Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ɗalibai 9 'yan aji guda sun kamu da korona

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci ne muka kawo karshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labarai da rahotannin.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • Ƙarin mutum 14 sun warke daga cutar korona a Kaduna
    • Za a gudanar da sabon bincike kan Akinwumi Adesina
    • An sauke ministar da za ta sayi alawar miliyoyin dala a Madagascar
    • Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram da 'yan fashi
    • An yi taron addu'ar shekara shida da rasuwar Sarkin Kano Ado Bayero
    • An tuɓe shugabannin ƙananan hukumomi 14 a Zamfara
    • 'Yan sandan Najeriya na zanga-zangar ƙin jinin fyaɗe a Twitter
    • An nemi shugaban Mali ya sauka daga muƙaminsa

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta wasu labaran...

  2. Ɗalibai 9 'yan aji guda sun kamu da korona

    Wata makarantar firamare a lardin Quebec da ke ƙasar Canada ta zama wata cibiya ta annobar korona bayan kusan aji guda na ɗalibai sun kamu da cutar.

    Hukumomin lafiya a ƙasar sun tabbatar da cewa cikin ɗalibai 11 na ajin da suka kamu, tara daga ciki sun kamu.

    Hakan ya faru ne bayan yaro ɗaya mai ɗauke da cutar ya shafa wa sauran cutar.

    An bayyana cewa a halin yanzu makarantar ta ɗauki matakan kariya da suka haɗa da wanke hannu da kuma bayar da tazara tsakanin ɗalibai

  3. An fara zanga-zangar yanke ƙauna ga shugaban Mali

    Dubban mutane a Mali, sun shiga zanga-zangar yanke ƙauna inda suke yin kira ga Shugaba Boubakar Keita ya yi murabus, saboda karuwar hare-haren masu iƙirarin jihadi da kuma tabarbarewar tattalin arziƙi.

    Wata kungiyar mai rajin karfafa mulkin dimukradiyya ce ta shirya zanga-zangar da aka yi a babban birnin Bamako, da haɗin gwiwar jam'iyyun adawa da kungiyoyin kare haƙƙin dan adam.

    Fitaccen limamin nan Imam Mahmoud Dicko da ke ta kiran yin sulhu da masu kai harin ne ya jagoranci zanga-zangar.

    Wata kungiya dake marawa gwamnati baya, ta soki zanga-zangar, da ta kira a matsayin wani yunkuri na dagula al'amura a kasar.

  4. Buhari ya ƙara wa shugaban hukumar sadarwa wa'adin shekara biyar

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake amincewa da naɗin Farfesa Umar Garba Danbatta a matsayin shugaban hukumar sadarwa ta Najeriya.

    A halin yanzu, Farfesa Danbatta zai sake shafe wasu shekaru biyar a matsayinsa na shugaban hukumar.

    A wata sanarwa da ma'aikatar sadarwa ta Najeriya ta fitar, ta bayyana cewa naɗin Danbatta ya biyo bayan shawarar da Ministan Sadarwa na ƙasar Isa Ali Pantami ya bai wa shugaban ƙasar na sake naɗa Farfesa Danbatta.

  5. Babu me ɗauke da korona a asibitin birnin Wuhan - inda korona ta samo asali

    Hukumomi a birnin Wuhan na China - inda annobar korona ta faro - sun sanar ranar Juma'a cewa an sallami dukkanin waɗanda suka nuna alamun cutar korona daga asibiti.

    Jaridar Global Times ta ƙasar ta ce "an sallami mutum uku na ƙarshe da suka warke daga korona daga asibiti a Wuhan" - abin da 'yan ƙasar suka riƙa yabo a shafukan zumunta.

    Lokacin da take kan ganiyarta, korona ta kama fiye da mutum 50,000 a birnin, wanda nan ne cibiyar korona ta farko.

    Sai dai, ya kamata a san cewa China ba ta ƙirga waɗanda suka kamu da cutar amma ba su nuna wata alama ba. Ta fafra ƙirga irin waɗannan mutanen daga 1 ga watan Afrilu.

  6. An yi zanga-zangar adawa da fyade a Abuja

    Masu fafutuka sun kwarara kan tituna a manyan biranen Najeriya biyu Lagos da Abuja, don nuna fushinsu a kan lamarin fyade da ke kara kamari a kasar.

    An yi zanga-zangar a Legas ranar Alhamis yayin da aka yi ta Juma'a a Abuja.

    Ga wasu hotuna na yadda ta kasance a Abujar:

  7. An nemi shugaban Mali ya sauka daga muƙaminsa

    Dubban mutane ne suka taru domin yin zanga-zangar neman Shugaban Mali, Ibrahim Boubakar Keita ya sauka daga muƙaminsa sakamakon ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga da rikin ƙabilanci a ƙasar.

    An gudanar da zanga-zangar ne a Bamako, babban birnin ƙasar kuma gamayyar ƙungiyar 'yan adawa ce ta shirya shi mai suna Front For Safeguarding Democracy.

    Ya kuma gudana ne a ƙarƙashin jagorancin wani malamin addini Mahmoud Dicko, wanda ya sha kiraye-kirayen a tattauna da 'yan bindigar.

    Kazalika an yi irin wannan macin a watan Maris kan zaɓen 'yan majalisa da aka gudanar.

    Kusan mutum 10,000 ne suka shiga zanga-zangar na ranar Juma'a, a cewar AFP. 'Yan jarida sun yi ta wallafa hotunan cincirundon mutanen.

  8. 'Yan sandan Najeriya na zanga-zangar ƙin jinin fyaɗe a Twitter

    Hedikwatar 'yan sandan Najeriya na daga cikin na baya-bayan nan da suka shiga zanga-zangar neman kawo ƙarshen yi wa mata fyaɗe a ƙasar ta hanyar amfani da maudu'in #SayNoToRape a intanet.

    A cikin abin da bai wuce mako biyu ba an samu yawaitar rahotannin yi wa mata fyaɗe a Najeriyar, ciki har da wadda ta aka kashe ta bayan yin lalata da ita a coci.

    Tuni wasu daga cikin shugabannin al'iumma suka yi Allah-wadai da wannan mummunar ta'ada.

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga hukumomin kasar su yi wa dokokin fyade garambawul ta yadda masu yi wa mutane fyade ba za su kubuta ba.

    Ita ma Aisha Buhari, mai ɗakin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ta ce yawaitar yi wa mata fyade yana matuƙar tayar mata da hankali.

  9. Ronaldo ne ɗan ƙwallo na farko da ya zama biloniya

    Tauraron ɗan wasa Cristiano Ronaldo ya zama mutum na farko da ya zama biloniya a cikin 'yan wasan ƙwallon ƙafa a duniya, a cewar jaridar Forbes.

    Jaridar ta ce shahararren ɗan wasan na Juventus ya samu dala miliyan 105 a shekarar da ta gabata ban da haraji, abin da ya sa ya zama na 4 a jerin taturari 100 da suka fi samun kuɗi - ya bar Messi a mataki na 5.

    Ronaldo mai shekara 35, shi ne na huɗu da arzikinsa ya kai dala biliyan ɗaya yayin da yake tsaka da murza leda bayan Tiger Woods (ɗan wasan golf) da ya zama a 2009, da Floyd Mayweather (ɗan damben boksin) a 2017.

    Ronaldo ya samu dala miliyan 650 a matsayinsa na ƙwararren ɗan wasa sannan ana tsammanin zai samu dala miliyan 765 na albashi bisa yarjejeniyarsa ta yanzu, wadda za ta ƙare a shekarar 2022.

    Ɗan wasan Tennis Roger Federer ne kawai ya shiga gabansa a samun kuɗi cikin 'yan wasa a bara.

    Dan wasan ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau biyar sannan ya murza leda a Manchester United da Real Madrid kafin ya koma Juventus.

    Ana sa ran babban abokin hammayarsa Lionel Messi ya shiga wannan rukunin na wadanda suka samu fiye da dala biliyan ɗaya a shekara mai zuwa.

  10. An tuɓe shugabannin ƙananan hukumomi 14 a Zamfara

    Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta sauke shugabannin ƙananan hukumomi 14 bayan wata ganawar gaggawa sannan 'yan majalisar suka nemi Gwamna Bello Matawalle ya naɗa kantomomi.

    Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Shamsudden Mafara ne ya sanar da hakan bayan kammala zaman a yau Juma'a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

    Shamsudden Mafara ya ce a cikin shawarwarin da suka bai wa gwamnan sun buƙaci a gudanar da zaɓe a ƙananan hukumin da abin ya shafa cikin wata uku masu zuwa.

  11. Kotun Ƙoli ta tabbatar da tuɓe rawanin Aminu Babba Ɗan'agundi

    Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da matakin da marigayi Sarkin Kano da ke Najeriya, Alhaji Ado Bayero ya dauka na tube rawanin Aminu Babban Ɗan'agundi daga mukaminsa na Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa.

    Da take tabbbatar da hukuncin, Mai shari`a Mary Odili, wacce ta jagoranci alkalan Kotun Kolin su biyar, ta ce matakin da marigayi Ado Bayero ya dauka yana kan ka'ida.

    A shekara ta 2003 ne marigayi mai martaba Sarkin Kano Ado Bayero ya sauke Aminu Babba Dan`agundi daga mukamin nasa, bayan an zarge shi da nuna rashin da`a ga sarki, da aikata wasu laifuka da suka saba da dabi`un mai rike da mukami irin nasa.

  12. An yi taron addu'ar shekara shida da rasuwar Sarkin Kano Ado Bayero

    Gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero sun halarci taron addu'a na musamman na cika shekara shida da rasuwar marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

    Limamin Kano Farfesa Sani Zahraddin ne ya jagoranci addu'o'in tare da sauran manyan malamai na jihar Kano, kamar yadda mai taimaka wa Gwamna Ganduje ya bayyana shafinsa na zumunta.

    Taron adduar ya samu halartar hakimai da dama.

    Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya rasu ranar 6 ga watan Yunin 2014 bayan doguwar jinya.

    Ya hau kujerar sarautar Kano tun shekarar 1963, inda ya shafe shekara 51 a gadon mulki.

    Ɗan shekara 84, Margayi Alhaji Ado Bayero, shi ne Sarkin da ya fi kowanne dadewa a kan mulki a tarihin Masarautar Kano.

  13. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram da 'yan fashi

    Wani harin makaman atilare da sojojin Najeriya suka ce sun kai wa 'yan ƙungiyar Boko Haram da ISWAP ya yi sanadiyyar kashe 'yan ƙungiyar da dama a garin Pulka na Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

    Hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriyar da ke Abuja babban birnin ƙasar ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole sun kai harin ne ranar Talata, inda uku daga cikin 'yan Boko Haram suka miƙa wuya.

    A wani harin na daban, rundunar sojan ta ce dakarunta sun kashe wasu 'yan fashi biyu, yayin da wasu suka tsere da raunukan bindiga a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

    Kazalika an kashe ɗan Boko Haram ɗaya a Ƙaramar Hukumar Madagali ta JIhar Adamawa sannan suka ce sun kama wasu matan 'yan ƙungiyar guda uku.

  14. Sabbin bayanai daga Turai

    A yayin da kasashen Nahiyar Turai ke kokarin sassauta dokokin kan iyakokinsu, Kungiyar Tarayyar Turai ta EU na kokarin tsara yadda abin zai kasance:

    • Tarayyar Turai, wacce ta samar da daftarin dokokin kungiyar, tana neman mambobin kungiyar mai kasashe 27 su dage dokokin kan iyakokinsu nan da 1 ga watan Yuli. Akasarinsu suna yankin Schengen zone - yankin zirga-zirga ba tare da iyaka ba
    • EU ta bambance tsakanin iyakar cikin gida da kuma ta waje. Saboda haka ba wai kawai a kan bai wa mutane damar shiga ƙasashe ake magana ba, wasu matakan an daɗe da ɗage su da ma
    • Ana sa ran gwamnatin ƙasar Ireland ta amince da shirin cire dokar kulle nan gaba kaɗan. Za a ƙyale ƙananan shaguna da wuraren aiki su buɗe
  15. An sauke ministar da za ta sayi alawar miliyoyin dala a Madagascar

    An sauke ministar Ilimin Madagascar bayan an gano cewa ta yi shirin sayen alawa ta dala miliyan 2.2.

    A makon jiya Rijasoa Andriamanana ta ce ta bayar da umarnin sayo alawar ga kananan yara din ba su ita da maganin korona don kashe kaifin dacin da maganin yake da shi, a cewar, kamfanin dillacin labarai na AFP.

    Maganin gargajiyar na Covid-Organics shi ne ganyen da gwamnatin kasar ta rika tallatawa wasu kasashe inda ta ce yana maganin Covid-19. Ko da yake Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce babu wani riga-kafi ko magani cutar korona kawo yanzu.

    AFP ya ce ana sa ran kowanne dalibi a kasar zai samu alawa uku.

    Kafofin watsa labaran kasar sun ce ministar ta fasa shirin sayo alwarar bayan Shugaba Andry Rajoelina ya ki amincewa da bukatarta.

    Ranar Alhamis aka sanar da korar ministar a wata sanarwa da inda aka ce takwararta a ma'aikatar ilimi mai zurfi , Elia Béatrice Assoumacou, za ta maye gurbinta don yin rikon-kwarya.

  16. Ƴar Najeriyar da za a sayar a Lebanon ta ƙi yarda ta koma gida

    Matar nan 'yar Najeriya da aka tallata a shafin Facebook don sayar da ita a Lebanon ta ki amincewa ta koma kasarta, a cewar hukumar kula da 'yan kasashen waje ta Najeriya.

    A watan Afrilu ne aka ceto daga kasar Lebanon, kwanaki kalilan bayan hukumomin kasar ta Lebanon sun kama wani mutum da ake zargi da yunkurin sayar da matar a kan $1,000 sannan aka kai ta ofishin jakadancin Najeriya da ke Beirut.

    Matar mai shekara 30 ta ce ta samu sabon aiki a Lebanon.

    Shugabar hukumar kula da 'yan kasashen waje ta Najeriya, Abike Dabiri-Erewa, ta ce ta yi kokarin rarrashin matar ta koma gida amma ta ki yarda.

    "Shi ma Sakataren Gwamnatin jihar Oyo, jhar da ta fito, ya yi magana da ita. Muna fatan za a rika mutunta 'yan Najeriya da ke aiki a Lebanon, ba kawai a rika kallonsu tamkar bayi ba," a cewar Ms Dabiri-Erewa.

    Ta kara da cewa gwamnatin Lebanon ta mayar da 'yan Najeriya 69 cikin 79 kasarsu. A halin da ake ciki an killace dukkansu 69.

    Ofishin jakadancin Lebanon ya dakatar da bayar da biza ga 'yan Najeriya wadanda ke neman aikatau a gidajanen attajirai a Lebanon bayan batun matar.

  17. Ma'aikatan lafiya 70 sun kamu da cutar korona a Ghana

    Hukumomin lafiya a Ghana sun ce ma'aikatan lafiya saba'in a yankin tsakiyar kasar sun kamu da cutar korona.

    An tabbatar cewa yanzu mutum fiye da 8,000 ne suka kamu da cutar, yayin da mutum 38 suka mutu ko da yake mutum sama da 3,000 sun warke daga cutar.

    Ma'aikatan lafiyar da suka kamu da cutar basu nuna alamar harbuwa da ita ba.

    Hukumomi sun ce wasu daga cikinsu basu bi ka'idojin kare kai daga kamuwa daga cutar ba lamarin da ya sa suka kamu da ita.

    An tabbatar mutum fiye da 400 sun kamu da cutar korona a Kudancin Ghana, kuma 70 daga cikinsu ma'aikatan lafiya ne.

    Shugaba Nana Akufo-Addo ya sassauta dokar tarukan addini sannan ya bude makarantu ga daliban ajin karshe duk da yake ana samun karuwar masu kamuwa da cutar.

    Sai dai iyakokin kasar ta Ghana suna ci gaba da kasancewa a garƙame.

  18. Cutar korona: Brazil tana gogayya da Amurka da Birtaniya

    Yanzu Brazil ta sha gaban Italiya inda ta kasance kasa ta uku da ke da yawan mutanen da suka mutu sakamakon annobar korona, bayan Amurka da Birtaniya.

    Ministan Lafiyar kasar ya ce sama da 'yan kasar dubu 34 cutar korona ta hallaka.

    A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kasar ta bayar da rahotannin mutuwar mutum kusan 1,500-- a kowanne minti kenan ana samun mutuwa.

    Shugaban kasar, Jair Bolsonaro da ke adawa da sanya dokar kulle tun farkon soma barkewar cutar, ya sake nanatawa a cikin wannan makon cewa yunwa da rashin aiki za su fi yin kisa akan cutar korona.

  19. Chilwell yana son komawa Chelsea, Liverpool ta janye daga batun ɗauko Werner

    Dan wasan Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23, yana son amsa tayin da aka yi masa na komawa Chelsea nan gaba a bazara ko da yake har yanzu ba a gaya masa ya bar Leicester City ba.(Mirror)

    Liverpool ba za ta yi gogayya da Chelsea a fafutukar dauko Timo Werner mai shekara 24 ba domin kuwa dan wasan na RB Leipzig da Jamus yana dab da komawa Stamford Bridge.(Evening Standard)

    Tottenham tana jiran dan wasan Belgium Jan Vertonghen, mai shekara 33, ya yanke shawara kan ko zai kammala kakar wasa ta bana ko kuma zai bar kungiyar kafin a gama kakar.(Sky Sports)

    Dan wasan Newcastle Matty Longstaff bai yi atisaye ba a wannan makon saboda fargabar rashin sanin makomarsa a kungiyar, a yayin da rahotanni suke cewa Udinese tana son dauko dan wasan inda za ta rika ba shi £30,000 duk mako. A bazarar nan kwangilar dan wasan za ta kare a Newcastle.(Mail)

  20. Za a gudanar da sabon bincike kan Akinwumi Adesina

    Bankin ci gaban Afirka, African Development Bank (AfDB), ya ce ya kaddamar da sabon bincike mai zaman kansa kan shugaban bankin, Akinwumi Adesina, a kan zarge-zargen hanci da rashawa.

    Tsohon ministan na aikin gonar Najeriya yana son sake tsayawa takarar shugabancin bankin a zaben da za a gudanar a watan Agusta mai zuwa.

    Amurka tana cikin kasashen da suka jagoranci kira da a gudanar da bincike a kansa game da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa.

    Sai dai Mr Adesina ya musanta zarge-zargen.

    Kazalika shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai goyi bayan takarar Mr Adesina.

    Amurka tana da kashi 6.5 na hannun jari a bankin, kuma ita ce ta biyu mafi yawan hannun jari bayan Najeriya.

    Denmark, Norway, Sweden da kuma Finland - wadanda su ma suna da hannun jari a bankin - sun aike da sakon da ke goyon bayan gudanar da bincike mai zaman kansa a kan Mr Adesina.