Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya yi umurni a kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail, Mustapha Musa Kaita and Awwal Ahmad Janyau

  1. Duniya 'ta yi watsi da rikicin Kamaru'

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Norwegian Refugee Council ta ce rikicin da gwamnatin Kamaru ta kwashe shekara biyu tana yi da 'yan a-waren yankin rainon Ingilishi na kasar shi duniya ta fi rashin bai wa muhimmanci.

    'Yan a-waren suna fafutukar ganin sun balle daga Kamaru don samun bisa abin da suka bayyana da cewa danne su da yankin da ke magana da Faransanci yake yi.

    Wasu daga cikin 'yan a-waren sun ayyana ballewa daga kasar - matakin da gwamnatin Shugaba Paul Biya ta ki amincewa da shi.

    Kazalika kasar ta Kamaru tana fama da kwararowar 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da kuma Arewacin Najeriya sakamakon rikice-rikicen da ake yi a can.

    Hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta ce ta yi amfani da hanyoyi uku ne wajen fitar da wannan matsayi: rashin kudi, rashin bayar da rahotannin abubuwan da ke faruwa a yankin daga wurin 'yan jarida, lda kuma rashin samun kulawa daga wurin 'yan siyasa da jami'an difilomasiyya.

    Kasashen Afirka goma ne hukumar ta ce suna cikin jerin wadanda aka yi watsi da su, kuma Venezuela ce kasa daya kawai da ba ta Afirka ba da ke cikin jadawalin.

    Rahoton hukumar ya yi tsokaci kan rikice-rikicien da ake yi a yankin Sahel wanda ya kunshi kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

  2. Wainar da ake toyawa a kasuwar 'yan kwallon kafa

    Chelsea ta yi amannar cewa dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, zai koma Manchester United don haka yanzu ta mayar da hankali wurin dauko dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz.(ESPN)

    A gefe guda, Chelsea ta tuntubi kungiyar wacce take buga Gasar Bundesliga domin yiwuwar dauko dan wasan mai shekara 20 Havertz, a yayin da ake rade radin cewa shi ma dan wasan Brentford Said Benrahma yana cikin wadanda Chelsea take son daukowa.(Guardian)

    Aston Villa ta dade tana son dauko dan kasar Algeria mai shekara 24 Benrahma kuma za ta yi kokarin sayensa - idan ta kauce wa fadawa kasan teburin Gasar Premier.(The Athletic)

    Dan wasan Brazil Thiago Silva yana son ci gaba da zama a Turai bayan da aka gaya masa cewa ba za a sabunta kwangilarsa a Paris St-Germain ba, kuma ya yi amannar cewa zai iya buga tamaula a kungiyar akalla tsawon kakar wasa biyu masu zuwa.(ESPN)

  3. Mutumin da ya 'yi wa mata 40 fyade a Kano zai gurfana gaban kotu'

    Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da mutumin nan da ta kama bisa zargin yi wa mata 40 fyade a gaban kotu.

    Kakakin rundunar ‘yan sandan ASP Abdul Kiyawa ya shaida wa manema labarai ranar Laraba cewa sun kama Muhammad, wanda aka sani da mai sket bayan sun dade suna farautarsa.

    Ya kara da cewa mutumin -- wanda yake yi wa matan aure da 'yan mata fyade ta hanyar haura katanga domin shiga gidajensu -- ya ce shi da kansa ne yake wannan ta'ada a tare da hadin bakin wasu ba.

    A cewarsa, "Da zarar mun kammala bincike a kansa za mu mika shi a gaan kotu domin ya girbe abin da ya shuka. Ya dade yana tsorata mata a garin Kwanar Dangora kuma ya ce shi yake aikatawa."

    Matsalar fyade dai tana neman zama ruwan dare a Najeriya.

    Ko a farkon wata yarinya mai shekara 12 ta shaida wa 'yan sanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.

    Kazalika a farkon watan an zargi wasu mutane da kisan wata ɗaliba ƴar jami'a bayansun yi mata fyade a jihar Edo da ke kudancin Najeriya.

  4. Barkanmu da warhaka

    Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.