COVID-19: Za a tursasa wa mutane sanya takunkumi a Ghana
Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana ya sanar da cewa daga yanzu wajibi ne 'yan kasar su rika sanya takunkumin rufe fuska a bainar jama'a sannan ya umarci 'yan sanda su tabbatar an bi wannan umarni.
Adadin masu kamuwa da cutar korona ya kusa kai wa 12,000, a kasar yayin da kuma mutum 54 suka mutu sannan aka gano mutum 4,000 na dauke da cutar.
A jawabin da ya yi ta gidan talabijin na kasar, Shugaba Akufo-Addo ya ce an samu karin masu kamuwa da cutar ne saboda an inganta yadda ake gudanar da gwajin kuma hakan ya nuna cewa cutar tana ci gaba da yaduwa.
An sassauta dokar hana tarukan addini kuma an sake bude makarantu ga daliban ajin karshe. Za a ci gaba da rufe iyakokin kasar.
Ya zuwa yanzu mutum 250,000 aka yi wa gwaji a kasar da ke da yawan mutane miliyan 30.