An saki tsohon gwamnan Abia Orji Kalu daga gidan yari

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe inda za mu ci gaba da kawo labarai da rahotanni a shafin namu.

    Mu kwana lafiya.

  2. An saki tsohon gwamnan Abia Orji Kalu daga gidan yari

    Tsohon gwamnan jihar Abia Sanata Orji Uzor Kalu

    Rahotanni daga Najeriya sun ce an saki tsohon gwamnan jihar Abia Sanata Orji Uzor Kalu daga gidan yarin Kuje inda yake zaman hukuncin shekaru 12 da aka yanke masa.

    Jaridar Tha Nation ta ce an saki tsohon gwamnan ne da yammacin ranar Laraba bayan kotu ta bayar da umurnin a sake shi.

    A ranar Talata ne wata Babbar Kotun Tarayya a Legas ta yi umarni da a saki Sanata Orji Uzor Kalu bayan ya nemi kotun ne ta jingine hukuncin ɗaurin da aka yi masa na ranar 5 ga watan Disamban 2019, wanda Mai Shari'a Mohammed Idris ya yanke.

    An yanke masa hukunci ne kan zargin wawushe dukiyar da ta kai sama da naira biliyan 7 na jihar Abia.

  3. Hana yara zuwa Masallaci na cikin sharuɗan da aka gindaya a Najeriya

    Babban Masallacin Ikko

    Asalin hoton, Getty Images

    Hana wa yara zuwa wuraren ibada na cikin sharuɗɗan da hukumomin Najeriya suka shata kafin buɗe masallatai da coci coci.

    Haramta zuwa da Yara masallaci na cikin matakan da hukumomi suka ɗauka domin daƙile yaduwar cutar korona.

    Kuma kwamitin shugaban ƙasa kan yaki da cutar a Najeriya ya buƙaci gwamnonin jihohi su tabbatar da matakan domin rage bazuwar cutar da ta kama mutum 10,819 tare da kashe mutum 299 duk da an sallami mutum 3,239.

    Daga cikin sharuɗɗan sun hada da buɗe masallaci minti 20 kafin fara sallah sannan kuma a rufe bayan minti 20 da gudanar da sallah.

    Lokacin Magariba da Sallar Isha za a buɗe minti 10 kafin sallar Magariba sannan a rufe minti 10 bayan Sallar Isha'i.

    Ana son a bayar da tazara ga mutanen da za su jira Sallar Isha'i bayan Magariba.

    Sannan adadin lokacin da aka ƙayyade na gudanar da Sallar Juma'a da huɗuba duka kada ya wuce awa ɗaya. Haka kuma ba a yadda a gudanar da Salloli ba baya ga Salloli biyar na farilla da Sallar Juma'a.

    Haka kuma akwai rukunin waɗanda aka haramta wa zuwa masallaci da suka haɗa da waɗanda shekarunsu suka haura 65 da kuma masu fama da cututtuka kamar tarin fuka da cutar SIDA ko HIV da kuma cuwon suga.

    Sauran Matakan sun haɗa da:

    • Amfani da takunkumi ga duk wanda zai shiga masallaci
    • Tsabtace masallaci kafin gudanar da ko wace Sallah musamman amfani da sinadari domin goge kafet
    • An buƙaci masallatai su samar da na'urar da ke auna zafin jiki da kuma samar da abin wanke hannu kafin shiga masallaci da kuma makewayi ga dukkanin masallata da kuma dukkanin masu kula da masallaci
    • Lokacin kiran Sallah da Iƙama kada ya wuce minti 10
    • Ana son a bude ƙofa da tagogi a duk lokacin gudanar da Salloli biyar na farilla da kuma Sallar Juma'a
    • Ana kuma son duk wanda zai zo masallaci ya zo tare da dardumarsa ta Sallah. Sannan ana son a bayar da tazara akalla mita biyu tsakani a sahu
    • Yawan masu Sallah kada ya wuce kashi ɗaya bisa uku na yawan adadin mutanen da Masallacin ke ɗauka
    • Ba a son mutane su riƙa gaisawa da juna. Haka kuma ana son a dinga rubuta sunayen duk waɗanda suka shiga masallaci domin gudanar da salloli biyar na farilla
    • Makarantun Islamiyya za su ci gaba da kasancewa a rufe.
  4. Ƴan bindiga sun ba ƴan gudun hijirar Mali wa'adi su fice Nijar

    ƴan gudun hijirar Mali a Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Mali na cewa ƴan gudun hijirar Mali na ficewa daga sansaninsu kwana uku bayan harin da aka kai a sansanin Intikane da ke Tilia yankin jihar Tawa a Jamhuriyyar Nijar.

    Jaridar L'Independant a Mali ta ce ƴan bindigar sun ba ƴan gudun hijirar wa'adin sa'a 48 su fice daga sansanin ko kuma su sake ƙaddamar da sabbin hare-hare.

    Jaridar ta ce ƴan bindigar sun yi gargaɗin ne kan ƴan gudun hijira da suka zarga da ƙarfafawa ƙungiyoyin ƙasashen waje shigowa yankin.

    A ranar Lahadi ne ƴan ta'addar masu alaƙa da ƙungiyar al Ƙaida suka kai hari sassanin da ke ɗauke da dubban ƴan gudun hijirar Mali inda suka kashe jami'an da ke kula da sansanin.

    Rahotannin sun ce har yanzu ƴan gudun hijirar na nan cikin yankin Nijar, saboda iyakoki da aka rufe saboda annobar cutar korona.

  5. Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya gargaɗi Amurkawa

    Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya gargaɗi Amurkawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya gargaɗi Amurkawa da su dakatar da ziyartar ofishin da ke kan Titin Walter Carrington a Jihar Legas sakamakon zanga-zanga da wasu suka shirya game da kisan baƙar fatar nan mai suna George Floyd.

    Wasu 'yan Najeriya ne dai suka shirya zanga-zangar don nuna goyon bayansu ga kiraye-kirayen Allah-wadai da mutuwar George Floyd, wanda ya mutu a hannun 'yan sandan Amurka.

    Jaridar The Punch ta ruwaito ofishin jakadancin yana shawartar Amurkawa su kula sosai a inda suke zaune.

    "Ofishin Jakadancin Amurka ya samu rahotannin cewa wasu mutane sun shirya zanga-zanga a gaban ofishin a ranar 3 ga watan Yuni," in ji wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa.

    Sanarwar ta ƙara da cewa: "Zanga-zangar lumana ka iya rikiɗewa zuwa rikici."

  6. Amurka za ta hana wa jiragen China shiga ƙasarta

    Amurka na shirin hanawa jiragen China zirga-zirga zuwa ƙasar bayan China ta hanawa wasu jiragen Amurka na dakon kaya dawo da zirga-zirga zuwa China.

    Kamfanonin jiragen Amurka, da suka haɗa da Delta da United. sun dakatar da zirga-zirga zuwa China a watan Fabrairu saboda annobar korona.

    Hukumomin Amurka sun ce China ba ta ba jiragen na Amurka damar dawo da zirga-zirga ba - sabon matakin zai fara aiki a watan Yuni amma kuma shugaba Trump na iya aiwatar da dokar ba da daɗewa ba

    A watan Maris, China da taƙaita wa jiragen China zirga-zirga, inda aka ba kamfanonin amfani da jirgi ɗaya yin zirga-zirga a mako zuwa ƙasashen da suke zirga-zirga.

  7. Ɗan wasan Tottenham ya kamu da korona

    Tottenham

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu mutum daya a kungiyar kwallon kafa ta Tottenham dauke da cutar korona a wani gwaji da aka yi, kamar yadda kungiyar da ke buga Premier League ta sanar. .

    Mutumin zai killace kansa na kwana bakwai kamar yadda doka ta tanada, sannan a kara gwada shi.

    Tottenham ta ce saboda matakan lafiya ba za ta bayyana sunansa ba.

    Shi ne mutum na farko da aka samu dauke da annobar bayan gwajin da aka yi wa 'yan wasa da jami'ai 1,197.

  8. An buɗe makarantu a Nijar

    Nijar

    Asalin hoton, Others

    Bayanan hoto, Ɗalibai a yankin Tillabery na Jamhuriyar Nijar

    A ranar Litinin 1 ga watan Yuni aka buɗe makarantu a Jamhuriyar Nijar bayan fiye da wata guda da rufe su saboda annobar korona.

    Ɗalibai a yankin Dosso

    Asalin hoton, Others

    Bayanan hoto, Ɗalibai a yankin Dosso na Jamhuriyar Nijar

    Mutum 958 ne suka kamu da cutar korona a Nijar, a cewar alƙaluman hukumar CDC Africa mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Afirka.

    Ɗalibai a yankin Dosso na Jamhuriyar Nijar

    Asalin hoton, Others

    Daga cikin 958, 64 sun rasa rayukansu sannan kuma 839 sun warke.

  9. Fafaroma Francis ya yi tur da kisan George Floyd

    Fafaroma Francis

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Francis ya yi tur da kisan da 'yan sanda suka yi wa wani bakar fata a Amurka George Floyd.

    "Ya ku 'yan uwa maza da mata da ke Amurka, na damu kwarai da gaske da hargitsin da ake yi a kasarku a kwanakin baya bayan nan, sakamakon kisan da aka yi wa Mr. George Floyd," in ji Fafaroma a jawabin da ya yi daga Vatican.

    Ya kara da cewa yana yin addu'ar “Allah Ya jikan George Floyd da kuma dukkan mutanen da suka mutu sakamakon wariyar launin fata”.

    "Abokaina, ba za mu amince ko kuma mu ki mayar da hankali kan wariyar launin fata ba ta kowacce fuska, sannan kuma mu ce muna mutunta dan adam," a cewarsa

    "A lokaci guda, ya kama mu yi la'akari da tarzomar da aka kwashe tsawon wasu dare ana yi wadanda ba su da amfani. Babu abin da za a yi nasara a kansa ta hanyar tarzoma," in ji Fafaroma.

  10. An buɗe kasuwanni a Kano

    Kasuwar Sabon Gari

    A yau Laraba ne sassaucin dokar fita da gwamnatin Kano ta yi wa ‘yan kasuwa domin ci gaba da domin ci gaba da harkokin kasuwancinsu yake farawa.

    Kasuwar Sabon Gari

    Gwamnatin jihar ta ce za’a buɗe kasuwar ne bayan cimma matsaya da wakilan 'yan kasuwar wajen samar da matakan da za’a a ɗauka don ganin ba’a samu yaɗuwar cutar ba a kasuwannin.

    Kasuwar Sabon Gari

    Kasuwanni a Kano sun kasance a rufe tun ranar 27 ga watan Afrilu kafin daga bisani a riƙa buɗe wasu daga ciki a ranakun Litinin da Alhamis bayan sassauta dokar, wadda aka saka domin daƙile yaɗuwar cutar korona.

  11. Sojojin Najeriya sun 'kashe kwamandojin Boko Haram'

    Hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta na rundunar Operation Lafiya Dole da ke arewa maso gabashin Najeriya sun yi nasarar kashe kwamandojin ƙungiyar Boko Haram guda uku.

    A sanarwar da rundunar ta fitar ranar Laraba, lamarin ya faru ne bayan Boko Haram ta kai hari a yankin Banki Junction, inda sojoji suka mayar musu da martani a ranar 26 ga watan Mayu kuma suka yi nasarar kashe kwamandojin Boko Haram na ɓangaren Abubakar Shekau.

    Manzar Halid da Amir Abu Fatima da Nicap na daga cikin manyan mayaƙan ƙungiyar da suka halaka, a cewar sanarwar.

    A baya-bayan nan, sojojin Najeriya na bayyana irin nasarorin da suke samu a yaƙin da suke yi da Boko Haram, sai dai majiyarsu ce kawai ke bayar da rahotannin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. An kama matar tsohon firaministan Lesotho

    Maesaiah Thabane

    Asalin hoton, AFP

    An kama tsohuwar uwar gidan shugaban ƙasar Lesotho - Shugaba Thomas Thabane da ya sauka daga mulki kwanan nan.

    An janye hukuncin belin da aka bai wa Maesaiah Thabane a makon da ya gabata.

    Shi kansa Shugaba Thabane na cikin mutanen da ake zargi da kisan Lipolelo, wadda aka harbe shekara uku da suka wuce 'yan kwanaki kaɗan kafin rantsar da Thabane a matsayin firaminista.

    Ma'auratan sun musanta zargin da ake yi musu na kisan. Lamarin ya jawo tayar da jijiyoyin wuya a Lesotho.

  13. Labaran duniya cikin minti ɗaya...

    NCDC

    Asalin hoton, NCDC

    • Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce wasu mutum 241 ne suka sake kamuwa da cutar korona a kasar. Hakan ya kai adadin masu cutar zuwa 10,819, mutum 3239 suka warke yayin da 314 suka mutu
    • An samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar korona a Kamaru bayan bude makarantu ranar 1 ga watan Yun. Mutum 254 ne suka harbu da cutar ranar Litinin, yayin da wasu 188 suka kamu da ita ranar Talata
    • Jamus za ta ɗage duka dokokin da ta sanya game da tafiye-tafiye daga ranar 15 ga wannan watan da muke ciki
    • Ministan harkokin wajen kasar, Heiko Maas ya ce, za a maye gurbin dokar da shawarwarin tafiya da ke da alaka da kowacce kasa
    • Kasuwar hannayen jari ta duniya ta fara farfadowa daga koma bayan da annobar korona ta haifar mata
    • Wannan farfadowar da kasuwar ta yin a da alaka ne da sake bude harkokin kasuwanci da gwamnatocin turai ke yi
    • Chelsea ta ce babban abin da ta sanya a gaba yanzu shi ne dauko dan wasan Leicester Ben Chilwell, mai shekara 23
    • Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi magana da wakilin dan wasan Manchester United Paul Pogba, mai shekara 27
  14. Gwamna Zulum ya dakatar da dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala

    Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum, ya dakatar da dukkan ma'aikatan babban asibitin garin Ngala saboda sun bar bakin aiki.

    A sanarwar da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ma'aikatan da aka dakatar sun hada da likitoci da ma'aikatan jinya, da masu bayar da magunguna da masu gwajin jini.

    Ya dauki matakin ne bayan ya kai ziyarar ba-zata ranar Litinin da misalin karfe 11 na safe, yana mai cewa bai ji dadin barin da ma'aikatan suka yi wa bakin aikinsu ba duk da yake ana biyansu albashi yadda ya kamata.

    Garin na Ngala yana da kan hanyar zuwa kasashen Kamaru da Chadi, da Sudan na kuma Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. An umarci wakiliyar WHO 'ta fice daga Equatorial Guinea'

    Equatorial Guinea ta umarci wakiliyar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta fita daga kasar, a cewar kamfanin dillacin labarai na AFP.

    Hukumomi sun zargi Triphonie Nkurunziza da bayar da "bayanan karya" game da adadin masu dauke da cutar korona a kasar.

    An ambato Firaiminista Pascual Obama Asue yana shaida wa Majalisar Dattawan kasar ranar Juma'a cewa: "Ba mu da matsala da WHO, amma muna da matsala da wakiliyarta da ke Malabo."

    AFP ya ambato wata majiya a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke babban birnin kasar Malabo tana cewa: "Gwamnati ta umarce ta ta tafi, mun karbi wasu takardu - inda aka zarge ta da bayar da bayanan karya kan adadin masu dauke da Covid-19".

    Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu Dr Nkurunziza tana Malabo domin kuwa babu jirgin da zai fita daga kasar, inda suka kara da cewa alkaluman da WHO ta fitar da wadanda gwamnati ta bayyana yanzu iri daya ne.

  16. Chelsea tana son sayo Chilwell, har yanzu Zidane yana son ɗauko Pogba

    Chelsea ta ce babban abin da ta sanya a gaba yanzu shi ne dauko dan wasan Leicester Ben Chilwell, mai shekara 23, ko da yake za a sayar da dan wasan na Ingila a kudin da ya kai £85m.(Athletic - subscription required)

    Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi magana da wakilin dan wasan Manchester United Paul Pogba, mai shekara 27, yana mai cewa har yanzu suna sha'awar dauko dan wasan na Faransa.(Le 10 Sport - in French)

    Manchester United tana son karbo dan wasan Velez Sarsfield dan kasar Argentina Thiago Almada, mai shekara 19, a matsayin zabin da ya rage mata idan bata samu damar dauko dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20 ba.(Manchester Evening News)

    Chilwell

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Chilwell
  17. An samu ƙarin masu korona bayan buɗe makarantu a Kamaru

    An samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar korona a Kamaru bayan an sake bude makarantu ranar 1 ga watan Yuni.

    An samu karin mutum 254 da suka harbu da cutar ranar Litinin yayin da karin mutum 188 suka kamu da cutar ranar Talata.

    Gwamnatin kasar ta ce ta dauki matakai domin kare dalibai daga kamuwa da cutar cikinsu har da tsaftace azuzuwa da raba sinadarin goge hannu da kuma sanya makarin fuska.

    Dalibai 'yan ajin karshe na makarantun sakandare da kuma takwarorinsu na jami'o'in kasar sun zauna nesa-nesa da juna a cikin azuzuwa.

    Jami'an hukumomin ilimi sun yi barazanar hukunta duk malamin da ya ki komawa bakin aiki bayan wasu daga cikinsu sun nuna fargaba kan yawaitar bullar cutar ta korona, a cewar jaridar Journal Du Cameroun

    Kawo yanzu an tabbatar mutum 6,585 sun kamu da cutar korona a Kamaru yayi da mutum 200 suka mutu.

    Dalibai sun zauna nesa-nesa da juna

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Dalibai sun zauna nesa-nesa da juna
  18. Mataimakin gwamnan Bauchi Baba Tela ya kamu da cutar korona

    Gwamnan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, Sanata Bala Mohammed, ya tabbatar da cewa mataimakinsa Sanata Baba Tela ya kamu da cutar korona.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, Gwamna Bala ya ce Baba Tela ta kamu da cutar ne a bakin aiki a matsayinsa na shugaban kwamitin yaki da cutar na jihar Bauchi.

    A cewarsa, tuni aka killace Sanata Tela kuma ma'aikatan lafiya suna ba shi kulawa kamar yadda ya kamata.

    Gwamna Bala ya kara da ce an gudanar da gwajin cutar korona kan mutanen da ya yi mu'amala da cu inda aka shawarce su su killace kansu har sai an fitar da sakamakon gwajin.

    "Ina yin jaje a gare shi da iyalansa, a yayin da muke yi masa addu'ar samun sauki", in ji gwamnan na Bauchi.

    Gwamna Bala yana cikin mutane na farkofarko da suka kamu da cutar ta korona a Najeriya, ko da yake ya sanar da cewa ya warke ranar 9 ga atan Afrilun da ya gabata.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Buɗewa

    Nasidi AdamuYahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.