Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya jajanta wa mutanen Sokoto

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Mustapha Musa Kaita

  1. Faransa ta zaftare ayyuka 850,000 a watan Afrilu

    Nan da daƙiƙa 30 za mu iya samun sabbin adadin marasa ayyukan yi a Amurka.

    Makonnin takwas da suka gabata sama da Amurkawa miliyan 30 ne suka rasa ayyukansu lokacin da ake fama da wannan annoba ta korona.

    A gefe daya kuma, Faransa ta zabtare kusan ayyuka 850,000 a watan Afrilu, wanda ya kai adadin marasa ayyukan yi a kasar miliyan 4.5.

    Hukumar da ke kula da ɗaukar ma'aikata ta kasar ta ce wannan ne adadi mafi girma da aka samu tun daga 1996.

    Watan Afirilu ne wata na farko da aka share shi cikin dokar kulle saboda cutar korona a kasar.

    Amma jami'ai a kasar sun ce wadanda suka zama mara sa aikin yi, dama suna cikin wadanda ba su da wani kwakkwaran abin yi a baya.

  2. An samu ƙaruwar masu ɗauke da korona a Zimbabwe

    Adadin masu korona a Zimbabwe ya ninka sau biyu daga 56 zuwa 132 a cikin ƙasa da awa 24.

    Mafi yawan mutanen da aka samu da cutar, sun dawo ne daga ƙasashen da ke makwabtaka kamar Afrika ta Kudu da Botswana, waɗanda galibinsu suna killace a cibiyoyin kula da masu cutar da ke fadin kasar.

    A tsakiyar birnin Gweru, a kalla mutum 19 da ba akai ga yi musu gwaji ba sun tsere daga cibiyar.

    Ɗan majalisar da ke wakiltar yankin ya shawarci iyalan mutanen da su mayar da su cibiyoyin.

    Gwamnati ta yi gargadin cewa za a iya samun wasu masu dauke da cutar a kasar, duk da cewa adadin masu cutar a yanzu ba shi da yawa.

  3. Cutar korona ta kashe Amurkawa fiye da dubu 100

    Adadin mutanen da suka mutu saboda cutar korona a Amurka ya haura dubu 100.

    Cikin sama da watanni uku, mutanen da suka rayukansu a Amurka sakamakon wannan annoba sun haura wadanda aka kashe lokacin yaƙin Koriya da na Vietnam da kuma rikicin Iraƙi idan an hada baki daya.

    Idan muka koma watan Fabirairun da ya gabata, shugaba Trump ya ce Amurka ta shawo kan wannan annoba kuma nan da watan Afirilu za a nemeta a rasa a kasar.

    Joe Biden wanda shi ne abokin kararwar Trump a zaben watan Nuwamba mai zuwa, ya ce da shugaban ya dauki matakin da ya kamata tun da wuri da ba a samu wannan asarar rayukan ba.

    Yanzu dai adadin masu kamuwa da cutar a Amurka na raguwa sannu a hankali - kuma an fara sake bude harkokin kasuwanci a wasu sassan kasar.

  4. Kamfanin jirgin Afirka ta Kudu 'ba zai iya biyan albashi ba'

    Kamfanin jirgin South African Airways (SAA) ya ce ba shi da kudin da zai biya ma'aikatansa albashin watan Mayu.

    Ba a biya ma'aikata kusan 5,000 albashinsu ba tun farkon watan Mayu.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato kungiyar kwadago ta ma'aikatan jjiragen sama Derek Mans tana cewa za a biya ma'aikatan alawus na inshora ne kawai a wannan watan.

    Tun da fari da kamfanin jirgin yana son ya kori dukkan ma'aikatan 5,000 daga aiki.

    Sai dai kotun kwadago ta hana shi ko da yake ta bar kamfanin ya daukaka kara, a cewar shafin intanet na the Independent Online.

  5. Ɗaruruwan mutane sun tsere daga cibiyar killace masu cutar korona a Malawi

    Kimanin mutum 400 ne suka tsere daga cibiyar killace masu dauke da cutar korona a Blantyre, birni na biyu mafi girma a kasar Malawi, bayan sun yi korafin cewa ba a kula da cibiyar.

    Kafofin watsa labaran kasar sun rawaito cewa an killace mutanen ne bayan sun isa kasar daga Afirka ta Kudu kuma sun kamu da cutar korona.

    Sun yi korafin cewa filin kwallon kafar da aka ajiye su, wanda aka mayar da shi cibiyar killace masu dauke da cutar, ba shi da isasshen ruwa, da makewayi da kuma abinci.

    Gwamnati bata yi tsokaci a kan batun ba.

    An wallafa hotunan cibiyar babu kowa a shafin Twitter:

    Lamarin ya faru ne kwana guda bayan kafofin watsa labarai sun bayar da rahoton cewa mutum takwas wadanda suka dawo daga Afirka ta Kudu dauke da cutar korona, sun tsere tsere daga cibiyar killace masu cutar korona da ke Kameza a Blantyre.

    Ya zuwa yanzu an tabbatar mutum 101 sun harbu da cutar korona a Malawi, kuma mutum hudu sun mutu.

  6. An bukaci rufe majalisar dokokin Ghana saboda cutar korona

    'Yan jam'iyyar hammaya da dama na Majalisar Dokokin Ghana suna so a rufe Majalisar na ɗan lokaci saboda fargabar cutar korona.

    Kasar ta Ghana ta tabbatar mutum 7,000 sun kamu da cutar korona, yayin da mutum 34 suka mutu.

    Kakakin Majalisar Dokokin Mike Oquaye ya bukaci 'yan majalisar da ma'aikatanta su je a yi musu gwajin cutar korona kafin a koma zaman majalisa makon jiya.

    Ana fargabar cewa 'yan majalisar suna cikin hatsarin kamuwa da cutar kuma wasu daga cikinsu sun bayar da shawara a rika gudanar da zaman majalisar ta hanyar intanet a wani mataki na hana yaduwar cutar.

    An gudanar da gwajin cutar korona kan mutum 200,000 kuma ma'aikatan lafiya sun ce hakan ya nuna cewa ana samun raguwar masu kamuwa da cutar a Ghana.

  7. Mutum 252 sun harbu da cutar korona a jihar Oyo

    Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, Seyi Makinde, ya ce mutum 252 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a jihar.

    "Sakamakon gwajin CIVID-19 da aka yi mutum biyu da aka kawo sun nun suna dauke da cutar. Daya yana zaune a iSON Xperiences yayin da dayan kuma daga karamar hukumar Ido yake. Don haka, jumullar mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar a jihar Oyo sun kai 252," a cewar sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis.

  8. Shugaban Kenya ya gargaɗi ɗansa kan karya dokar kulle

    Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana yadda dansa ya karya dokar hana fita daga dare zuwa safe wacce gwamnati ta sanya don dakile yaduwar cutar korona.

    Ya ce kwanakin baya 'ya'yansa biyu, wadanda bai ambaci sunayensu ba, sun tafi birnin Mobamsa - inda aka fi fama da korona - da daddare domin yin sharholiya.

    Da ma dai an hana tarukan jama'a a kasar ta Kenya.

    Kazalika gwamnati ta takaita zirga-zirga a cikin da wajen Nairobi, babban birnin kasar, da kuma yankuna uku, wadanda suka hada da Mombasa, inda iyalai da mahaifiyar shugaban kasar suke da zama.

    A wata hira, shugaban kasar ya ce dokar yaki da cutar korona ta hau kan kowa, ko da yake ana sukarsa saboda kin kai dansa cibiyar killace mutane kamar yadda ake yi wa duk mutumin da ya karya dokar kulle.

    Mr Kenyatta ya ce ya yi wa dansa nasa fada sosai saboda yadda ya jefa rayuwar kakarsa Ngina Kenyatta cikin hatsari.

  9. 'Masu ɗauke da cutar korona a Najeriya sun ninka sau huɗu a kan da yadda ake sanarwa'

    Kungiyar likitoci ta Najeriya ta ce akwai yiwuwar masu dauke da cutar korona a kasar sun nunka sau hudu kan adadin da hukumomi irin su hukumar yaki da dakile cutuka masu yaduwa, NCDC, suka sanar.

    Ya zuwa ranar Laraba dai, NCDC ta ce mutum 8,733 ne suka harbu da cutar.

    Sai dai shugaban kungiyar likitocin Najeriya, Francis Faduyile, ya shaida wa BBC cewa suna jayayya game da sahihancin wadannan alkaluma.

    Ya ce: "Mun damu saboda alkaluman da aka sanar sun gaza kwarai da gaske da hakikanin alkaluman da muka sani ko wadanda muka sa rai za a sanar. A halin da ake ciki, mun san cewa ba mu da kasa da ninki hudu na ilahirin alkaluman da aka fitar... Akwai mutane da dama da suka nuna alamar suna dauke da Covid-19 amma suna jira kwana uku zuwa biyar kafin a sanar da sakamakon gwajinsu. Don haka akwai masu cutar da dama da ba a sanar da sakamakonsu ba."

    Da ma dai an dade ana fargabar cewa akwai mutane da dama da suke mutuwa sakamakon kamuwa da abin da aka ce bakuwar cuta ce a jihar Kano da ke arewacin kasar, ko da yake wasu na ganin cutar korona ce take kashe su.

    Masu haka kaburbura a makabartu sun bayyana cewa gawarwakin da ake kai musu sun zarta yadda suka saba gani a irin wannan lokaci a shekarun da suka gabata.

    Wani kwamiti da gwamnatin tarayya ta aika jihar ta Kano da wasu jihohin arewacin kasar yana gudanar da bincike kan lamarin, kuma ya ce sun gano dalilai bakwai da ke suka haddasa mutuwar mutanen.

    Wani likita Nicaise Ndembi, wanda yake aiki a cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka, ya ce yana fargabar cutar korona za ta yadu daga Kano zuwa makwabtan jihohi.

  10. Maraba

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Sashen Hausa na BBC ne yake muku barka da safiya. Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.