Rufewa
Anan ne muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku a wannan shafin, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu. Buhari Muhammad Fagge ne ke muku sallama.
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge
Anan ne muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku a wannan shafin, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu. Buhari Muhammad Fagge ne ke muku sallama.

Asalin hoton, Radio Mogadishu
Majalisar wakilan Somaliya ta amince da kudurin bai wa mata kashi 30 cikin 100 na duka majalisun dokokin kasar.
Majalisar wakilan kasar na da kujera 274 yayin da ta dattijai ke da kujeru 54.
Mata a kasar na ta koken rashin cikakken wakilci a siyasar kasar.
Amma wasu daga cikin mazajen da ke takara tare da sanya ran za su lashe wasu kujerun sun yi watsi da wannan sabuwar doka suna cewa mutane na da 'yancin zabar wadanda za su jagorance su.
Abdurrashin Duale Ahmed ya shaida wa BBC cewa wannan tauye hakkin bil'adama ne".
Kalibun ko wanne mamba ne ke zabar wanda zai wakilcesu.

Asalin hoton, AFP
Masu zanga-zangar rashin aiki a Tunisia na kara fusata, bayan taho mu gama da suka yi da 'yan sanda a rana ta biyu ta zanga-zanagr a kudacin birnin Tataouine.
MAsu zanga-zangar na bukatar gwamnati ta cika alkawarinta na samar da aiki a yankin.
Rashin aikin yi ya kai kaso 30 cikin 100 - wanda wannan ne abu mafi muni da kasar ta taba gani.
Kuma suna neman a saki shugaban wannan tafiyar ta su, Tarek Haddad, wanda tuni jami'an tsaro ke tsare da shi.
Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma Ecowas, ta goyi bayan takarar Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar kungiyar cinikayya ta duniya.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar wadda ministan harkokin wajen Najeriya Geoffery Onyeama ya wallafa a shafinsa na tuwita, ta ce Dakta Ngozi za ta jagoranci kungiyar ne daga shekarar 2021 zuwa 2025 idan aka zabe ta.
Sanarwar ta kara da cewa Najeriya ce ta mika sunan 'yar takarar bayan la'akari da aka yi da kwarewarta a fannin ilimi da kuma bangaren aiki kan abin da ya shafi tattalin arzikin Najeriya da zamanta ministar harkokin kudi a 2003 da kuma 2011.
Shugabannin kungiyar cinikayya ta duniya sun lura cewa babu wani dan Afrika da ya taba jagorantar kungiyar tun bayan kafa ta a ranar 1 ga watan Janairun 1995, kamar yadda sanarwar ta zayyana.
Shugaban kungiyar kasuwanci ta cikin sanarwar ya ce an bude karbar sunayen 'yan takarar ne daga ranar 8 ga watan Yuni da muke ciki kuma za a rufe karbar a ranar 8 ga watan Yuli mai kamawa.
Kungiyar Ecowas ko kuma Cedeao ta yi kira ga sauran kasashen Afrika da wadanda ma ba na nahiyar ba da su goyi bayan takarar tata.
Misis Okonjo-Iweala ita ce mace ta farko da ta fara zama ministar kudin Najeiya da kuma ministar harkokin waje a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2006.
Tsohuwar ministar ta taba yin aiki da Bankin Duniya, inda ta shafe fiye da shekara 20 a hedikwatarsa da ke birnin New York na Amurka.
Ko a kwanakin baya ma sai da kamfanin sada zumunta na tuwita ya nada Dakta Ngozi a matsayin daya daga cikin manyan daraktocinsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, ANI
Kotun koli a India ta yi amai ta lashe inda ta ba da damar gudanar da wani gangamin al'ada da aka shirya a gobe.
Makon da ya gabata ne kotun ta dakatar da gudanar da bikin saboda fargabar bazuwar cutar Korona.
A yanzu kotun ta ce ya rage ga masu shirya bikin al'adar na Rath Yatra su duba yiwuwar yi ko barinsa.
Dama gwamnati ta ba da izinin gudanar da bikin wanda dimbin jama'a ke taruwa, inda ta kafa hujja cewa yana da alaka da addini.

Asalin hoton, Reuters
Shahararren dan Tennis dinnan na duniya Novak Djokovic na shan suka bayan da mutane hudu suka kamu da cutar Korona a gasar da ya shirya.
Djokovic ne na daya a wasan Tennis a duniya, kuma ya shirya wasanne da nufin bai wa yan wasa damar motsa jiki, bayan dadewa ba su buga wasa ba saboda annobar Korona.
Daga cikin wadanda suka kamu akwai yan wasa biyu wato Grigor Dimitrov da kuma Borna Coric.
Sauran kuma masu horar da yan wasa ne da kawo yanzu ba a bayyana sunayensu ba.
An lura cewa ana rungumar juna da kuma gaisawa a tsakanin 'yan wasa, wanda hakan ya nuna ba a kiyaye ba da tazara ba tsakani.

Asalin hoton, AFP
Mutane ashirin da bakwai ne rahotanni suka ruwaito cewa yan bindiga sunyi garkuwa da su a arewacin Mozambique.
Tuni an tsinci gawar shida daga cikinsu a kauyen Macomia dukansu maza.
Da yawa daga cikin wadanda aka sacen mata ne, kuma dama ana zargin Al-Shabaab da anfani da matan wurin dafa musu abinci da sauran aikace-aikace.
Daga shekarar 2017 zuwa yanzu mayaka sun hallaka sama da mutun 700.

Asalin hoton, APF/GETTY
Dubban jama'a ne aka bari cirko cirko a Afrika Ta Kudu, bayan da direbobin tasi suka tsunduma yajin aiki.
Direbobin kananan motocin kasuwar sun datse manyan hanyoyin da ke shiga biranen Johannesburg da Pretoria duk da girke yan sanda da aka yi.
Bukatarsu dai itace gwamnati ta tallafa musu, bayan da suka ce dokar kulle da ta biyo bayan bullar cutar Korona ta sa abin da suke samu ya yi kasa.
A baya gwamnati ta yi musu tayin tallafin dala 300 ga ko wanne dan tasi da ke da rajista, sai dai sun yi watsi da batun.

Asalin hoton, EPA
Gwamnatin Afghanistan ta bayyana makon da ya gabata a matsayin mafi muni ga jami'an tsaron kasar a cikin kusan shekaru 20.
Mai magana da yawun hukumar tsaro Javid Faisal ya zargi kungiyar Taliban da kashe jami'an tsaro kusan dari uku a hare hare sama da dari hudu da aka kai.
Ya kara da cewa an jikkata wasu dari biyar da hamsin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa irin yadda hare hare suka zafafa ya nuna cewa Taliban ba da gaske ta keyi ba kan batun samar da tsaro a Afghanistan.
To sai dai a nata bangaren kungiyar Taliban ta ce sanarwar gwamnatin wani wata makarkashiya ce ta lalata yarjejeniyar zaman lafiya da ake kokarin kullawa.
Duka wadannan kalamai na zuwa yayin da ake shirin haduwa tsakanin wakilan bangaroran biyu don tattauna batun zaman lafiyar.

Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin duba wata na Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce watan Shawwal ya cika kwana 30 saboda ba a ga sabon watan Zulki'ida ba ranar Lahadi.
Sakon da kwamitin ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin ya ce "Kwamitin Majalisar Sarkin Musulmi kan addinin Musulunci da hadin gwiwar kwamitin kasa na duban ba su samu rahoto ganin watan Zulk'ida 1441 AH ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni daidai da 29 ga watan Shawwal daga kwamitocin neman wata na fadin kasar ba.
Don haka yau Litinin 22 ga watan Yuni ta yi daidai da ranar 30 ga watan Shawwal 1441 AH".
A cewar sanarwar, ranar Talata 23 ga watan Yunin 2020 ta yi daidai da 1 ga watan Zulki'da 1441 AH.
Ta kara da cewa Sarkin Musulmi ya amince da wannan sanarwa kuma za a yi aiki da ita.
Batun ganin wata ya dade yana jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya musaman a lokacin azumin Ramadana.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadi kan rashin shugabanci a yayin da ake tsaka da annobar korona.
"Duniya tana cikin halin da take bukatar hadin kai na kasa da ma na duniya. Siyasantar da annobar korona ya ta'azzara yaduwarta," a cewar shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, a wani taro ta intanet da ya yi da ma'aikatan lafiya ita ce matsalarmu."
WHO ta kara da cewa cutar tana ci gaba da yaduwa kuma za a ga tasirin da ta yi kan tattalin arziki da sauran fannonin rayuwa shekaru aru-aru masu zuwa.
Mutum kusan miliyan tara cutar ta kama kuma ta yi ajalin kusan mutum 470,000.
'Yan wasa biyar na tawagar kwallon kafar Serbia, Red Star Belgrade, sun harbu da cutar korona.
Sanawar da kungiyar kwallon kafar ta fitar ranar Litinin na zuwa ne bayan tawagar ta fafata a gasa da dama a kusa da dandazon 'yan kallo.
Sauran kungiyoyin kwallon kafa – ciki har da gasar Premier ta Ingila – sun yanke shawarar komawa wasa ba tare da 'yan kallo ba.
Da farko gwamnatin Serbia ta dauki irin wannan mataki, amma a farkon watan nan, ta amince a yi wasa a gaban 'yan kallo.
Akalla 'yan wasa hudu cikin biyar da ska kamu da cutar ba su yi wasan da aka yi ranar Asabar ba, saboda sun ji alamun kamuwa da cutar, in ji kungiyar.

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, DELE MOMODU/TWITTER
Ma'aikatar wajen Ghana ta soma bincike kan rusa wani gina da ke ofishin jakdancin Najeriya da ke Accra, babban birnin kasar.
Ranar Asabar Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya yi tir da hare-hare biyu da wasu mutane da ba a san ko su wa ye ba suka kai a ofishin jakadancin kasar.
Ministan ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, inda ya bukaci Ghana ta dauki matakin gaggawa domin gano mutanen da suka yi wannan aika-aika.
Mataimakin ministan wajen Ghana Charles Owiredu, ya shaida wa BBC Pidgin cewa "abin da ya faru abin takaici ne; Bai kamata mutum ya shiga ofishin jakadanci ba ba tare da an gayyace shi ba kuma Ghana ce take da alhakin kare lafiyar ma'aikatan difilomasiyya
A duniya baki daya, maza sun fi mata mutuwa sanadin cutar korona.
Misali, a Italiya da China da Amurka, cutar korona ta kama maza fiye da mata, kuma ta fi kashe mazan.
Sabra Klein, wata masaniya kan irin bambancin da ake da shi game da yadda kwayar cuta mai yaduwa take kama maza da mata, a Jami'ar Johns Hopkins Bloomberg, ta ce "kasancewar mutum namiji zai zama mai kasadar kamuwa da korona kamar yadda tsoho yake da irin wannan kasada."
Sai dai wani abin mamaki yana faruwa a India.
Wani sabon bincike na masana kimiyyar India da Amurka ya nuna cewa ko da yake maza sun fi hatsarin kamuwa da cutar, mata sun fi hatsarin mutuwa sanadin cutar.

Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Francis ya ce ya kamata a rika fadar gaskiya sannan a guji munafunci a yakin da ake yi da cutar korona.
A wani tsakure kan hirar da ya yi da marubucin tarihinsa,Fafaroman ya ce: "Wannan annobar tana shafar dukkanmu, mai kudi da talaka kuma tana fito da munafukai.
"Na damu da yadda wasu 'yan siyasa suke munafunci a game da wannan annoba.
"Akwai matsalar yunwa a duniya, amma su wane ne suke kirkirar makamai.
"Wannan lokaci ne da ya kamata mu daina munafunci. Ya kamata mu fadi gaskiya."

Asalin hoton, PA Media
Chelsea za ta iya mayar da hankalinta kan dan wasanParis St-Germaindan kasar Faransa Layvin Kurzawa, mai shekara 27, idan suka gaza dauko dan wasan Leicester dan kasar Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23.(Express)
Barcelona ta soma tattaunawa a kan sabunta kwangilar shekara biyu da dan wasan Argentina Lionel Messi, wanda zai shekara 33 ranar Laraba.(Marca)
Juventus ta shirya domin bai waWolves'yan wasan Italiya Daniele Rugani, mai shekara 25, da Federico Bernardeschi, mai shekara a yunkurin da take yi na rage tsadar sayen dan wasan Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29.(Tuttosport)
Liverpool na son sayo dan wasanNapolida Senegal Kalidou Koulibaly a kan £54m. Manchester United da Chelsea ma suna zawarcin dan kwalln mai shekara 29.(Corriere dello Sport)

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na cewa an kashe akalla mutum 19 a gabashin Jamhuriyar dimokradiyyar Kongo, a harin da aka dora alhakinsa kan 'yan tawayen kasar.
Jami'ai sun ce an gano gawarakin mutum tara da suka bata ranar Juma'a a Arewacin Kivu.
A yakin Ituri da ke makwabtaka, 'yan tawayen Allied Democratic Forces ko ADF sun ka hari a kauyen Bukaka ranar Asabar inda suka kashe mutum goma.
An dora alhakin kashe-kashen fiye da mutum dari biyar kan The ADF - wacce ba ta da wata manufa ta siyasa- a watanni biyar zuwa yanzu, domin yin ramuwa kan dirar mikiyar da sojoji suka yi musu.

Asalin hoton, Getty Images
Likitocin Najeriya sun janye daga yajin aikin da suka mako daya suna yi domin nuna rashin jin dadinsu kan rashin isasshen albashi da kayan kariya na yaki da cutar korona.
Kungiyar likitoci ta National Association of Resident Doctors (Nard), wacce ke wakiltar kashi 40 na likitocin kasar, ta ce ta janye daga yajin aikin ne bayan gwamnati ta amince ta biya mata bukatunta, a cewar sanar da kungiyar ta fitar ranar Litinin.
Sai dai ta ce yajin aikin bai shafi yada take gudanar da aikin yaki da cutar korona ba.
Ta kara da cewa tuni gwamnati ta soma biyan bukatunta, wadanda suka hada da dawo a likitocin Asibitin Koyara na Jami'ar Jos da kuma ta umarci babban likitan asibitin ya biya albashinsu da aka rike.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya ce za a shawo kan rikicin jam'iyyar ne kawai idan aka yi biyayya ga tanade-tanaden kundin tarin mulkinta.
Ya bayyana haka ne bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Lahadi.
A sakon da Ahmad Lawan ya wallafa bayan ganawar, ya ce "na yi amannar dole mu duba kundin tsarin mulkin jam'iyyarmu sannan mu ga yada za mu magance wadannan masaloli. Kuma a yayn da muke yin wannan duba, ya zama wajibi mu hana rikicin ya ci gaba da faruwa.
Ya kara da cewa "ina so na tabbatarwa dukkan mambobin jam'iyyarmu cewa da yardar Allah, nan da kwanaki kadan, za mu ga yadda za a dauki matakin shawo kan rikicin".
Rikicin APC ya sake tabarbarewa ne bayan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya fice daga jam'iyyar sakamakon takaddamar da ke tsakaninsa da shugabanta da kotu ta dakatar, Mr Adams Oshiomhole.
Hakan ya sa jam'iyyar ta nada tsohon gwamnan jihar Oyo wanda shi ne shugabanta na yankin kudancin kasar, Abiola Ajimobi, a matsayin shugaban riƙo na jam'iyyar APC.
Amma wani fitaccen dan jam'iyyar Victor Giadom ya samu izini daga kotu cewa ya shugabanci jam'iyyar a matsayin riƙo, lamarin da masu fashin bakin siyasa suka ce zai hana jam'iyyar lashe zaben 2023 idan ba ta dinke barakar ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Barkanmu da safiyar Litinin. Nasidi Adamu Yahaya ne yake tare da ku a wannan lokaci.
Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da ake ciki a sassan duniya.
Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu.