An gudanar da zanga-zangar neman shugaban Mali ya sauka daga mukaminsa
Dubban masu zanga-zanga a Mali sun taru a babban birnin kasar Bamako, suna kira da shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa.
Limamin nan mai ra'ayin rikau Mahmoud Dicko ne ya jagoranci zanga-zangar tare da goyan bayan gamayyar 'yan adawa, suna bukatar kawo sauyi a tsarin siyasar kasar da kuma tattalain arzikinta.
Suna bukatar shugaba Ibrahim Boubacar Keïta da ya yi murabus saboda karuwar aikin masu tsattsauran ra'ayin addini da kuma karuwar rikicin kabilanci.
Sai dai shugaban ya nemi a sake kafa wata gwamnatin gambiza da mambobin jam'iyyun adawa.
Amma duk da tattaunawar neman mafitar da aka yi a farkon makon nan, an gudanar da zanga-zangar kamar yadda aka tsara.
Mista Keita mai shakara 75, an fara zabar shi ne a matsayin shugaban kasar a 2013. Ya kuma koma zagaye na biyu na milkinsa a 2018.
Sai dai a bayan nan yana fama da matsin lamba saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar, ga cutar korona, ga kuma yajin aikin malaman makarantu.
An kuma fara fuskantar rikicin siyasa da ya bullo kai bayan zaben 'yan majalisa a kasar da ya gudana mai cike da rikici a watan Maris, da kuma zargin cin hanci da rashawa.