Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya yi umurni a kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail, Mustapha Musa Kaita and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu zuwa gobe inda za mu ci gaba da kawo labarai da rahotanni kai tsaye.

    Sai da safe.

  2. Buhari ya sake yin Allah wadai da hare-haren Boko Haram

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya kadu da hare-haren da Boko Haram ta kai a Gubio jihar Borno.

    Sanarwar da mai taimaka wa shugaban kan harakokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar Buhari ya ce yana jiran karin bayani daga gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum wanda ya ziyarci mutanen yankin da abin ya shafa.

    Ya ce, yadda aka kai hare-haren abin damuwa saboda sun faru ba a dade da kammala azumin Ramadan da kuma bikin Sallah ba yayin da kuma kasar ke shirin bikin dimokuradiyya.

    Bayan Allah wadai da hare-haren da kuma yi wa al'ummar Borno jaje, shugaban ya kuma umurcin jami'an tsaron Najeriya da su tabbatar da nasarorin da suka samu akan 'yan ta'adda tare da kubutar da dukkanin mutane da shanun da aka sace.

  3. An gargadi mutane kan manhajar cutar korona

    Masana tsaro a internet sun gargadi jama'a da su guji sauke wasu manhajoji da ake badda kama ana fakewa da cewa suna gano masu cutar korona

    Masanan sun ce masu satar bayanai ta internet na amfani da wannan dubarar don satar bayanan al'umma.

    Binciken da masanan kamfanin Anomali a Amurka suka gudanar ya nuna cewa barayin na satar bayanan mutane musamman na banki da zarar ya sauke irin wannan manhaja. Kuma sun ce irin wadannan manhajoji sun yadu sosai a shafukan internet.

    Akwai runbun tattara manhajoji da ba a tantance ba da shafukan Intanet da suke bayar da kwarin guiwar sauke ire-irensu.

  4. Cutar korona na nan ba ta wuce ba - WHO

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ya yi gargadin cewa cutar korona nan ba ta wu ce ba kamar yadda wasu yayata cewa annobar ta wuce.

    Hukumar ta kuma nuna damuwa kan halin da tsarin lafiyar wasu kasashe ke ciki.

    Shugaban sashen harkar lafiya ta gaggawa Mike Ryan ya yi gargadin cewa annobar za ta iya sake mummunar barna a kudancin duniya.

    Dr Ryan ya ce har yanzu akwai kalubale musamman rashin isassun kayan kariya a wurare da dama.

    Ya ce suna ganin yadda cutar ke kara yaduwa a tsakiya da kudancin Amurka. A cewarsa abin damuwa ne matuka, kuma dole a maida hankali wurin ganin yadda za a dakile ta.

  5. Mataimakin gwamnan Bauchi ya warke daga cutar korona

    Mataimakin gwamnan jihar Bauchi Sanata Baba Tela ya warke daga cutar korona, bayan ya yi jinyar cutar na kwanaki kaɗan.

    Kafin kamuwarsa da cutar, shi ne shugaban kwamitin yaƙi da cutar ta korona a jihar inda ake zargin ya kama cutar ne yayin da yake gudanar da wannan aiki na yaƙi da korona.

    A yau Laraba ne dai aka sallame shi daga asibiti bayan likitoci sun tabbatar da cewa ya warke.

    Mataimakin gwamnan ya shaida wa wakilin BBC Is'haq Khalid ta wayar tarho cewa cutar ta yi matuƙar galabaitar da shi.

    Jihar Bauchi ce dai jiha ɗaya a Najeriya da ta kasance gwamna da mataimakin gwamna sun kamu da wannan cuta ta korona.

    Gwamnan jihar ta Bauchi Bala Muhammad shi ne gwamna na farko da ya kamu da korona a ƙasar.

  6. Zulum ya ziyarci ƙauyen da aka kashe mutum 81

    Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci ƙauyen Faduma Kolomdi na makiyaya da ke yankin ƙaramar hukumar Gubio na jihar.

    A ƙauyen ne dai aka kai wani hari inda ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne a jiya Talata inda suka kashe mutanen ƙauyen 81, suka raunata mutum 13, kuma suka sace mutum bakwai, ciki kuwa har da mai garin ƙauyen.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Isa Gusau ya fitar, gwamnan jihar ya yi kira ga sojojin Najeriya da su yi wani gagarumin kukan kura, wanda zai kawo ƙarshen masu tayar da ƙayar baya a yankin tafki Cadi.

    Wani wanda ya tsallake riya da baya yayin harin, ya shaida wa gwamnan jihar cewa masu tayar da ƙayar bayan sun isa ƙauyen ne da misalin karfe goma na safiyar jiya Talata, da manyan bindigogi da motocin sulke na yaƙi.

    Maharan sun kwashe tsawon sa’o’i shida suna ƙaddamar da hari, kafin su bar kauyen da misalin karfe hudu na yamma.

  7. Majalisa ta amince da kasafin kuɗin da Buhari ya yi wa kwaskwarima

    Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kasafin kuɗin da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi wa kwaskwarima na naira biliyan 10.8.

    Sai dai 'yan majalisar sun ƙara dala uku a kan farashin kowacce gangar mai, ba kamar yadda Buhari ya aike musu ba - sun saka farashin a kan dala 28 kan kowacce ganga, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Kazalika sun ƙara naira biliyan 300 a kan abin da Buhari ya buƙata a ƙarshen watan da ya gabata.

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta rage yawan kasafin ne sakamakon halin da annobar korona ta jefa tattalin arzikinta.

  8. A watan Yuli Man City za ta san makomarta a gasar Zakarun Turai

    Cikin watan Yuli ake sa ran kotun sauraron ƙararrakin wasanni ta duniya (CAS) za ta yanke hukunci kan dakatar da Manchester City da aka yi na shiga gasar Zakarun Turai har kakar wasa biyu.

    Lauyoyin kotun ƙararrakin wasannin za su yi nazari kan hukuncin da ya kamata a yanke bayan sauraron daukaka ƙarar da Man City ta yi.

    An saurari ƙarar da Man City ta shigar ta bidiyo tun daga Litinin zuwa Laraba.

    CAS ɗin ta ce hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyar Turai da Man City sun amince da yadda ta gudanar da aikinta.

  9. 'Yan uwan waɗanda korona ta kama a Italiya za su kai ƙarar gwamnati

    Wata ƙungiyar 'yan uwan wadanda suka kamu da korona a Italiya za su shigar da ƙara kan yadda ƙasar ta tafiyar da shirin daƙile annobar.

    Zuwa yanzu mutum 50 sun gabatar da koke ga masu shigar da ƙara a birnin Bergamo da ke arewacin ƙasar.

    Arewacin Italiya na daga cikin wuraren da cutar korona ta yi wa mummunar illa.

    Mambobin ƙungiyar sun ce an yi watsi da su da 'yan uwan nasu da cutar korona ta kama a lokacin da ake tsakiyar annobar.

    Sun kuma ce adalci suke nema a yi musu ba wai a ba su tara ba. Duk da cewa ba ta kama suna ba, ƙungiyar na buƙatar a gudanar da sahihin bincike.

  10. Buhari ya yabi 'yan Majalisa yayin da suke cika shekara guda da kama aiki

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya taya 'yan majalisar tarayyar ƙasar murnar cika shekara guda da kama aiki a majalisa ta tara a tarihin ƙasar na shekara kusan 60.

    Wata sanarwa da Fadar Gwamnatin Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce Buhari ya yabi mambobi da shugabancin majalisar bisa "jajircewarsu wurin tafiyar da ayyukan da suka shafi ci gaban ƙasa".

    "Yayin da Majalisar Tarayya ta tara ke bikin cika shekara ɗaya da kama aiki, Shugaba Buhari ya aminta cewa ta samar da kima da girmamawa ga 'yan ƙasa kuma yana fatan ganin ci gaban hakan a shekaru masu zuwa," a cewar sanarwar.

    An rantsar da majalisar ne ranar 11 ga watan Yunin 2019 kuma nan take suka zaɓi Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaba ta hanyar jefa kuri'a, inda ya kayar da Sanata Ali Ndume.

  11. Ana sa ran ƙaruwar masu korona a Masar

    Wani babban jami'in lafiya a Masar ya yi gargaɗi cewa, za a iya samun ƙaruwar adadin masu korona a ƙasar a wannan wata.

    Hossama Hosni wanda shi ne ke jagorantar kwamitin yaƙi da cutar korona a ma'aikatar lafiya ta ƙasar, ya ce 'yan ƙasar ba su damu da dokar bayar da tazara ba kuma suna hofintar da sauran dokokin kullen da aka kafa domin yaƙi da wannan annobar.

    "Bayar da tazara na da matuƙar muhimmanci sama da dokar kulle," kamar yadda ya shaida wa wata kafar yada labarai.

    "Dokar kulle zaman kanta take yi, haka ma dokar bayar da tazara, don haka dole a kiyaye da kowacce."

    Ya ce adadin waɗanda ke kamuwa da cutar a kullum yana kaiwa 2,000 a kullum kuma ana zaton zai iya haura hakan a nan gaba. Amma ya yi hasashen za a iya samun raguwar masu ɗauke da cutar a tsakiyar watan Yuli.

    Ya zuwa yanzu waɗanda suka harbu da cutar korona a Masar sun kai 35,000 kuma tuni sama da mutum 1,200 suka mutu.

  12. An gurfanar da gwamnatin Afirka ta Kudu a kotu kan hana sayar da taba

    Wata kotu a Afirka ta Kudu ta fara sauraron wata ƙara mai cike da ruɗani kan ƙalubalantar hukuncin dakatar da sayar da ganyen taba a watan Maris a wani ɓangare na yaƙi da cutar korona a ƙasar.

    Wata ƙungiyar masu sayar da taba a ƙasar da ake kira Fita ce ta shigar ga gwamnati ƙara gaban wata babbar kotu a Pretoria.

    "Mun kira wannan haramci da aka ƙaƙaba a matsayin tsattsaura domin matsa wa wasu" in ji lauyan Fita Arnold Subel.

    Sai dai lauyan gwamanti ya ce an ƙaƙaba haramcin ne da nufin matsa wa mutane su daina shan taba, wanda zai taƙaita wahala ga tsarin lafiya na ƙasar.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya cire dokar hana sayar da giya ranar 1 ga watan Yuni, amma an bar haramci kan taba saboda haɗarin da ke tattare da shan taba.

  13. 'Yan sanda 'sun kashe mutum 15 a Kenya' yayin dokar kulle

    Aƙalla mutum 15 'yan sandan Kenya suka kashe yayin dokar kulle, wadda aka saka da zummar daƙile yaɗuwar annobar korona.

    Wani rahoton hukumar sa ido kan ayyukan 'yan sanda ta ƙasar mai suna Independent Police Oversight Authority (IPOA) ne ya bayyana hakan.

    'Yan sanda shida za a tuhuma da laifin kisa da kuma cin zarafi a lokacin da suke ƙoƙarin tabbatar da dokar.

    Wani rahoton na hukumar kare haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa 'yan sanda sun ci zarafin mutane a yanki 182 na ƙasar - sun haɗa da duka da yin amfani da harsashi mai kisa da hayaƙi mai sa hawaye da yin lalata da kuma lalata gidaje.

    An gano cewa an fi samun yawan cin zarafin a babban ƙasar, Nairobi.

  14. Labaran duniya cikin minti ɗaya

    • Hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta ce wasu sabbin mutum 663 sun kamu da cutar a kasar jiya Talata. Abinda yakai adadin masu cutar 13,464, mutum 4,206 suka warke wasu 365 suka mutu.
    • Masu shigar da kara a Sweeden sun ce a karshe dai sun gano wanda ya kashe Firaiminista Olof Palme a 1986. Sun ce mutumin wani mai zane-zane ne dan kasar ta Sweeden kuma ya mutu shekara 20 baya.
    • Hukumar Lafiya ta Duniya ta ja kunnan Pakistan kan ta ci gaba da aiwatar da dokar kulle domin dakile cutar korona. WHO ta ce kasar ba ta cika ko sharadi daya ba na sassauta dokar kullen da ake sanywa saboda korona.
    • ‘Yan sanda a Hong Kong sun kama sama da masu zanga zanga 50, wadanda suka rufe titinan birnin.An kira zanga-zangar ne da nufin tunawa da masu goyon bayan dimokradiyya a kasar.
    • Chelsea ta janye daga cinikin dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, ta koma kan dan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz.
    • Dan wasan Brazil Thiago Silva yana son ci gaba da zama a Turai bayan an ce ba za a sabunta kwangilarsa a Paris St-Germain ba.
  15. An ɗage shari'ar ɗan jaridar da ake zargi da yaɗa labaran ƙarya a Kamaru

    Wata kotu ta ɗage zaman da ta shirya yi a yau Laraba domin sauraron ƙarar Paul Chouta, wani ɗan jarida mai zaman kansa da ake zargi da wallafa labaran boge da kuma yin ɓatanci ga shugaban ƙasa.

    Kotun ta ce sai ranar ranar 24 ga Yuni za ta zauna domin ta samu tattara wasu bayanai da take bukata.

    A ranar 23 ga watan Fabarairun 2019 ne ‘yan sanda suka chafke Paul Chouta suka kai shi gidan yari ba tare da shari’a ba.

  16. Annobar zazzaɓin aladu 'ta kashe alade fiye da 300,000 a Najeriya'

    Wata annobar zazzaɓi ta afka wa wata katafariyar gonar kiwon aladu mai suna Oke Aro da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    Wannan ne karon farko da aka tabbatar da ɓullar cutar a Najeriya cikin shekara 12.

    Duk da cewa mutane ba sa kamuwa da cutar, amma takan kashe aladu masu yawa a ƙanƙanin lokaci. Hukumar Lafiyar Dabbobi ta Duniya (OIE) ta ce yiwuwar mutuwar aladun idan ta kama su zai iya kaiwa kashi 100 bisa 100.

    Wani manomi ya shaida wa BBC cewa cutar ta kashe alade fiye da 300,000 tun sanda ta ɓulla a 'yan watannin da suka gabata.

    "A watan Fabarairu muka lura aladu na mutuwa a wani ɓangare na gonar. Da muka gudanar da gwaji sai muka tabbatar cewa muna fuskantar cutar zazzaɓin aladu," in ji Ayo Omirin.

    Gonar Oke Aro wadda ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Jihar Legas, ana ganin ta a matsayin ɗaya daga cikin mafiya girma a Afirka ta Yamma.

    Tana samar da aikin yi ga mutum sama da 3,000 da ke fafutikar samar wa abokan hulɗa mutum miliyan 50 a yankin.

  17. Ghana za ta karrama sunan George Floyd

    Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo ya ci alwashin karrama baƙin fatar nan da ake zargin 'yan sanda sun yi sanadiyyar mutuwarsa a Amurka mai suna George Floyd a birnin Accra.

    Mai magana da yawun gwamnati ya ce iyalan George Floyd sun ji daɗin karamcin yayin jana'izar da aka yi a Houston na Jihar Texas.

    Shugaban ya ce za a rubuta sunan Floyd a jikin ginin Cibiyar 'Yan Afirka Mazauna Ƙasashen Waje da ke birnin Accra.

    George Floyd ya mutu ne a asibiti bayan wani bidiyo da ya ɓulla ya nuna wani ɗan sanda ya maƙure masa wuya da gwiwa na tsawon minti bakwai lokacin da yake kama shi.

  18. An zaɓi 'coronavirus' a matsayin Kalmar Yara ta Shekara

    Masu rubuta ƙamus na harshen Ingilishi sun zaɓi 'coronavirus' wato cutar korona a matsayin Kalmar Yara ta Shekara bayan sun tantance labari 130,000 da aka aka tura wa BBC a wata gasar rubutu.

    Kamfanin Oxford University Press ya samu wuri 459 da aka ambaci kalmar ta coronvirus a labaran gasar da aka nemi kada su wuce kalma 500 kowannensu.

    Kamfanin ya dakatar da karɓar labarai daga shiga gasar ranar 27 ga watan Fabarairu, kusan wata guda kenan kafin a shiga dokar kulle a Ingila.

    Helen Freeman ta kamfanin Oxford University Press ta ce ta yi mamakin yadda aka riƙa amfani da kalmar.

    Kalmomi irinsu NHS, virus, antibodies, epidemic, Wuhan, lockdown na daga cikin waɗanda aka fi amfani da su fiye da yadda aka saba.

    An fi amfani da sunan Shugaban Amurka Donald Trump a labari 134,709, sai kuma sunayen Hitler da Cristiano Ronaldo.

  19. COVID-19: Gwamnatin Buhari za ta bai wa likitoci alawus

    Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin bai wa likitocin da ke fafutukar yaki da cutar korona alawus-alawus.

    Rahotanni sun ce gwamnatin ta dauki matakin ne ranar Talata bayan likitocin sun yi barazanar tsunduma yajin aiki.

    Kafafen yada labaran kasar sun rawaito cewa nan gaba kadan gwamnatin za ta soma bai wa likitocin alawus-alawus.

    Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta ce likitoci da dama ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar korona a bakin aiki.

    Ya zuwa ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, mutum 13,464 suka kamu da cutar korona, bayan da aka samu sabbin masu dauke da cutar korona 663 a kwana guda.

  20. WHO ta ja kunnen Pakista kan sassauta dokar kulle

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ja kunnen Pakistan kan sassauta dokar kulle tana mai cewa dole ne kasar ta ci gaba da aiwatar da dokar idan tana son dakile cutar korona.

    WHO ta ce kasar ba ta cika ko sharadi daya ba na sassauta dokar kullen da ake sanyawa saboda korona.

    Hukumomin lafiya a Islamabad sun sanar da sabbin masu dauke da cutar a kasar, wadda take da sama da mutum dubu 130 da aka tabbatar suna dauke da cutar, kuma sama da 2,000 ne suka mutu.

    Wani babban jami’i mai bayar da shawara a gwamnatin kasar ya ce suna cikin tsaka mai wuyar da sai sun zaba tsakanin matsin rayuwar kulle da kuma cutar korona.