Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Majalisa ta amince wa Buhari karɓo rancen dala biliyan 5

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu dakata da kawo maku labarai da rahotanni kai-tsaye da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe idan Allah Ya kai mu inda za mu ci gaba da kawo rahotanni kai tsaye.

  2. Mutum 33 sun warke daga cutar korona a Legas

    Gwamnatin Legas ta ce ta sallami ƙarin mutum 33 da suka warke daga cikin korona.

    Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta jihar Legas ta fitar a Twitter ta ce daga cikin waɗanda suka warke, 7 daga cikinsu mata ne yayin 26 kuma maza ne da suka haɗa Indiyawa guda uku da aka sallama daga asibitin da ake kula da masu ɗauke da cutar korona.

    Hukumomin lafiyar sun ce yanzu adadin mutum 908 suka warke daga cutur a Legas.

  3. 'WHO ta sha wahalar samun bayanan korona daga China'

    Wani bincike da kamfanin dillacin labarai na AP ya gudanar ya nuna cewa Hukumar Lafiya ta duniya ta yi ta ƙoƙarin samun wasu muhimman bayanai daga ƙasar China a farkon ɓullar cutar korona.

    An bayyana cewa bayanan da aka naɗa sun nuna cewa jami'an WHO sun yi ƙorafi da gwamnatin Beijing kan yadda ta ƙi bayar da bayanai da sauri - wanda hakan ya ci karo da iƙirarin farko da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi na yaba wa China kan yadda ta yi yaƙi da annobar.

    Sai ranar 20 ga Janairu China ta sanar da cewa cutar na saurin yaɗuwa.

    Rahoton na zuwa a yayin da ake nuna yatsa kan China tare da ɗora laifin cewa sakacinta ne ya sa cutar ya yaɗu zuwa sassan duniya.

    Sai dai China ta sha kare matsayarta kan batun.

  4. Ɗan ƙunar baƙin wake ya tarwatsa kansa a Masallaci

    Ɗan ƙunar baƙin wake ya tarwatsa kansa kusa da wani masallaci a Kabul babban birnin Afghanistan, inda ya kashe mutum biyu tare da raunana wasu guda biyu.

    Jami'ai sun ce daga cikin waɗanda suka mutu akwai wani sanannen malamin Sunni da aka kashe a harin da aka kai a Wazir Akbar Khan.

    An bayyana cewa malamin mai zuna Mawlawi Ayaz Niazi ya ya daɗe yana caccakar hare-haren ta'addanci.

    Ƙungiyar Taliban ta yi Allah waddai da harin.

    Masallacin na kusa ne da unguwar da mafi yawanci ofisoshin jekadancin ƙasashen waje.

  5. Majalisa ta amince wa Buhari cin bashin dala biliyan 5

    Majalisar dattawan Najeriya ta amince wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbo rancen kudi dala biliyan 5.513.

    Majalisar ta amince da buƙatar ne a zaman da ta yi ranar Talata, ƙasa da mako ɗaya da shugaban ya tura da buƙatar karbo rancen daga waje domin cike giɓin kasafin kudin 2020.

    Bayanai sun ce Najeriya za ta karɓo rancen ƙudin ne daga hukumar lamuni ta duniya IMF da Bankin raya ƙasashen Afirka da Bankin duniya da kuma Bankin musulunci.

    A makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya aika wa majalisar da kasafin kuɗin na sama da tiriliyan10 da aka yi wa kwaskwarima

  6. Mutum uku sun mutu a harin sansanin 'yan gudun hijirar Nijar

    Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu yayin wani hari da aka kai sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da iyakar Nijar da Mali.

    Wata sanarwa da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Ɗuniya (UNHCR) ta fitar ta ce an kai harin ne ranar Asabar.

    Wakiliyar BBC Hausa a Nijar, Tchima Illa Issoufou ta ce aƙalla maharan su 50 ne suka afka wa sansanin 'yan gudun hijirar da ke ɗauke da 'yan ƙsar Mali 20,000 da kuma 'yan Nijar 15,000.

    Maharan sun yi awon gaba da kayayyakin agaji tare da lalata layukan wayar salula da ke cikin sansanin, a cewar sanarwar.

    Sanarwar ta yi kira ga ɓangarorin da ke gaba da juna da su kiyaye 'yan gudun hijira da sauran fararen hula da ke yankin sahel.

  7. An buɗe masallatai a Abuja

    Biyo bayan umarnin sake buɗe wuraren ibada da kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da annobar korona a Najeriya ya bayar, wasu masallata sun ci gaba da sallah a masallatan Abuja, babban birnin ƙasar.

  8. Najeriya ta fara aiki da yarjejeniyar rage yawan man fetur

    Adadin ɗanyen man fetur da Najeriya ke haƙowa ya ragu zuwa ganga miliyan 1.613 a watan Mayu daga miliyan 1.829 da take haƙowa a baya.

    Wata sanarwa da Ƙaramin Ministan man Fetur na Najeriya Timipre Sylva ya fitar ranar Talata ta ce hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da Najeriya ta shiga da sauran ƙasashen ƙungiyar OPEC+ domin rage adadin.

    Ƙasashen sun yanke shawarar rage adadin ne sakamakon faɗuwar farashin man da annobar korona ta haifar.

    Ministan ya ce wannan ya nuna cewa Najeriya ta yi aiki da yarjejeniyar kashi 52 cikin 100 ba 19 ba kamar yadda wata kafar yaɗa labarai ta ruwaito.

  9. Gwamnatin Kaduna ta ce dokar kulle na nan daram

    Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewa maso yammcin Najeriya ta jaddada cewa dokar kulle kasuwanni da wuraren ibada na nan daram, inda ta shawarci mazauna jihar da su ƙara haƙuri.

    Wannan kira na zuwa ne kwana ɗaya bayan kwamitin shugaban ƙasa ya bayar da damar buɗe dukkanin wuraren kasuwanci da ibada amma ya ce gwamnoni ne ke da ikon tsara yadda za a koma harkokin.

    Kazalika kwamitin ya ce akwai yiwuwar ci gaba da zirga-zirga tsakanin jihohin Najeriya nan da 21 ga watan Yuni.

    Wata sanarwa da Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar ranar Talata ta ce zuwa yanzu gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da shugabannin addini da na al'umma game da tsarin komawa harkokin yau da kullum.

  10. Buhari zai taimaka wa Akinwumi Adesina don ya ci zaɓe

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban bankin ci gaban Afirka, African Development Bank (AfDB), Akinwumi Adesina, wanda ya fada cikin rikici.

    Babban mai bai wa Buhari shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa Shugaba Buhari zai yi tsayuwar daka domin tallafa wa Adesina a takarar da yake yi na lashe zaɓe a karo na biyu.

    Sanarwar da Bashir Ahmad, mai taimaka wa Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata, ta ce an yi ganawar ce a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

    Sai dai bai yi cikakken bayani kan ganawar ba.

    Amma masu lura da lamura na ganin ganawar tasu tana da nasaba da rikicin da Mr Adesina ya fada a ciki na zargin da aka yi masa kan nuna ɓangaranci a bankin.

    Wasu masu kwarmata bayanai ne suka zargi Mr Adesina da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa. Sai dai ya musanta zarge-zargen.

    Hukumar gudanarwar bankin ta ce tana yin nazari da gaske kan zarge-zargen da aka yi masa.

    Amurka ta yi watsi da wani bincike da aka yi a kansa game da zarge-zargen - sai dai bankin ya wanke Mr Adesina daga aikata su.

  11. Ahmad Lawan yana so a yanke tsattsauran hukunci kan masu fyade

    Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya bukaci mahukunta su rika yanke tsattsauran hukunci kan duk mutumin da aka samu da laifin fyade.

    Ahmad Lawan ya yi kiran ne lokacin zaman Majalisar Dattawan na ranar Talata.

    Sai dai bai bayyana abin da yake nufi da "tsattsauran hukunci" ba.

    Yana kiran ne a daidai lokacin da 'yan kasar suke Allah-wadai da fyaden da aka yi wa wasu mata a wurare daban-daban na kasar.

    A cewar shugaban Majalisar Dattawan, "samun tsauraran dokoki na hukunta masu irin wannan laifi zai sa masu yin irin wannan ta'ada su daina".

  12. CBN ya umarci bankuna su gaggauta mayar wa mutane kuɗin da suka maƙale a ATM

    Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce wajibi ne bankunan kasar su mayar wa masu amfani da ATM kudi a cikin asusunsu nan-take idan kudin nasu ya makale.

    Wannan umarni yana cikin sabbin ka`idoji da suka shafi makalewar da kudi ke yi yayin amfani da katin ATM da sauran hada-hada ta intanet da babban bankin ya gicciya wa bankunan.

    Daraktan harkokin sadarwa na babban bankin Najeriya, Isaac Okorafor ne ya sanar da sabbin ka`idojin, wadanda ya ce sun fara aiki daga wannan wata na Yuni.

    Babban bankin ya ce idan kuma aka fuskanci wadansu matsaloli da suka shafi tangardar na`ura da sauran dangoginta, ya ba wa bankuna tsawon kwana guda domin jami`ansu su yi amfani da hannu su mayar wa mai kudin kudinsa a cikin asusunsa.

    Dangane da wadanda kudinsu ya makale bayan sun yi amfani da katinsu na ATM a na`urar bankin da ba nasu ba kuwa, babban bankin ya umurci bankuna su cake wa mai kudi abinsu a cikin asusunsa cikin kwana biyu, sabanin yadda ake daukar tsawon kwana uku zuwa biyar a baya.

    Babban bankin Najeriyar ya fitar da wadannan sabbin ka`idojin a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta ba wa bankuna damar budewa, tun bayan rufe su da aka yi sakamakon bullar annobar korona.

    Kazalika CBN ya bayyana cewa ya gicciya ka`idojin ne da nufin kyautata hidimar da bankuna ke yi wa abokan huldarsu, tare da magance ko wane irin rinto.

  13. Chelsea tana son dauko Werner, Messi yana nan daram a Barcelona

    Chelsea tana duba yiwuwar mayar da hankali wajen dauko dan wasan RB Leipzig Timo Werner, mai shekara 24, idan dan kasar ta Jamus ya bayyana sha'awar komawa can. (ESPN)

    Shahararren dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d'Or sau shida Lionel Messi, mai shekara 32, zai ci gaba da zama a Barcelona zuwa kakar wasa ta badi bayan wa'adin damar da aka ba shi ta barin kungiyar don radin kansa ya wuce. (Standard)

    Real Madrid ta yi watsi da damar karbo aron dan wasan Chelsea Willian, mai shekara 31. Kwangilar dan wasan na Brazil za ta kare a Stamford Bridge a bazara. (Mirror)

    Manchester United za ta biya £10.5m saboda tsawaita zaman aron dan wasan Najeriya mai shekara 30, Odion Ighalo, zuwa watan Janairu - za a bai wa Shanghai Shenhua £6m sannan £130,000 su zama alawus-alawus na duk mako. (Mail)

  14. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta umarci a saki Sanata Orji Uzor Kalu daga gidan yari

    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Jihar Legas ta yi umarni da a saki Sanata Orji Uzor Kalu daga Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Mai Shari'a Mohammed Liman ne ya bayar da uamarnin a safiyar yau Talata bayan ya saurari buƙatar da tsohon gwamnan na Jihar Abia ya gabatar wa kotun.

    Orji Kalu ya nemi kotun ne ta jingine hukuncin ɗaurin da aka yi masa na ranar 5 ga watan Disamban 2019, wanda Mai Shari'a Mohammed Idris ya yanke.

    Ya bayyana cewa hakan ya zama wajibi tun da Kotun Koli a hukuncinta na ranar 8 ga watan Mayu ta tabbatar cewa Mai Shari'a Mohammed Idris ba shi da hurumin yanke hukuncin.

    A shekarar 2019 ne Mai Shari'a Idris ya yanke wa Mr Kalu hukuncin ɗaurin shekara 12 a gidan yari.

    Hakan ya faru ne bayan kotun ta tabbatar da zargin da ake yi masa tare da wasu mutum biyu kan almundahanar naira biliyan 7.65 lokacin da yake gwamnan Jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya.

  15. Coronavirus: An ƙaddamar da motocin fasinja na kyauta a Jihar Rivers

    Gwamnatin Jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ƙaddamar da wasu manyan motocin bas da za su riƙa ɗibar fasinja kyauta domin rage wa mazauna jihar da kuma baƙi raɗaɗin annobar korona.

    Kwamishinan Sufuri na jihar Mista Sunny Ejekwu ne ya ƙaddamar da shirin ranar Litinin a babban Port Harcourt birnin jihar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.

    A cewar Ejekwe, motocin guda 28 za su fara yin zirga-zirga ne a ƙananan hukumomin Obio/Akpor da Port Harcourt da Oyigbo da kuma Eleme a matsayin gwaji.

    Ejekwe wanda ya yaba wa Gwamna Nyesom Wike bisa ƙirƙirar shirin, ya ce za su yi aiki ne bisa sharuɗɗan da masana harkar lafiya suka gindaya na yin nesa-nesa da juna da amfani da man wanke hannu da kuma saka takunkumi.

  16. An yi wa mutum sama da 4, 500 gwajin cutar korona a Kano

    Ma'aikatar Lafiya ta jihar Kano da ke Najeriya ta ce an yi wa mutum 4,777 gwajin cutar korona jumulla daga lokacin da ta barke a watan Afrilun 2020.

    A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin da maraice, ma'aikatar ta ce ya zuwa ranar 1 ga watan Yuni, mutum 958 ne suka kamu da cutar.

    Ta kara da cewa an sallami mutum 265 bayan sun warke lamarin da ya rage adadin masu cutar zuwa 648.

    Sai dai ta ce mutum 45 sun mutu.

    Amma masana harkokin lafiya irin su Farfesa Abubakar Sadiq Isa, shugaban Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa da ke Jami'ar Bayero ta kano, ya shaida wa BBC cewa mutanen da ke dauke da cutar a Kano sun yi matukar zarta wadanda hukumomi suka bayyana.

    Farfesa Sadik Isa ya ce ko kaɗan ba wai rage alƙaluman masu cutar da aka gano ake yi da gangan ba, a'a.

    Akwai jerin matsaloli tattare da ƙoƙarin gwaje-gwajen samfuran mutane a jihar.

    Shugaban na cibiyar bincike kan cutuka masu yaduwa a Jami'ar Bayero Kano ya ƙara da cewa alƙaluman da ake gani na mutanen da suka kai kansu asibiti ne bayan an yi zargin sun yi hulɗa da masu korona.

    Ga alama su kuma jama'ar gari ba sa kai kawunansu don a yi musu gwaji a cibiyoyin da aka tanada a Kano, balle a yi batun mazauna yankunan da ke wajen birnin.

  17. Sabbin bayanai kan dokar kulle a Turai

    Faransa ta kasance kasar Turai ta baya bayan nan da ta sassauta dokar kulle. Ga sabbin bayanai kan dokar kulle a sauran kasashen Turai:

    • Ranar Talata, Faransa ta shiga mataki na biyu na sassauta dokar kulle. An sake bude gidajen sayar da barasa da na sayar da abinci – an bar mutane su yi tafiyar da ta kai kilomita 100 daga Paris, kuma za a sake bude makarantu.
    • Rasha ta tabbatar da sabbin mutum 8,863 da suka kamu da cutar korona yayin da mutum 182 suka mutu, inda yanzu jimulla mutum 423,741 suka harbu da cutar. An sassauta dokar kulle a babban birnin kasar Moscow ranar Litinin, ko da yake wasu sun ce an yi hakan ne saboda dalilai na siyasa.
    • Hukumomi a Jamhuriyar Czech sun sanar da sabbi dokokin fitilun hanya ga matafiya. Turai ta kasu gida-gida game da amfani da fitilun hanya, wadanda suka hada da koraye, rawaya da ja inda suke bayar da mabambanta umarni a kasashe daban-daban.
    • Montenegrois tana shirin sanar da cewa ta kawar da cutar korona.Idan ba a samu karin sabbin mutanen da suka kamu da cutar zuwa maraice ba, to zai kasance kwana 28 ba a samu wanda ya kamu da cutar ba.
  18. Tsofaffin shugabannin Afirka sun yi tur da kisan George Floyd

    Tsofaffin shugabannin kasashen Afirka sun yi tur da kisan da wani dan sanda ya yi wa wani bakar fata George Floyd a Amurka a yayin da ake ci gaba da zan-zangar kyamar kisan nasa a fadin kasar.

    Kungiyar tsofaffin shugabannin kasashe da gwamnatocin Afirka ta bukaci shugabannin Afirka masu ci su "nuna matukar rashin amincewa" kan kisan sannan su nemi a hukunta "wadanda suke da alhakin kisan da ma wasu laifukan kafin wannan", a cewar sanarwar da tsohon shugaban kasar Benin Nicéphore Soglo ya fitar.

    “Wannan irin ƙeta ce da ya kamata dukkan duniya ta yi tur da ita domin ta wukalanta dan adam. Wane ne ya isa ya fito ƙiri-ƙiri a nan ya wulaƙanta Turawa, ko Larabawa ko Indiyawa, ko 'yan ƙasar China, ko Japanawa, ko 'yan kasar Argentina, da makamantansu a nan. Wannan wulakanci ya isa haka," in ji shi.

    "Muna goyon bayan 'yan uwanmu da ke Amurka a wannan mawuyacin hali, kuma muna fatan wannan kisa da aka yi wa George Floyd zai kawo karshen wariyar launin fata da ake nunawa a Amurka."

  19. Najeriya: Me ya sa maza suke yi wa mata fyaɗe a ƙasar?

    Fyaɗe wata matsala ce da ke ƙara kamari a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da ƙananan yara ta hanyar fyaden.

    A ranar Litinin rundunar ƴan sandan jahar Jigawa da ke arewacin a Najeriya ta tabbatar da kama mutum 11 da ake zarginsu da yi wa wata yarinya mai shekaru 12 fyade.

    Ƴan sandan a Jigawa sun ce sun kama mutanen ne bayan wani koke da suka samu daga kasuwar Limawa da ke ƙaramar hukumar Dutse, inda aka zargi wani mutum mai kimanin shekaru 57 da yunkurin cin zarafin wata yarinya.

    Wannan kuma na zuwa a dai-dai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kisan wata dalibar jami'a mai shekaru 22 da ake zargin ta rasa ranta sanadin fyade a wata majami'a da ke kusa da jami'ar Benin a jahar Edo.

    Ana dai danganta karuwar matsalar ga wasu dalilai da suka hada da rashin dokoki masu karfi na hukunta masu aikata fyaden.

  20. Najeriya: Za a koma zirga-zirgar jiragen sama ranar 21 ga watan Yuni

    Gwamnatin Najeriya ta ce kamfanonin jiragen saman kasar za su koma zirga-zirga daga ranar 21 ga watan Yuni, 2020.

    Babban jami'i a kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da annobar korona ya ce sun buɗe zirga-zirga tsakanin jihohi ta hanyar jiragen sama ne saboda sufurin jirgin sama na da tsari.

    Dr. Sani Aliyu ya ce an gindaya wa kamfanonin jiragen sharuɗan da za su bi kafin su ci gaba da harkokinsu.

    Da ma dai masu kamfanonin jiragen saman sun ce suna yin asarar nara biliyan ashirin duk wata sakamakon hana jigilar jiragen saboda dakile annobar korona.