Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Eid-al-Fitr: El-Rufai ya jinjina wa Musulmi kan dokar kulle
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita
Abin da ya kamata ku sani game da saka takunkumi
Korona: Ba wanda ya kamu, ba wanda ya mutu, ba wanda ya warke a Kano ranar Asabar
Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce ba a samu wani ƙarin mutum da ya kamu ko ya warke ko ya mutu ba sakamakon cutar korona a jihar ranar Asabar.
Alƙaluman da maikatar lafiyar ta wallafa sun nuna cewa har yanzu waɗanda suka kamu da cutar suna nan a 883 kamar yadda suke a ranar Juma'a.
"Kano ba ta samu wanda ya kamu ba, babu wanda aka sallama sannan babu wanda ya mutu," in ji ma'aikatar, a wani saƙon Tiwtter.
Ya zuwa ƙarfe 11:50 na daren Asabar, 23 ga watan Mayu, mutum 883 ne suka kamu jumilla, sai 36 da suka rasu, an sallami 133 da kuma 714 da ke jinyar cutar a yanzu.
Mutum fiye da dubu 100 sun harbu da korona a Afirka
Alƙaluman da hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Afirka, CDC Africa, ta fitar sun nuna cewa mutum fiye da dubu 100 ne suka harbu da cutar korona a ƙasashe 54 mambobin Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka ta AU.
CDC ta ce mutum 107,412 ne suka harbu ya zuwa ƙarfe 9:00 na safiyar Lahadi, 24 ga watan Mayu.
Kazalika, hukumar ta ce mutum 3,246 sun mutu, yayin da 42,626 suka warke daga cutar.
Barka da Sallah
Barkanmu da Idin Ƙaramar Sallah tare da fatan Allah ya maimaita mana.
Umar Mikail ke muku maraba da shigowa shafinmu na labarai kai-tsaye - kuna cin tuwon sallah kuna ganin yadda duniya ke ciki.
Ku biyo mu kawai.