Kasuwar saye da musayar 'yan kwallon kafa
Borussia Dortmund za ta sayar da dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho a kan £115m.(Telegraph)
Paris St-Germain tana son dauko dan wasan Ivory Coast mai shekara 27,Wilfried Zaha.(90 Min)
Southampton tana shirin sabunta kwangilar dan wasan Ingila Ryan Bertrand, mai shekara 30, a yayin daLeicestertake zawarcin dan wasan.(Daily Mail)
Golan Poland Bournemouth Artur Boruc, mai shekara 40, dan dan wasan tsakiya na Ingila Andrew Surman, mai shekara 33, da takwarorinsa masu tsaron baya Simon Francis, mai shekara 35, da Charlie Daniels, mai shekara 33, na shirin sanya hannu kan kwangilar gajeren lokaci.(Bournemouth Echo)