusan dubu takwas.

    Kamfanin ya ce za a ci gaba da aiki tare da ɗaukar matakai na kariya.

    An kulle kamfanoni da dama bayan saka dokar kulle a fadin Indiya a ƙarshen watan Maris, kamfanonin sun shafe sama da watanni biyu a rufe.

    Sama da mutum 600,000 suka kamu da cutar korona a Indiya, kusan mutum dubu tara cutar ta kashe a halin yanzu a ƙasar.

  8. Shararriyar mai koyar da rawa a Bollywood ta rasu

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Saroj Khan, daya daga cikin shahararrun matan da ke koyar da rawa a Indiya ta rasu tana da shekara 71.

    Khan ta yi fice wajen koyar da rawa sama da shekara 40, ta kuma koyar da rawar wasu fitattun wakokin Indiya.

    Ta fara kaurin suna ne a farkon shekarun 1980, lokacin da ta yi aiki da manyan taurari irinsu Madhuri Dixit da Sridevi.

    Khan ta mutu sakamakon bugawar zuciya a wani asibiti a Mumbai, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

    An kwantar da ita a asibiti ne a watan jiya, bayan ta yi kukan yin nunfashi da kyar abin da yasa aka yi mata gwajin cutar korona kenan aka ga ba ta dauke da ita.

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Sri Lanka ta girke 'yan sanda don bin dokar sanya takunkumi

    epa

    Asalin hoton, EPA

    'Yan sanda a Sri Lanka sun ce an girke sama da jami'ai 2,000 a lardin yammacin kasar, ciki har da babban birninta Colombo, domin tabbatar da ana sanya takunkumi a bainar jama'a.

    Wasu daga cikin jami'an za su rika sanya kayan gida ne, domin tisa keyar wadanda suka ki bin dokar zuwa killace kansu na tsawon mako biyu.

    Sri Lanka ta yi kokarin shawo kan cutar ta hanyar sanya tsauraran matakan hana zirga-zirga.

    Akwai sama da mutum 2,000 da ke dauke da cutar a kasar inda kuma tuni 11 suka rasa rayukansu.

  10. Da gaske Pantami ya saya wa matansa uku gidaje a Abuja?

    @MCD/Facebook

    Asalin hoton, @MCD/Facebook

    Ma'aikatar sadarwa ta Najeriya ta musanta wasu labarai da ke ta yawo a kafafen sada zumunta na kasar cewa Minista Dakta Ali Isa Pantami ya sayawa matanshi uku gidaje a Abuja.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar Uwa Suleiman ta fitar ta ce wannan batu ba shi da tushe balle makama.

    Sanarwar ta ce "labarin jaridar intanet ta Sahara Reporters ta wallafa da ke zargin cewa ministan ya sayawa matansa uku gidajen a Abuja karya ne.

    Tun da ministan ya kama aiki a bai sayi gida ko daya ba, kuma gidan da yake zaune ciki ya kama shi ne tun a watan Janairun 2017, shekara biyu kenan gabanin ya kama aiki".

    sanarwar ta kuma ce sauran gidaje biyun da jaridar ta wallafa ba ma a san daga inda ta samo su ba.

    Bugu da kari ta yi kira ga al'ummar kasar da su yi watsi da wannan kokarin bata wa Minista Ali Pantami suna da ake kokarin yi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Hotunan shagunan gyaran kai da aka bude a Ingila

    Ana fuskantar dogayen layi a shagunan gyaran kai a Ingila.

    bbc
    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Matakin Ingila kan daina killace ‘yan wasu kasashe ‘shirme’ ne - Portugal

    Ministan harkokin wajen Portugal ya ce cire kasar da aka yi daga cikin jerin kasashen da za a killace wadanda suka shiga Ingila daga su "shirme" ne

    Augusto Santos Silva shaida wa BBC rashin sanya Portugal ciki "shirirta ce kuma rashin adalci ne".

    An wallafa jerin sunayen kasashen da shirin killacewar bai shafa ba a ranar Juma'a.

    Firaiminstan Burtaniya Boris Johnson ya ce za a ci gaba da killace mutane na tsawon mako biyu wadanda suka fito daga inda suka gaza shawo kan annobar.

    Sauran kasashen da aka cire daga cikin jerin, sun hadar da Amurka da China da kuma Sweden.

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

  13. Gwamnan Ebonyi ya kamu da korona

    EBONYI GOVERNMENT

    Asalin hoton, EBONYI GOVERNMENT

    Gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi ya kamu da cutar korona.

    Gwamnan ya bayyana hakanne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

    Sanarwar ta ce sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta yi ya nuna gwamnan na dauke da cutar. Haka zalika wasu daga cikin mukkarbansa.

    Gwamnan ya umarci mataimakinsa Kelechi Igwe ya ci gaba da jan ragamar yakin da ake yi da annobar a jihar.

    Umahi, wanda ya ce babu wasu alamu da ke nuna wa na ya kamu da cutar, ya nemi al'ummar jihar da su ci gaba da girmama ayyukana hukumar NCDC.

    Ya ce zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga gida ta hanyaar tattauanwa da mutane ta intanet.

    Ya zuwa yanzu jihar na da wadanda suka kamu da cutar 438.

    An sallami mutum 357 da suka warke yayin da 3 suka mutu.

  14. An kama mutumin da ya ci mutuncin mata a Saudiyya

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an 'yan sanda a Saudiyya sun kama wani mutum da ya zagi matan kasar, yana cewa suna yin abubuwan da suka saba ladubban kasar, na basu damar yin sana'a da kuma zuwa aiki wurare daban-daban.

    Kamar yadda jaridar Saudi Gazzete ta ruwaito cewa, mutumin na kalubantar aikin mata, kuma sukar da ya yi kan goyan bayan mata wajen sana'a a cikin al'umma, ya yi ta ne ta hanyar da hukumomi ba su ji dadi ba a tuwita, wanda kuma labarin ya yadu a kafafen sada zumunta.

    Ta hanyar bibiyar shafin da aka wallafa labarin, jami'an tsaro sun gano bayanansa.

    Mutumin dan asalin Saudiyya ne kuma shekarunsa sun kai 60 a yanzu haka yana karkashin kulawar jami'an tsaron kasar.

  15. Indiya na ƙara shiga hadarin annobar korona

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Sama da mutum dubu ashirin da biyu ne suka kamu da korona a Indiya, wanda shi ne adadi mafi girma da aka samu na masu kamuwa da cutar a ko wacce rana tun bayan sake bullar cutar a kasar

    Akwai fargabar wani ruwan sama mai hade da guguwa da za a iya samu a wasu yankunan kasar zai haifar da tsaiko game da aikin da ake yi na shawo kan annobar.

    Da kusan masu dauke da cutar dubu dari shida da hamsin, inda ta zama kasa ta hudu da ke da yawan masu cutar a duniya, kuma da yiwuwar ta zarce Rasha da Italiya a 'yan kwanakin masu zuwa.

    Yankin arewacin jihar Maharashtra na daga cikin inda cutar ta fi kamari kuma akan samun ruwa kamar da bakin kwarya a yankin.

    Sama da mutum 18,600 ne suka rasa rayukansu a Indiya sakamakon wannan annoba.

  16. Matar gwamnan Benue ta kamu da cutar korona

    FACEBOOK/EUNICE ORTOM

    Asalin hoton, FACEBOOK/EUNICE ORTOM

    Matar gwamnan Benue Dakta Eunice Ortom ta kamu da cutar korona.

    Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma'a Dakta Eunice ta ce ɗanta da kuma wani ma'aikacinta duka an gwada su an tabbatar suna dauke da cutar.

    Eunice ta ce za su killace kansu tare da bin ka'idojin da mahukunta a fannin lafiya suka shimfida musu.

    Haka kuma ta umarci mutanen da suka yi mu'amala da ita a baya-bayan nan da su killace kansu kuma a tabbatar an yi musu gwajin wannan cuta.

    Uwar gidan gwamnan ta ce kamuwa da cutar korona ba yana nufin mutuwa ba ne, ta ce da sannu za su warke nan ba da dadewa ba.

    A yanzu dai akwai mutum 97 da aka tabbatar suna dauke da wannan cuta a jihar ta Benue.

  17. Korona ta sake ɓulla a Barcelona

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a yankin Cataloniya da ke arewa maso gabacin Spaniya sun mayar da wasu mutum dubu dari biyu cikin dokar kulle saboda kara bullar cutar korona tsakaninsu.

    Mutane ba za su iya fita ko kuma shiga yankin sergia ba, wanda yake a arewacin Barcelona ba tare da izinin hukumomi ba.

    Yankunan da abin ya shafa sun hadar da Lieda. An kuma dauki matakan yin amfani da shingayen 'yansanda a lardin.

    Mutane sama da 10 ba su da damar haduwa wuri guda, a waje ko kuma a cikin gida.

    Catalonia na daya daga cikin wuraren da annobar korna ta yi wa mummunar barna a Spaniya, kuma ya fi kowanne yanki yawan masu dauke da cutar a halin da ake ciki.

  18. An kashe mutum hudu a wani harin bam a Somaliya

    BBC

    Akalla mutum hudu ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani harin bam da ya tarwatse a wani gidan cin abinci a birnin Baidoa da ke Somaliya.

    A Mogadishu babban birnin kasar kuwa, 'yan sanda sun ce sun harbe wani dan kunar bakin wake da ya nifo inda suke binciken ababan hawa a wata mota a wajen tashar jirgin ruwa. Daga baya kuma motar ta shi ta tarwatse.

    Rahotanni sun ce akalla mutane bakwai ne suka jikkata a harin.

    Gwamnatin Somaliya da ke samun goyan bayan kasashen duniya na ta yaki da kungiyar 'yan tada kayar baya ta al-Shabaab ne tun 2008.

  19. Ambaliyar ruwa ta tashi dubban mutane daga muhallansu a Japan

    getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Sama da mutum dubu biyu ne aka bai wa umarnin su tashi daga muhallansu da ke kudancin Japan, a wani mataki da hukumomi suka ce gargadi ne kan wata mabaliyar ruwa da ake tsammanin faruwarta.

    Mutum takwas ne suka ba ce a yankin Kumamoto, inda kogin Kuma ya sha yin ambaliya tare da mamaye yankunan da ke makwabtaka da shi.

    Kafafen yada labarai na kasar sun ce jami’an ceto ta fuskantar kiraye-kiraye daga al’umma na su taimaka musu.

    Firaiministan Japan Shinzo Abe ya ce za a aika sojoji dubu 10 yankin domin ba da agaji.

    Ana tsammanin samun wani ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin karshen mako.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkanmu da wannan lokaci da kuma sake ganin wata safiyar, kamar dai yadda aka saba.

    Yau ma muna dauke da labarai da rahotanni da suka shafi Najeriya da sauran kasashe makwanta a nahiyar Afrika, kama daga Nijar Kamaru Chadi da dai sauransu - har ma da sauran sassan duniya baki daya.

    Za ku iya samun labaran kai tsaye a wannan shafi da Facebook da tuwita da ma Instagram.

    ku kasance tare da Ni Buhari Muhammad Fagge a yinin na yau.