Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Somaliya na zargin Iran da yin su a ruwanta ba bisa ƙa'ida ba

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge

  1. COVID-19: Tattalin arzikin Kenya na tafiyar hawainiya, Charles Gitonga BBC News

    Tattalin arzikin Kenya ya samu tagomashi da kashi 4.9 cikin 100 a rubu'in farkon shekarar da muke ciki sai dai ci gaban tattalin arzikin ya fuskanci tafiyar hawainiya idan aka kwatanta da tagomashin kashi 5.5 cikin 100 da ya samu a rubu'in farko na bara.

    Ofishin kididdiga na Kenya ya ce kasar ta dan samu tsira daga tasirin annobar Covid-19 ban da bangaren karbar baki da annobar ta fi shafa.

    Hukumar kula da kididdiga ta Kenya ta ce bangaren kula da saukar bakin ya fuskanci koma-baya da kusan kashi 10 saboda soke tare da dakatar da tafiye-tafiye zuwa wasu kasashe da kuma rufe otal-otal da sauran wuraren bude ido yayin da kasar ke kara kaimi wajen hana bazuwar cutar korona.

    Kawayen Kenya ta fuskar kasuwanci irin su China da Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka sun fuskanci koma-baya sakamakon annobar korona.

    Bangaren noma da sufuri da na kasuwanci duk su ma sun kasance cikin wani hali saboda illar da cutar korona ta yi.

  2. Ƙasashen yankin Sahel za su ƙara ƙaimin kai hare-hare kan 'yan ta'adda

    Shugabannin kasashen duniya musamman na yankunan Sahel sun amince su ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren soji kan kungiyoyin da ke ikirarin Jihadi a yankin na Yammacin Afirka.

    Sun dauki matakin ne bayan taron kwana daya da suka gudanar ranar Talata a Nouakchott, babban birnin Mauritania, wanda shugabannin kasashen Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da Jamhuriyar Nijar, tare da shugabannin Faransa da Sufaniya suka halarta.

    An gudanar da taron ne da zummar samar da hanya kwakkwara ta dakile maharan da suka addabi yankin Sahel, bayan taron da aka yi a watan Janairu sakamakon koma-bayan da aka fuskanta a yaki da ta'addanci musamman bayan kisan sojin Faransa 13 wadanda aka harbo jirginsu mai saukar ungulu.

    Masu tayar da kayar baya sun matsa kai hare-hare a yankin a shekaru biyu da suka wuce, musamman a kan iyakar Nijar, Burkina Faso da Mali.

    Sanarwar bayan taron ta ce: "Shugabannin kasashen sun jaddada bukatar kara kaimi wajen fafarar 'yan ta'adda na gida da na waje ta kowanne bangare."

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce suna dab da yin nasara kan masu ikirarin jihadi.

  3. Barkanmu da warhaka

    Barkanmu da sake saduwa a wannan rana ta Laraba, wadda Hausawa kan ce Tabawa ranar samu.

    Nasidi Adamu Yahaya da Nabila Muktar Uba ne suke yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.