Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Dalilin 'yan sanda na kama shugaban waɗanda suka yi zanga-zanga a Katsina

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Buhari Muhammad Fagge

  1. Sabuwar dambarwa a APC a yayin da Giadom ya ce shi ne shugaban riko

    An shiga rudu a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya bayan da mataimakin babban sakataren jam’iyyar na kasa, Victor Giadom ya bayyana kansaa matsayin sabon shugaban jam’iyyar na riko.

    Matakin Mr Giadom ya ci karo da sanarwar da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta fitar inda ta bayyana, tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi a matsayin shugaban jam’iyyar na riko.

    Jam’iyyar APC a cikin wata sanarwa da kakakinta Malam Lanre Issa-Onilu ya fitar, ta ce Ajimobi ne zai dare kujerar shugabancin jam’iyyar.

    Rahotanni sun ce Mr Giadom ya yi jawabi ga manema labarai a shalkwatar jam’iyyar na kasa a Abuja yau da safe, inda kuma ya ce ya soke wasu daga cikin hukunce-hukunce da Oshimole ya dauka.

    Wannan dambarwar na zuwa ne kasa da kwana guda bayan kotun daukaka kara a Abuja tatabbatar da dakatar da Adams Oshiomole a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

  2. COVID-19: Har yanzu Yarima Charles ba ya jin ƙamshi da ɗandano

    Har yanzu Yarima Charles ba ya jin ƙamshi da ɗandano bayan ya warke daga cutar korona wacce ta kama shi a watan Maris.

    Ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara ga wani likita.

    An gano cewa Yariman, mai shekara 71, ya kamu da Covid-19 gabanin barkewarta bayan ya yi fama da kananan alamomin cutar.

    Ana kallon rashin jin ƙamshi a matsayin daya daga cikin manyan alamomin cutar.

  3. Shugaban kasar Honduras ya kamu da cutar korona

    Shugaban kasar Honduras Juan Orlando Hernández ya ce shi da mai dakinsa da ma'aikatansa biyu sun kamu da cutar korona.

    A jawabin da ya yi wa 'yan kasar ta gidan talbijin, ya ce ya soma jin alamar rashin lafiya a karshen makon jiya amma sai ranar Talata aka tabbatar ya kamu da cutar.

    Mr. Hernández ya ce yana samun sauki kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga gida.

    “Ina da kuzarin da zan iya ci gaba da aiki domin mu kawar da wannan annobar,” in ji shi. “Za mu yi galaba a kanta. Mun yi imani da Allah, da likitocin Honduras da kuma magunguna.”

    Mutum 9,600 sun kamu da cutar korona a Honduras inda ta yi ajalin mutum 330, a cewar Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, wacce ke bin diddigin cutar.

    A makon jiya aka sake bude kasuwanni a kasar bayan an rufe su kusan wata uku domin dakile yaduwar cutar.

  4. An kama shugaban ƙungiyoyin da suka yi zanga-zanga a Katsina

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama Nastura Ashir Sharif, shugaban kwamitin amintattu na Coalition of Northern Groups (CNG), wadanda suka yi zanga-zanga a birnin Katsina da ke arewacin kasar inda suka yi kira a dauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman, ya aike wa BBC ranar Laraba ta ce yanzu haka Ashir Sharif yana tsare a hedikwatar rundunar da ke Abuja, babban birnin kasar.

    Ya kara da cewa an kama shi ne ranar Talata da tsakar rana bayan sun kammala zanga-zangar.

    Kungiyar "CNG ta yi matukar kaduwa ganin cewa gwamnatin da ke ikirarin kare mulkin dimokradiyya za ta iya hantarar mutanen da suka fito don kare nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu", in ji Abdul-Azeez Suleiman.

    Masu zanga-zangar, mai taken#ArewaIsBleedinga turance, wato 'Jini yana kwarara a Arewa', sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.

    Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin kasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen.

  5. An kama wani mutum bayan samun gawar budurwa a rataye

    'Yan sanda a Afirka ta Kudu sun kama wani mutum mai shekara 31 bisa zargin hannu a kisan wata budurwa mai shekara 28, Tshegofatso Pule.

    Za a gurfanar da mutumin a gaban kotu ranar Laraba domin tuhumarsa kan zargin kisan budurwar.

    A makon jiya masu mu'amala da shafin Twitter a Afirka ta Kudu sun yi amfani da maudu'i mai taken #JusticeForTshego a turance, wato a yi wa Tsego adalci, domin matsa lamba ga 'yan sanda su gano wadanda suka kashe ta.

    An gano gawarta rataye a wata bishiya bayan an sassara ta a birnin Johannesburg.

    Jaridar Sowetan ta bayar da labarin cewa Ms Pule ta ɓata a makon shekaranjiya amma daga bisani an gano gawarta a rataye.

  6. Manchester United tana son ɗauko Willian, Everton tana zawarcin Allan

    Manchester United ta tuntubi wakilin Willian domin tattaunawa kan karbo dan wasan mai shekara 31 dan kasar Brazil, wanda kwangilarsa za a kare a Chelsea wannan bazarar.(France Football - in French)

    Kocin Everton Carlo Ancelotti ya soma tattaunawa da dan wasan tsohuwar kungiyarsa Napoli Allan dan shekara 29, dan kasar Portugal.(Express)

    Kazalika Ancelotti ya yi yunkurin dauko dan wasan Paris St-Germain da Brazil mai shekara 35 Thiago Silva da zarar kwangilarsa ta kare a bazarar nan.(Express)

    Dangantakar Gareth Bale da kocin Real Madrid Zinedine Zidane ta yi tsamin da ba za ta gyaru ba, ko da yake dan wasan na Wales mai shekara 30 yana cike da farin ciki a kungiyar ta Spaniya.(Marca)

  7. Ganduje ya yi watsi da rahoton kwamitin Buhari kan mace-macen Kano

    Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan.

    A wata sanarwa da ya fitar, Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan mace-mace ya gano cewa kusan kashi kashi goma sha shida cikin dari ne suka mutu sanadin korona.

    Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: "Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9... ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona."

    A makon jiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.

    A watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kwamitin na musamman zuwa Kano don gano sanadin yawaitar mace-macen, sannan ya sanya dokar hana fita ko da yake daga bisani Gwamna Ganduje ya kyale mutane su ci gaba da fita a wasu ranaku.

  8. Abin da ya sa aka dakatar da bude wuraren ibada a Lagos

    Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriyata ta ce ta dage lokacin da za a bude majami'u da masallatai har zuwa wani lokaci a nan gaba.

    Gwamnan jihar Babajide Olusola Sanwo-Olu ya ce an yanke hukuncin hakan ne sakamakon yadda ake samun karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar korona a jihar.

    A baya dai gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar bude masallatai da majami'u a ranakun 19 da 21 na wanann wata.

    A wani taron manema labarai da gwamnan ya yi ya nuna matakin dakatar da budewar wuraren ibadun nan take na da nasaba da yadda ake kara samun karuwar wadanda ke harbuwa da cutar coronavirus a jihar.

  9. Barka da warhaka

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Daga nan BBC Hausa muke yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.