Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Somaliya na zargin Iran da yin su a ruwanta ba bisa ƙa'ida ba

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge

  1. Rufewa

    A nan ne muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a shafinnan kai tsaye - sai kuma gobe idon Allah ya kai mu.

    A madadin abokan aiki Nasidi Adamu da Nabeela Mukhtar ni Buhari Muhammad Fagge nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Meke faruwa a Peru?

    Peru na daga cikin kasashen da suka fara sanya tsattsaurar dokar kulle a Latin Amurka domin shawo kan yaduwar annobar korona - amma yanzu tana cikin jerin kasashe shida da vutar tafi kamari a duniya.

    Shugaban kasar Peru Martin Vizcarra ya ce, abubuwa suna gyaruwa amma a baya ya ce sakamakon kullen bai ba da sakamakon da aka yi tsammani ba.

    Me yasa cutar ta yi kamari a Peru?

    An fara dokar kulle a Peru a ranar 16 ga watan Maris - tun gabanin Burtaniya da wasu kasashen Turai - kuma dokar ta ci gaba har karshen watan Yuni.

    Yanzu dai ana samun raguwar rahotonnin masu kamuwa da cutar a kullum - sai dai har yanzu ana samun karuwar masu mutuwa sakamakon cutar.

  3. Uganda ta buɗe iyakokinta ga masu gudun hijira

    Ƙasar Uganda ta buɗe iyakarta da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo domin bai wa dubban mutanen da suka makale shiga ƙasar sakamakon bullar korona

    A kalla mutum 3,000 ne suka yi hijira a watan Mayu bayan rikicin ƙabilancin da aka yi a arewa maso gabashin lardin Ituri.

    Sai dai masu gudun hijirar sun kasa ƙetarawa zuwa Uganda domin neman mafaka sakamakon ƙasar ta kulle iyakokinta tun a watan Maris domin daƙile annobar korona.

    An cimma matsayar cewa 'yan gudun hijirar za a killace su na wani lokaci kafin su shiga cikin jama'a.

    Za a rike su ne na kwana 14 a sabuwar cibiyar killace mutane da ke da nisan mil takwas daga iyaka.

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya UNHCR ta ce za a rika yi musu gwaji domin tabbatar da babu wanda ke dauke da cutar.

    Wannan zai taimakawa hukumomin kasar wajen yanke yaushe ne za a mayar da mutanen sansani.

  4. Somaliya na zargin Iran da yin su a ruwanta ba bisa ƙa'ida ba

    Hukumomin Somaliya da ke lura da harkokin kamun kifi sun ce kasar ta shigar da korafinta a hukumance kan cewa jiragen ruwan Iran na yin su a cikin ruwanta ba bisa ka'ida ba.

    Gwamnatin Somaliya ta zargi jiragen ruwan da ke dauke da tutar Iran da shiga kasan ruwanta suna kama kifi nau'in tuna.

    Ministan su na kasar Abdullahi Bidhan ya shaida wa BBC cewa Somaliya ta gano sama da jirage 100 a ruwanta ta hanyar amfani da hotunan tauraron dan adam.

    A cewar ministan, Somaliya za ta nemi a biya ta diyya kan yin su a ruwanta ba bisa ka'ida ba na tsawon shekaru.

    Somaliya ta yanke huldar diflomasiyya da Iran tun a watan Janairun 2016, kuma ta kori jakadan Iran daga kasar 'yan kwanakin bayan da Saudiyya ta yanke huldar jakadanci da Iran.

    A baya kasar ta yi gargadi ga Pakistan da Iran kan yin su a ruwanta ba bisa ka'ida ba.

    Rahotanni na cewa kimanin jiragen Iran 200 aka kama a Somaliya da kuma ruwan Yemen.

  5. An yanke wa wasu mukarraban Boutaflika hukuncin gwamman shekaru a gidan yari

    Wata Kotu a Algeria ta yanke hukuncin dauri ga wasu daga cikin mukarraban tsohon shugaba AbdelAziz Boutaflika.

    Ali Haddad wanda daya ne daga cikin masu arziki a kasar, na daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin daurin bisa zargin cin hanci da rashawa.

    An yanke masa shekaru 18, yayin da aka yanke wa tsoffin shugabanni Ahmed Ouyahia da Abdelmalik Sellal daurin shekaru 12 kowannensu.

    An tursasa wa shugaba Boutaflika barin mulki a farkon shekarar 2019, bayan zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa da ta gudana.

  6. Ana zanga-zangar tir da Isra'ila

    Dubban mutane na gudanar da zanga-zanga a Gaza, domin nuna rashin amincewa da shirin Isra'ila na mamaye yankin gaɓar yamma da Kogin Jordan.

    Masu boren na ɗaga tutocin Falasdinawa, suna kuma yin Allah wadai da Shugaba Trump na Amurka kan goyon bayan da ya nuna ga shirin Isra'ilar.

    Shi ma Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya gargaɗi Isra'ila da ta watsar da shirin nata da ake hangen zai tayar da sabon rikici a yankin.

    Mista Jonhson ya ce abin da Isra'ila ke shirin yi ya saba wa dokar kasa da kasa, kuma kasarsa ba za ta aminta da shi ba.

    Wakilin BBC ya ce kusan dukkan kawayen Isra'ila sun ce shirin na mamayar da take yi ba da yawun bakinsu ba. Dama kuma kasar na cikin rudun siyasa''.

    To sai dai gwamnatin Benyamin Netanyahu ta ce a ranar Laraba ne za ta fara abin da ta tsara.

  7. Ko ƙauracewa Facebook zai rusa kamfanin?

    Kauracewa na da matukar tasiri - tamkar yadda Facebook ya gani.

    A karshen karni na 18, masu rajin bijire wa al'amura sun karfafa gwiwar mutanen Birtaniya, inda suka daina ta'ammali da abincin da bayi suka noma.

    Kuma ya yi tasiri. Kimanin mutane 300,000 suka daina sayen sukari, al'amarin da ya kara matsin lambar kawar da bauta.

    Fafutikar hana kiyayya ta 'Stop Hate for Profit campaign' ta baya-bayan nan da aka yi amfani da ita wajen bijire wa tsarin siyasa.

    Tana ikirarin cewa shafin sadarwar Facebook ba ya yin wani katabus don kawar da nuna wariyar launi da kiyaya daga kafar dandalinsa.

  8. Adadin masu korona a duniya ya zarce miliyan 10.5

    Yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a fadin duniya ya zuwa yanzu ya zarce miliyan 10 da rabi.

    Amurka ce dai ke da kaso mafi tsoka na masu cutar da fiye da miliyan 2, a cewar wata kididdiga daga jami'ar Johns Hopkins.

    Sama da mutum 127,000 ne dai suka mutu kawo wannan lokaci.

    Brazil kuma tana da kusan mutum miliyan daya da rabi da suke da cutar, kusan 60,000 kuma sun mutu.

  9. Zanga-zanga kan kisan mawakin siyasa a Ethiopia ta juye rikici, Kalkidan Yibeltal BBC News, Addis Ababa

    Kimanin mutum 50 sun mutu a yankin Oromia na kasar Habasha sakamakon wata zanga-zangar nuna fushi da kisan wani fitaccen mawaki a kasar.

    Getachew Balcha, mai magana da yawun yankin na Oromia ya ce wasu da dama sun jikkata sanadiyyar rikicin da ya barke yayin zanga-zangar sannan an lalata dukiya mai yawa.

    Rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana cewa an kashe dan sanda guda yayin tarzomar.

    An harbe mawaki Hachalu Hundessa ranar Lahadi da yamma a Addis Ababa, babban birnin kasar.

    Wakokinsa dai sun mayar da hankali kan sukar gwamnati.

    'Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu kan lamarin.

  10. Ku saurari Labaran Duniya Cikin Minti Daya Na BBC Hausa

  11. Mamaye West Bank saba manufar kasa ne – Boris Johnson

    Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya nemi Isra'ila da ta dakatar da shirinta na mamayar wani bangare na Gabar Yamma da Kogin Jordan, yana mai cewa hakan ba ya kan doka kuma sabanin manufar kasar ne.

    Takwaransa na Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanya yau Laraba a matsayin ranar da Isra'ila za ta fara jaddada ikonta kan yankunan Yahudawa da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Sai dai da alama wannan shiri ya fuskanci cikas.

    Falastinawa sun ce matakin zai rusa burinsu na samun tabbatacciyar kasa.

    Matakin na Isra'ila zai yi dai-dai da kudirin Shugaba Donald Trump na zaman lafiya - matakin da zai kawo karshen tsawon shekarun da aka shafe ana rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa da ya kaddamar cikin watan Janairu.

    Yahudawa 430,000 ne ke zaune a yankuna sama da 130 da aka gina, amma tun bayan da Isra'ila ta mamaye Yammacin Kogin Jordan a yakin Gabas Ta Tsakiya da aka yi a 1967.

    Ana yi wa yankunan kallon haramtattu karkashin dokokin kasashen duniya duk da Isra'ila - da Amurka karkashin mulkin Trump - sun musanta hakan.

  12. COVID-19: Uganda za ta bai wa dubban 'yan gudun hijra damar shiga kasar, Catherine Byaruhanga BBC News, Kampala

    A karshe dai gwamnatin Kampala ta amince ta bai wa dubban 'yan gudun hijrar da suka shiga halin tsaka mai wuya a yankin Ituri na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo DR wajen neman mafita a arewacin Uganda damar shiga kasar ta Uganda .

    Da farko sai an killace su na tsawon kwana 14 a sabuwar cibiyar da aka tanada mai nisan kilomita 13 daga kan iyakar kasar.

    Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce za a yi wa tawagar gwaji domin sanin ko suna dauke da cutar korona.

    Hakan kuma zai bai wa hukumomi damar yanke shawarar ko za a iya kai su sansanonin da aka tanada.

    Hukumomin ba da agaji sun yi magana kan kalubalen tabbatar da tsarin ba da tazara da tsafta a uraren da 'yan gudun hijrar ke zaune.

    Kimanin bakin hauren 52 ne suka kamu da cutar a Uganda daga cikin kusan mutum 900 da aka sanar suna dauke da cutar a kasar.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fargabar rahotannin karuwar rikici a jamhuriyar dimokradiyyar Congo inda mutum miliyan biyar suka rasa matsuguni.

  13. Kotu a India ta ba da damar bincikar 'yan sandan da suka kashe mutum biyu

    Wata kotu a India ta ba da izinin gudanar da bincike kan wasu jami'an 'yan sanda uku da ake zargi da azabtar da wasu mutum biyu har ta kai ga mutuwarsu.

    An mika batun hannun masu bincike na gwamnati duk da zargin yin rufa-rufa kan lamarin.

    P Jeyaraj mai shekara 58 da dansa Fenix dan shekara 38 sun mutu ranar 22 ga watan Yuni, kwana biyu bayan an sake su daga komar 'yan sanda.

    An kame su ne bisa zargin su da barin shagonsu a bude a lokacin da dokar hana fita ta fara aiki lokacin da ake kulle saboda korona.

    Jihar Tamil Nadu na karkashin dokar kulle domin hana bazuwar cutar korona.

    An dai garkame mutanen biyu a ofishin 'yan sanda na Sathankulam a Tutucorin, wani gari da ke kudancin jihar.

    Iyalan mamatan sun yi zargin an ci zarafin 'yan uwansu - kuma bayanan irin azabtarwar da aka yi musu ya janyo fushin jama'a har ma a kafafen sada zumunta lamarin da ya jawo hankalin al'ummar kasar ga lamarin.

  14. Za a gudanar da zaben gwamnan Ondo a Oktoba

    Hukumar zabe ta Najeriya ta ce za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo ranar 10 ga watan Oktobar bana.

    A cewar hukumar a shafinta na Twitter, "bisa tanadin sashe na 30 na dokar zabe ta 2010 da aka yi wa garambawul, an wallafa bayanan zaben na Ondo a harabar hukumar zabe ta jihar.

  15. Za a rarraba wa daliban Legas rediyo don karatu daga gida

    Gwamnatin Legas a Najeriya ta ce ta na shirin rarraba rediyo 10,000 ga dalibai domin karatu daga gida.

    Kwamishinar ilimi ta jihar Folashade Adefisayo ta ce jihar za ta yi hadin gwiwa da kamfanonin sadarwa wajen samar da intanet kyauta ga makarantu domin saukaka koyarwar ta intanet.

    A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sake bude makarantu ga daliban da ke ajin karshe a firamare da karama da kuma babbar sakandare domin ba su damar rubuta jarrabawar.

    Sai dai sauran daliban da ba a ajin karshe suke ba za su ci gaba da zama a gida.

    Gwamnatin ta Legas ta sanar da kudirin fara koyarwa ta rediyo domin tabbatar da cewa ba a bar daliban a baya ba a harkar karatunsu a wannan lokacin da ake fama da annobar korona.

    Ms Adefisayo ta ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafawa wannan tsari na karatu daga gida.

    Mai dakin gwamnan Legas Joke Sanwo-Olu a ranar Litinin ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta karbi tallafin rediyo:

  16. Kun san gwamna na shida da ya kamu da cutar korona a Najeriya?

    Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya ya kamu da cutar korona.

    Okowa ya bayyana yau Laraba cewa shi da mai dakinsa sun kamu da cutar.

    Kwana biyar da suka gabata ne aka bayyana cewa 'yar gwamnan ma ta kamu da korona.

    Okowa ne gwamna na shida da ya kamu da cutar korona a Najeriya.

    Gwamnonin sun hada da Nasir El-Rufai na Kaduna, Bala Mohammed na Bauchi, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia, da Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

  17. N-Power: Abin da ya sa aka keɓe wa 'yan majalisar dokoki guraben aiki

    Shugaban kwamitin majalisar wakilai ta Najeriya kan rage radadin talauci, AbdulLahi Barabe Salaame, ya ce ana kebe musu gurabe a hukumar samar da aiki ta N-Power ne saboda ba sa so a rika yin kashin dankali.

    Ya shaida wa BBC haka ne, a yayin da ofishin shugaban majalisar dattawan kasar ya musanta rahotannin cewa an kebe masa da wasu 'yan majalisar gurabun daukar matasa aiki karkashin shirin N-Power.

    A cewarsa, Shugaban Najeriya da ya bijiro da shirin na N Power, yana biyan bukatun siyasa ne saboda "damu da su mun yi alkawarin cewa cikin abin da za mu, yi za mu samar wa mutane aikin yi, za mu rage radadin talauci,"

    "Don haka kowa yana kamawa wani domin a tabbatar da alkawuran da muka yi."

    Sai dai ya ce "Tun bayan da muka fara aikinsu sun gano cewa akwai matsaloli da dama, "ba a samu abin ya kai kowane lungu da sako na Najeriya,"

    "Wasu wadanda ke da dama suna aiki da wurinn ko kuma suna da damar su kai ga ma'aikatan wurin sai su takaita (moriyar) abin ga wani sashe na kasa ko wata al'umma,"

    "Ko kuma a yi almundahana ciki inda za ka iske mutanen da ke ciki, ba duka ne na gaskiya ba, ko kuma mutanen da za a sa ba duka ne suke samun kudin nan ba."

    Abdullahi Salaame ya kara da cewa irin wannan kalubale ne ya sa suka ga dacewar samar da tsari da zai amfani kowane yanki na Najeriya.

  18. Ba zan gudanar da yakin neman zabe ba – Joe Biden

    Yayin da Amurka ke tunkarar lokacin zaben shugaban kasa da za a yi a watan Nuwamba, mai neman kujerar ta shugaban Amurkar Joe Biden ya sanar cewa ba zai gudanar da yakin neman zabe ba.

    "Zan bi ka'idojin likitoci - ba wai don kaina kadai ba har da kasar nan - kuma hakan na nufin ba zan yi gangamin yakin neman zabe ba," in ji tsohon mataimakin shugaban Amurka kuma mutumin da jam'iyyar Dimokrat ta tsayar domin yi mata takara.

    Wannan matakin nasa ya sha banban da matakin abokin karawarsa Shugaba Donald Trump wanda ya gudanar da yakin neman zabensa na farko a Tulsa a Oklahoma cikin watan da ya gabata duk da gargadin da ma'aikatan lafiya ke yi - sai dai ba a samu cukowar mutane ba a wajen gangamin kuma ya zuwa yanzu ba a sanar da kudirin gudanar da wani yakin neman zaben ba.

    Amurka dai ta na da sama da mutum 40,000 da suka kamu da korona cikin kwana biyar da suka gabata.

  19. Coronavirus: An buɗe masallatai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, By BBC Monitoring

    Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ta sanar da matakin bude masallatai da sauran wuraren ibada a fadin kasar daga yau Laraba bayan da aka kulle wuraren na tsawon makwanni saboda annobar korona, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar WAM.

    Sai dai kuma har yanzu matakin hana sallar Juma'a a masallatai na nan daram har sai illa Ma Sha Allahu , kamar yadda WAM ya rawaito.

    "Wuraren yin ibada a kan titi da masana'antu da ma'aikatu da tashoshin mota za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai baba ta gani.

    "Sabon matakin na nufin ba za a bar mutanen da shekarunsu suka ja da yara 'yan kasa da shekara 12 da kuma masu fama da matsalar numfashi zuwa masallatai da sauran wuraren ibada ba domin ba su kariya," a cewar hukumomi.

    Hukumomi a UAE sun bukaci jama'a su girmama matakan yayin zuwa sallah a masallatai tare da tabbatar da ba da tazarar a kalla mita uku tsakanin masallata, a kaucewa yin musabaha tare da sanya takunkumin fuska a ko da yaushe.

    A makon da ya gabata ne, hukumomin UAE suka dage dokar takaita zirga-zirga da aka sanya ta wani dan lokaci domin hana yaduwar korona.

    Ya zuwa 29 ga watan Yuni, kasar ta samu mutum 449 da suka kamu da korona, mutum 48,246 kenan jumulla a kasar har da 37,076 da suka warke da kuma 314 da suka mutu.

  20. Man Utd ba za ta biya sama da £50m kan Sancho ba, Tottenham za ta ɗauko Hojbjerg

    Manchester United ba za ta biya sama da £50m don sayo dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho ba. Sai dai Dortmund tana so ta sayar da dan wasan mai shekara 20 kan fiye da £100m.(Sky Sports)

    Arsenal na duba yiwuwar yin amfani da dan wasan Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 21, a wani bangare na musayar 'yan kwallon kafa a lokacin musayar da za a yi a bazara.(Mail)

    Tottenham tana da kwarin gwiwar dauko dan wasan Southampton da Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, a bazara amma sai ta soma sayar da wasu 'yan wasan tukuna.(Telegraph - subscription required)

    Manchester City tana shauƙin dauko dan wasan Bournemouth da Netherlands Nathan Ake. Amma za ta iya fuskantar kalubale daga Chelsea, wacce ita ma take son dauko dan wasan mai shekara 25.(Athletic - subscription required)