Kungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan 'yan kasar a yayin da matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin kasar.
A sanarwar da kakakin Amnesty International, Malam Isa Sanusi, ya aike wa manema labarai ranar Litinin, kungiyar ta ce "Rashin tsaro yana ci gaba da watsuwa a wani bangare na arewacin Najeriya; Katsina, Kaduna, Borno, Benue da wani yanki na jihar Niger, inda 'yan bindiga suke kashe mutane kullum, sannan su sace wasu, lamarin da ya jefa fargaba a zukatan mazauna kauyuka.
"Gazawar hukumomi wajen daukar matakin da zai kawo karshen wadannan hare-hare ta sa 'yan bindigar na cin karensu babu babbaka a wasu jihohin, kuma wannan lamari yana ci gaba da ta'azzara," in ji Amnesty International.
Kungiyar ta kara da cewa wadannan hare-hare sun sanya mazauna yankunan sun bar komai a hannun Mahalicci, inda kullum suke kwana su kuma tashi suna fargabar kai musu hare-hare.
Amnesty International ta nanata kira-kirayen da take yi wa gwamnati da ta mayar da kare rayukan jama'a ya zama babban abin da ta sanya a gaba.