Fitaccen mawaƙin Najeriya Majek Fashek ya mutu
Fitaccen mawakin nan na Najeriya Majek Fashek ya rasu.
Manajan mawakin ne ya tabbata da rasuwarsa ranar Talata a shafin marigayin na Instagam.
Majek ya shahara musamman a wakokin da ya rera a shekarun 1980 zuwa 1990, kamar fitattun wakokinsaSend Down the RaindaSo Long for Too Long.
Majek, wanda sunansa na yanka shi ne Majekodunmi Fasheke, ya kuma rera wakoki tare da shahararrun mawaka irin su Jimmy Cliff, Tracy Chapman da Snoop Dogg.
Manajansa Omenka Uzoma ya wallafa sanarwar rasuwar mawakin a shafin maragayin na Instagram ko da yake bai bayyana musabbabin rasuwarsa ba.