Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Nijar ta yi asarar dala miliyan 50 a badakalar siyan makamai

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Makomar Henderson, Kurzawa, Meunier, Onana

    Golan Manchester United Dean Henderson, wanda yanzu haka yake zaman aro aSheffield United,zai sabunta kwangilarsa a Old Trafford ne kawai idan aka ba shi tabbacin cewa shi ne mutum na faro da za a rika sanya wa a wasa.Chelsea da Tottenham suna sha'awar daukar dan wasan na Ingila mai shekara 23.(Manchester Evening News)

    Paris St-Germain ta bai wa dan wasan Faransa Layvin Kurzawa, mai shekara 27, sabuwar kwangilar shekara hudu, a yayin da Arsenal da Chelsea suke zawarcinsa.(France Football - in French)

    Barcelona ta rage farashin da ta sanya kan Philippe Coutinho daga £100m zuwa £63m, ko da yake tsohuwar kungiyarsaLiverpoolba ta sha'awar sake ayen dan wasan mai shekara 28 dan kasar Brazil.(Mirror)

    Dan wasan Arsenal Matteo Guendouzi, mai shekara 21, ya harzuka dan wasanBrightonNeal Maupay, mai shekara 23, a kan albashinsu lokacin wasansu ranar Asabar, inda dukkan 'yan wasan na faransa biyu suka yi ta caar-baki a karshen wasan.(Mail)

  2. An samu dan majalisar Kenya da laifin zambar $3m

    An samu wani dan majalisar dokokin Kenya da laifin zambatar wata hukumar gwamnatin kasar $3m sakamakon wata kwangila da aka ba shi ta sayen masara domin bai wa mutanen da suka fada cikin fari.

    John Waluke zai iya rasa kujerarsa idan aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na fiye da wata shida.

    Abokiyar kasuwacinsa, Grace Wakhungu - mahaifiyar wani tsohon minista - ita ma an same ta da laifi.

    Mutanen biyu suna hannun 'yan sanda a Nairobi, babban birnin kasar inda suke jira a yanke musu hukunci ranar Alhamis.

    An bai wa kamfaninsu kudin bayan an zargi hukumar samar da abinci ta kasar da keta dka a shekarar 2004. Anshaida wa kotu cewa sun yi afani da takardun bge da kuma shaidu na karya.

  3. Ana fafatawa a zaben shugaban kasar Malawi

    An bude rumfunan zabe a Malawi inda al'ummar kasar suke zaɓen shugaban ƙasa a zagaye na biyu, wata biyar bayan soke sakamakon zaɓen bara da aka yi taƙaddama kansa.

    Shugaba Peter Mutharika zai fuskanci ƙawancen 'yan adawar jam'iyyun da suka ƙalubalanci nasararsa ta 2019, bayan ya lashe zaɓen da ƙasa da ƙuri'a dubu ɗari da sittin.

    Bayan rashin tabbacin siyasa da zanga-zanga tsawon watanni, kawunan al'ummar Malawi ya yi matuƙar rabuwa, tattalin arziƙin ƙasar na cikin mawuyacin hali, talauci da rashin aikin yi kuma sun ƙaru.

    Tuni aka sauya tsarin zaɓen ƙasar na da ƙyar na sha.

    Yanzu sai wanda ya yi nasara ya samu rinjayen ƙuri'u fiye da rabin waɗanda aka kaɗa.

  4. Barkanmu da warhaka

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Daga nan BBC Hausa muke yi muku fatan alheri.

    Da fatan za ku kasance da mu domin sanin halin da duniya ke ciki inda za mu kawo muku labarai da rahotanni musamman game da kasashen Najeriya da Nijar, da ma sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.