Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban APC

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge and Halima Umar Saleh

  1. Uganda ta hana yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen ƙasar

    Hukumar zabe ta Uganda ta haramta yakin neman zaben da ake tara mutane a zahiri tare da bai wa 'yan takara shawara da su gudanar da yakin nasu ta kafafen sadarwa.

    Hukumar zaben ta ce kasar za ta kudanar da babban zabenta ne a watan Junairun 2021, amma za a sanya tsauraran matakai domin kare lafiyar masu zaben daga kamuwa da korona.

    Sanya takunkumi da wanke hannu da ba da tazara abubuwa ne da za su zama wajibi a rumfunan zabe a ranar.

    Hukumar ta matse lokacin gudanar da zaben cikin har da lokacin fitar da dan takara, zuwa kasa da wata shida.

    'Yan kasar za su zabi sabon shugabansu da mambobin majalisar dokoki da sauran shugabannin a yayin zaben.

    Shugaba Yuweri Museveni, wanda ya jagoranci kasar karo biyar, na da damar kara tsayawa takara amma har yanzu bai bayyana aniyarsa ta yi ko sabanin hakan.

  2. An kori Janar na sojan Najeriya Hakeem Otiki daga aiki

    Wata kotun rundunar sojin Najeriya ta kama Manjo Janar Hakeem Oladapo Otiki, wanda zai yi ritaya baɗi, da laifuka biyar sannan ta bayar da umarni a rage masa mukami kana a kore shi daga aiki cikin wulakanci.

    Otiki shi ne Kwamandan runduna ta 8 ta sojin Najeriya da ke Sokoto a watan Yulin July 2019 lokacin da ya aika sojoji biyar da ke aiki tare da shi su kai kudi daga Sokoto zuwa Abuja ta hanyar Kaduna amma kudin suka bata.

    Kotun, wacce shugaban tsare-tsare na rundunar sojin, Laftanar Janar Lamidi Adeosun ya jagoranta, ta kama Otiki da laifin rashin biyayya ga dokokin soji, da satar kudin jama'a da karkatar da su da kuma shiga harkokin kasuwanci.

    Kotun sojin ta yanke masa hukuncin da suka hada da: kora daga aiki a wulakance, rage masa mukami daga Manjo Janar zuwa Birgediya Janar da kuma jan kunnensa.

    Kotu ta nemi ya koma da kudin da aka gano a wurinsa wadanda suka kai N135.8m da $6,600. Ta bukaci ya nemo N150m da bai fito da su ba sannan ya mayar cikin lalitar sojin kasar.

    Za a zartar da wadannan hukunce-hukunce ne idan Majalisar Soji ta amince da su.

  3. Pakistan ta kara tsaurara dokar kulle

    Sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar korona, Pakistan ta yanke shawarar kulle gundumomi masu yawa a kusan manyan biranenta 20 a fadin kasar.

    Jami'ai sun ce duka yankunan da ake samun yaduwar cutar za a rufe su har na tsawon mako biyu, za kuma a sassauta dokar kullen ne kawai idan aka samu gagarumin ci gaba.

    Pakistan ta janye mafi yawan dokar kullen da ta sanya ne gabanin bikin sallar Eid da musulmai suka yi a ranar 23 ga watan Mayu.

    An dauki wannan matakin ke duk da sukar da ake samu daga ma'aikatan lafiya da kuma wasu kungiyoin adawa.

    Sun kuma alakanta wannan karuwar masu cutar ne da matakin sake bude kasuwanni masu cike da jama'a da aka dauka, ba kuma tare da tabbatar da wani matakin kariya ba ko kuma bin dokokin da aka shimfida.

    Sakamakon hakan adadin masu cutar ya karu a kasar cikin wata guda daga 15 ga watan Mayu da ake da 37,000 zuwa kusan mutum 149,000 ya zuwa ranar Talata.

    A makon da ya gabata, WHO ta shaida wa Pakistan cewa ta sassauta dokar kullen a lokacin da bai kamata ba.

  4. Cutar korona na ci gaba da ƙamari a Latin Amurka

    Kasashen Latin Amurka na ci gaba da fuskantar karuwar sabbin mutanen da suka kamu da Covid-19, kuma yankin yana tayar da hankula, a cewar Mike Ryan, shugaban shirin gaggawa na Hukumar lafiya ta Duniya:

    • Brazil ta zama kasa ta biyu da a duniya da ta fi fama da cutar - inda mutum fiye da 888,000 suka harbu da ita - da kuma mace-mace kusan 44,000. Masana sun ce za a c gaba da samun karn masu kamua da cutar korona a kasar sabod rashin isassun kayan gwaji, yayin da ake sa ran nan da makonni za a kai magaryar tukewar cutar.
    • A Mexico, mutum fiye 17,500 ne suka mutu sannan an tabbatar mutum 150,000 sun kamu da ita, ko da yake hukumomi sun ce watakila adadin ya zarta haka.
    • Chile ta tsawaita dokar kulle da ta sanya zuwa karin kwana 90 a yayin da ake ci gaba da samun masu kamua da ita- gaba daya, mutum fiye da 180,000 sun kamu da cutar inda mutum 3,300 suka mutu.
  5. Ma'aikatan lafiya na zanga-zanga a Faransa

    Ma'aikatan lafiya a fadin Faransa sun tsunduma cikin wata zanga-zanga neman karin kudi da kuma karin jarin a bangaren kiwon lafiyar kasar.

    Bayan janye taimakon da mutane ke ba da wa saboda cutar korona, Sun ce suna bukatar ganin sauyi na zahiri.

    Ainihin zanga-zangar ana gudanar da ita ne a wajen ma'aikatar Lafiya ta kasar da ke Paris, inda likitoci da ma'aikatan jinya suka taru suna neman a yi musu karin albashi, da samar da karin ayyuka da karin gadaje a asibitoci.

    Gwamnatin shugaba Macron na wata tattaunawa da ta shafi bangaren ayyukan lafiya sama da mako uku ya zuwa yanzu. kuma ta sanar da karin kudi ga ma'aikatan da suka yi aiki yayin wannan annoba.

    Sai dai kungiyar ma'aikatan lafiya ta kasar ta ce wannan cuta ta bankado wani rauni da ke a boye a tsarin kasar ta Faransa.

    A kalla ma'aikata 50 ne aka ci tararsu aka kuma kama wasu uku saboda zanga-zangar da suka yi a wajen wani asibiti a birnin na Paris.

  6. Za a sake bude makarantu da wuraren ibada a Guinea

    Shugaban Guinea Alpha Condé ya bayar da sanarwar sassauta dokar kulle wacce aka sanya da nufin dakile cutar korona.

    A jawabin da ya yi wa 'yan kasar ranar Litinin, shugaban kasar ya ce za a sake bude wuraren ibada daga ranar 28 ga watan Yuni a yankunan da cutar bata shiga ba.

    Ya kara da cewa daliban da za su rubuta jarrabawa da kuma na jami'a za su koma makarantu ranar 29 ga watan Yuni.

    A cewarsa, za a tabbatar da bin dokar bai wa juna tazara da tilasta sanya takunkumi a makarantun.

    Da ma dai an tilasta sanya takunkumin a bainar jama'a sannan akwai dokar hana fita tsakanin karfe 11 na dare zuwa kare hudu na asuba.

    An tabbatar mutu 4,572 sun kamu da cutar korona a kasar inda mutum 26 suka mutu.

  7. Shugaba Magufuli ya umarci a sake bude dukkan makarantun Tanzania

    Shugaban Tanzania John Magufuli ya bayar da umarni a sake bude dukkan makarantun kasar ranar 29 ga watan Yuni.

    Ya kuma bayar da umarni a sake bude harkokin kasuwanci da na mu'amalar yau da kullum kamar yadda suke a baya kafin bullar annobar korona.

    Mr Magufuli ya bayar da umarnin ne lokacin da yake jawabi a zauren majalisar dokokin kasar ranar Talata gabanin babban zaben kasar da za a yi a watan Oktoba mai zuwa.

    Ya jaddada kalaman da ya yi cewa Allah Ya kare kasar daga wannan annoba, kalaman da suka jawo ce-c-ku-ce.

    Ranar Litinin, Firaiminista Kassim Majaliwa ya ce mutum 66 ne kawai suka kamu da cutar a larduna 10 cikin 26 da ke fadin kasar.

    Da ma dai 'yan ajin karshe na makarantun sakandare da kuma daliban sun koma makaranta ranar 1 ga watan Yuni, amma sauran dalibai na ci gaba da zama a gida.

  8. Cutar korona ta kama Kwamishina da ɗan majalisar dokokin Gombe

    Kwamitin da ke yaki da cutar korona a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ya tabbatar cewa wani kwamishina da dan majalisar dokokin jihar sun kamu da covid-19.

    Jaridar Daily Trust ta ambato shugaban kwamitin yaki da cutar, Farfesa Idris Muhammad, yana bayyana hakan a taron kullum-kullum da ake yi kan cutar.

    Farfesa Muhammad ya kara da cewa jihar ta Gombe tana gudanar da gwajin cutar gadan-gadan kamar yadda jihar Lagos take yi yana mai cewa zuwa yanzu an yi wa mutum 3,668 gwajin cutar kuma an tabbatar mutun 410 sun kamu da ita.

    Tun da farko an tabbatar kwamishinoni hudu, 'yan majalisar dokoki biyar da kuma wani mai bai wa gwamnan jihar shawara sun harbu da cutar korona.

  9. Leicester da Crystal Palace na fafatawa don ɗauko Tarkowski

    Leicester City tana gogayya da Crystal Palace a yunkurin dauko dan wasanBurnleyda Ingila James Tarkowski, mai shekara 27.(Mirror)

    A wannan makon ne Timo Werner zai kammala komawa Chelsea daga RB Leipzig a hukumance, a yayin da wa'adin sayar da dan wasan na Jamus mai shekara 24 a kan £53m zai zo karshe yau.(Evening Standard)

    Juventus tana son dauko dan wasan Chelsea mai shekara 28 dan kasar Italiya Jorginho da dan wasan Spaniya Marcos Alonso, mai shekara 29.(Express)

    Manchester City tana sanya ido kan dan wasan Real Madrid da Morocco Achraf Hakimi. A halin da ake ciki dan wasan mai shekara 21 yana zaman aro a Borussia Dortmund.(AS, via Sun)

    Chelsea ta soma tattaunawa da dan wasan Brentford mai shekara 24 dan kasar Algeria Said Benrahma.(RMC, via Express).

  10. Ana zanga-zanga kan kashe-kashe a Arewacin Najeriya

    Kungiyoyi da dama ne suka fatsama kan tituna a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya ranar Talata da safe inda suke yin kira a dauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

    Masu zanga-zangar, mai taken #ArewaIsBleeding a turance, wato 'Jini yana kwarara a Arewa', sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.

    Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin kasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen.

    Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai 'yan bindiga da mayakan Boko Haram sun kashe mutum fiye da 100 a hare-haren da suka kai jihohin Katsina da Borno.

    Gwamnatin kasar ta sha cewa jami'an tsaro suna magance matsalar tana mai cewa galibin hare-haren da ake kai wa na gyauron 'yan bindiga ne, ko da yake 'yan kasar na cewa hakan ba gaskiya ba ne.

    Ranar Litinin kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan 'yan kasara yayin da matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin kasar.

  11. Ana bincike kan sace kayan kariya da aka bai wa Kenya gudunmawa

    Hukumomi a Kenya suna gudanar da bincike game da ɓatan da tufafin kariyar da aka bai wa kasar tallafi domin yaki da Covid- 19 suka yi.

    Kasar China ce ta bayar da tallafin tufafin kariyar, wadanda suka hada da takunkumin fuska na likitoci, rigunan zulumbuwa na likitoci, riguna da ake sanyawa idan za a killace mai dauke da cutar korona da kuma na'urorin auna zafin jikin mutane, wadanda kudinsu ya kai $2m.

    Binciken da gidan talbijin mai zaman kansa na KTN News ya gudanar ya nuna yadda wani kamfani da ke aiki da jami'an gwamnatin kasar da 'yan kasuwar China a Kenya, ya yi ikirarin cewa shi ne ya bayar da gudunmawar lokacin da kayan suka isa can.

    A wani mataki na ba kasafai ba, kamfanin ya dauki wasu daga cikin kayayyakin da aka sace ya bayar da su ga wasu hukumomin Kenyan a matsayin gudunmawa.

    Kenya ta samu tallafin miliyoyin dala daga kasashe da kungiyoyi daban-daban daga fadin duniya a kokarinta na yaki da cutar korona.

    Hamshakin attajirin nan na China Jack Ma, tda Asusun Lamuni na Duniya da kuma wasu kasashen Turai na cikin wadanda suka bayar da gudunmawa.

    Sai dai a gefe guda, likitoti da ma'akatan lafiya suna korafi kan rashin isassun kayayyakin kariya a yayin da suke yaki da cutar korona.

    Ministan Lafiya Mutahi Kagwe ya amince cewa akwai wasu bara-gurbi a ma'aikatarsa kuma ya sha alwashin hukunta su.

  12. Tambuwal na so a dinga kashe masu rike da makamai ba kan ka'ida ba

    Gwamnan jihar Sokoto da ke Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi kira a rika aiwatar da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama ya mallaki makamai ta haramtacciyar hanya.

    Gwamna Tambuwal, wanda ya sanar da hakan yayin wani taro a Sokoto ranar Litinin, ya ce ko dai a yi hukuncin kisa ko kuma majalisar dokokin kasar da fadar shugaban kasa su fito da dokar da za ta ba da damar yin hukuncin daurin rai-rai ga masu rike da makaman ba bisa ka'ida ba.

    Gwamnan ya ce shirye-shirye sun yi nisa don kafa wata rundunar bijilanti a jihar da nufin magance hare-hare 'yan fashin daji kan al'ummomin wasu sassa.

    Jihar ta Sokoto na cikin jihohin da 'yan fashin daji suka addaba inda ko a watan jiya sai da suka kashe mutane fiye da 60.

    Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren karin bayanin da kakakin gwamnan, Muhammad Bello, ya yi a BBC kan batun:

  13. Barkanmu da wannan safiya

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi AdamuYahaya ne yake yi muku barka da sake haduwa a wannan shafi mai albarka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.