Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Shugabannin Afirka na jimamin rasuwar shugaban Burundi

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Umar Mikail

  1. An yi zanga-zanga kan rashin tsaro a Katsina

    Mazauna kauyen 'Yantumaki da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga kan tabarbarewar tsaron da yankin ke fama da shi.

    Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna masu zanga-zangar da safiyar ranar Talata sun hau kan tituna suna kokawa kan yadda gwamnatocin tarayya da na jihar suka bar matsalar rashin tsaron tana ci gaba da tabarbarewa.

    Bayanai sun nuna cewa matasan yankin sun harzuka ne bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyen da jijjifin ranar Talata inda suka sace wani malamin asibiti da diyarsa. Koda yake babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar wa BBC hakan.

    Matasan sun rika kona tayoyi da kuma allunan jam'iyyar APC mai mukin jihar don nuna rashin jin dadinsu game da rashin tsaron.

    Ko a watan jiya sai da wasu mazauna yankin karamar hukumar Jibia suka yi zanga-zanga domin nuna matukar bacin ransu game da halin ko-in-kula da suke zargi shugabanninsu suna yi kan batun tsaron jihar.

    Matsalar tsaro na c gaba da ta'azzara a arewa maso yammacin Najeriya a baya baya nan.

    Kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10.

    Hukumomi dai suna cewa suna daukar matakan shawo kan matsalar, amma masu lura da lamuran tsaro sun ce akwai bukatar a dauki karin matakai domin magance ta.

  2. Manchester United ta kasa sayen Fati, Chelsea na son ɗauko Gerson

    Manchester United ta gaza biyan £89m domin sayo dan wasan Barcelona Ansu Fati, dan shekara 17, bayan ta sallama a yunkurin dauko dan wasan gaban Borussia Dortmund Jadon Sancho, mai shekara 20.(Sport)

    Ajax ta tabbatar da rahotannin da ke cewa Manchester United tana son dauko dan wasanta mai shekara 23 dan kasar Netherlands Donny van de Beek.(Sun)

    Chelsea tana gogayya da Tottenhamda Borussia Dortmun da yunkurin dauko dan wasan Flamengo dan kasar Brazil Gerson, mai shekara 23.(Fox Sports via Express)

    Wani dan kasuwar Amurka zai iya sayen Newcastle United idan 'yan kasuwar Saudiyya basu kammala biyan kudi domin sayen kungiyar ba.(Telegraph)

  3. Lauyoyi suna so a tsige shugaban Kenya

    Lauyoyi a Kenya sun ce za su gabatar da wani koke a gaban majalisun dokokin kasar biyu wanda zai nemi a tsige Shugaba Uhuru Kenyatta saboda abin da suka bayyana da cewa watsi da kundin tsarin mulkin kasar.

    Kungiyar lauyoyin kasar mai suna Law Society of Kenya (LSK) ta ce za ta kuma sauke Babban Lauyan Gwamnati kuma Antoni Janar na kasar daga cikn masu yi mata fafutuka saboda yana bai wa shugaban kasar gurguwar shawara.

    Hakan na faruwa ne bayan shugaban kasar ya ki amincewa ya rantsar da alkalai 41 da wata hukuma ta gabatar masa - yayin da shugaban hukumar shari'a ya zarge shi da yunkurin durkusar da fannin shari'ar kasar.

    "Bai kamata a rika zama da mutumin da ya rantse zai yi biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa ba amma ya kasa gudanar da ayyukansa," a cewar shugaban LSK Nelson Havi.

    A watan Fabrairu Shugaba Kenyatta ya ce ba zai rantsar da alkalan ba saboda wasunsu suna da kashi a gindi.

  4. Musulman Rohingya sun tsere daga wurin da aka tsare su

    Musulmai 'yan ƙabilar Rohingya kusan ɗari biyu da saba'in ne da suka tsere cikin jirgin ruwa daga kudancin Bangladesh, hukumomi a Malaysia suka tsare.

    Sun yi ta gararamba cikin teku a wani kwaraɓaɓɓen jirgin ruwa tsawon kusan wata biyu.

    Ba a san inda ragowar fasinjoji kimanin 200 da aka yi imani sun hau jirgin mai cunkoso, suke ba.

    Mahukunta sun hana jirginsu sauka a gabar ruwan ƙasar, wadda ke ƙarƙashin kulle mai tsanani saboda cutar korona.

    Mai aikowa BBC rahotanni na cewa 'yan gudun hijirar na fuskantar ƙarin matsanancin yanayi a sansanonin da ke Bangladesh kuma sun fid da ran iya sake komawa gida Myanmar.

  5. Buɗewa

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Daga na Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.