Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Masu cutar korona a duniya za su kai miliyan 10 zuwa makon gobe - WHO

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Me ya sa a bayar da cikakkun alƙaluman matan da ke kamuwa da korona?

    Wata ƙungiyar ba da agaji na gargaɗin cewa ba a bayar da cikakkun alƙaluman matan da ke kamuwa da cutar korona a wasu ƙasashe.

    Ƙungiyar mai suna International Rescue Committee na fargabar cewa ana barin mata a baya cikin shirye-shiryen gwajin korona a ƙasashen Somaliya da Yemen da kuma Afghanistan.

    Ta ce a ƙasashen ciki har da Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya fiye da kashi saba'in cikin 100 na mutanen da suka kamu da korona, maza ne, gagarumin yawa kan adadin da aka saba gani na kashi 51% a ƙasashen duniya.

    Gidauniyar ta ce hakan ba abu ne mai yiwuwa ba don kuwa matan sun fi yiwuwar kamuwa da ƙwayar cutar a irin waɗannan ƙasashe saboda su ne suka fi yin ayyukan kula da lafiya.

  2. Ana jiran sakamakon zaɓen Malawi

    Ana can ana ƙidaya ƙuri'u a Malawi bayan sake zaɓen shugaban ƙasar a jiya Talata.

    Akasari, an gudanar da zaɓuka lafiya, ko da yake, Shugaba Peter Mutharika ya zargi 'yan adawa da tarzoma a wuraren da suke da ƙarfi.

    An soke nasarar da ya samu da 'yar ƙanƙanuwar rata a zaɓen bara, bayan alƙalai sun yanke hukuncin cewa an jirkita sakamako.

    Shugaban mai ci na fuskantar gagarumin ƙalubale daga ƙawancen adawa ƙarƙashin jagorancin Lazarus Chakwera.

    Za a shafe tsawon kwanaki kafin sanar da sakamako.

  3. Barkanmu da wannan safiya

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.